Skip to content
NovelPress

Hausa Novels

Chapter 96

Chapter 96

Lullubin Biri Book 1 Complete Hausa Novel 1,223 words 0 views Progress saved
Download Book

wuce masallaci saboda ya makara, ko da ya dawo masallaci side ɗin Maama ya wuce, ya shiga bedroom nata ya sameta ta idar da sallah tana lazimi, anan ya zauna har ta idar suka shafa aduan tare, lokacin 6 har tayi. gabanta ya zauna ta ɗora hannunta saman kansa, ta dinƙa jero adu'oi tana tofa masa tana hawaye, har sanda ta ɗauki kusan minti 7 a haka sannan ta ƙarashe da faɗin,"Allah ya kai mun ku lafiya ya dawo da ku lafiya, Allah ya tsare min kai, dan Allah ka riƙe ibadarka, kar kayi wasa da azkar da adu'a. Bello yace ƙilan zaku iya kaiwa har 7days, but bana jin hakan zai yiwu, in ya wuce 4days ɗin ko ka taho ko na biyoku, Allah ya tsareku". Turaki ya amsa da amin yana me ɗago da kansa, ganinta tana hawaye hankalinsa yay mugun tashi. "Maama lafiya?, menene?, in ba kya so naje na haƙura kawai, Bello zai iya komai shi ɗaya and beside zai sami Sameer acan". ta girgiza masa kai da cewar,"a'a ku tafi tare, Sameer ai ya dawo jiya, yace yaje room ɗinka time kayi bacci". Turaki ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya rungumo Maama shima hawayen na sakko masa, ya tsani tafiyar nan da zai yi sam baya son yaje, dan ba shi da yanda zai yi tunda Maama tace yaje ɗin, amma ji yake kamar in yafi wani abun zai faru, kamar tafiyar tasa zai sa ya rasa ɓarin jikinsa. Fullo dai da asuban bayan fitar Turaki masallaci ba daɗewa ta tashi, taga ita kaɗai ce a ɗakin, cikin ranta ta ƙara yabon kyan hali irin na Turaki, watakam bai ma iya kwana the same room da ita ba, ta sauko a gadon tana tafiya a hankali saɗaf saɗaf saboda har sannan tsoron daren jiya bai barta ba, abinda ta fara tunawa ma kenan da ta buɗe idonta, maciji a compound da kuma bakin gate, yo ita kuwa me zai sake tsayar da ita a wannan wurin, ai har mutuwa. a rufe taji ƙofan sanda taje buɗewa, ta ɓata fuska ta dawo ciki ta shiga toilet tayi alwala ta fito, tana idar da sallah ana ɗauke wuta, hakan yasa a sukwane ta koma kan gadon ta kwanta tana ƙudundunewa tana adu'a a fili, har bacci ya ɗauketa. Turaki ya turo ƙofan ɗakin ya shigo, darduman sallah kawai ya kalla ya shaida tayi sallah ta koma ta kwanta, a yanayin kwanciyar kuma yasan tsoron jiya dai har yanzu bai barta ba. kayansa ya cire ya shiga yay wanka, komai a hankali yake yinsa gudun kar ya tasheta, 7:30am ya gama shiryawa cikin ƙananun kaya da bai cika sasu ba, ya ɗauka brief case daidai nan Zaytuna ta shigo ɗakin. duk da ita tasan Fullo matar Turaki ce hakan bai hanata jin kunya ba da ta shigo ta tarar da shi yana kissing forehead ɗinta. sai ta tsaya ɗaga bakin ƙofan tace,"B Ƙaraye yazo". ta faɗa tana murmushi. ya ƙaraso gabanta ya kama kumatunta yace,"ki zage ki dinƙa faɗar sunansa Bello, dan shi gatsal yake faɗar Zaytun a gabana". tasa hannu ta rufe fuska tace,"ai ni ba ya faɗa a gabana". Turaki yay murmushi yay mata side hug yace,"ki kula min da kanku, mussaman waccen fitinanniyar, dan Allah kisa ido akanta sosai kin riga dai kin san bata ji, sanya kai a hatsari shi yafi komai sauƙi a wurinta. ki faɗawa Kaka zata dawo wajenki da zama for some days dan na riga na tsoratata ba lallai ne take iya zaryan zuwa side ɗinsu da nan ba. ki sa ido akan fitarta, bata son cin abinci, bata son shan magani, na baki amanarta na baki amanar Maama na kuma baki amanar kanki, just 4days zanyi in dawo". ya ƙarasa faɗa Zaytuna ta rungume shi. cikin kukan da take yi tace masa,"jiya nayi mafarki Mum ta dawo, ta dawo hannunta da ƙafarta duk ciwo". ya kwantar da kanta a ƙirjinsa yana shafa bayanta yace,"ta kusa dawowa da izinin Allah, ina dawowa zamu nemota ni da Fulani". a sanyaye tace,"Hammah bana tunanin Mum na raye". yace,"yaro ma na riga babba mutuwa, so shekaru ba sune mutuwar mutum ba, gamu da Maama har yanzu a raye, kisa a ranki Mum ta kusa dawowa garemu da ranta da lafiyarta, zan faɗawa Fulani issue ɗin da zarar na dawo". kiran wayar Bello da ya shigo a karo na kusan huɗu yasa shi sakinta yana waiga yana daɗa kallon Fillo. ji yake kamar kar ya tafi, ya kama hannun Zaytun suka fita yana faɗa mata,"idan kinje wurin Kaka ki ɗauko cream ɗin da ta ke shafawa ki jefar, i don't think wanda kika saya ranar nan take shafawa". Zaytuna tace,"tayi haske sosai ko?, nayi zaton ma wanda na sayo mata ne so after na tambayeta tace min bata fara using da shi ba, tana shafa wani da aka kawo musu, Kaka ta hanata buɗe sabon wai almubazzaranci, but zanje ɗin sai na ɗauke". suka fito compound ɗin Bello dai na tsaye sai hararsa yake, Turaki ma ya hararesa ya ƙarasa wurin Maama, sallama dai kamar kar ai tafiyar, kuma kamar wannan ne karo na farko da zai fara tafiya, Nihal ma ta dage cewar ita dai zata bisa, yace sunyi late ai da tun jiya ta faɗa masa sai a anso tictiket har ita, Samha ma ta riƙesa tana faɗin kawai ba sai ya tafi ba ita bata so yana nisa da su, Hajiya Madina ta zabga mata harara tana me jin wani ɗaci da baƙin ciki na kasancewar Samha ƴarta. Ilham kam da ta kwana a gidan tana riƙe da hannun Boɗejo tana goge hawaye. Boɗejo tace,"ni wallahi duk kun saka jikina yayi sanyi, tafiya sai kace yau zai fara, ko saboda kawai ya jima bai yi nesa daku ba?. fisabilillahi irin wannan sallamar da kuke yi ai ta masu bankwana da juna ce, irin fa wannan sallamar akeyi idan mutum zai mutu. to ni dai gaskiya idan tafiyar nan bata zama dole ba ke Madina sai kisa shi ya haƙura". ta kalla Hajiya Madina taga tana goge hawaye tace,"ka ga wani ƙarin tsinkar da zuciya kuma". Turaki dai yana tsaye jikinsa duk yay sanyi, shima ji yake kamar idan ya tafi ba zai dawo ba, sai kallon side ɗinsu yake yi, kamar zai ga Fillo ta leƙo ta window, kamar zata leƙo suyi sallama. ya sauke ajiyar zuciya ya kira sunan Ilham, ta ɗago tana goge hawaye ta tafi zuwa gabansa, ya ɗauke hannunta daga fuskarta yana sa handky ɗinsa ya goge mata fuskar, a hankali yace,"kukan mene?". tace,"nace zan bika tun jiya". yay murmushi yace,"4days fa kawai zanyi na dawo". ya faɗa yana ɗago kai ya kalla Nihal yace,"auta zo". tazo itama nata hawayen na sauka a lokacin. yace,"ku shiga kuyi min rakiya to". Boɗejo tace,"kaga in ɗaukowa Ilham mayafinta ku tafi tare kawai, ni bana son kuka yana ɗaga min hankali". Khalil wanda zai driving nasu yace,"Allah babu da wadda zan tafi da ita, ina sauke su nima da inda zanje". Boɗejo na hararsa tace,"kana kama da mutanen kirki amma ba haka kake ba, in motar kai ka saya sai ka hanasu shiga ai". Khalil dai ya tubure babu me binsa, har sai da Hajiya Madina tasa baki, amma

Table of Contents

Chapters

243 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243