Skip to content
NovelPress

Hausa Novels

Chapter 7

Chapter 7

Lullubin Biri Book 1 Complete Hausa Novel 1,226 words 0 views Progress saved
Download Book

aka tanadarwa ma'aikata domin aje motoci. Tun kafin ya ƙarasa buɗe murfin motar wani tsoho ya ƙaraso wajen cikin sassarfa. "sannu da zuwa ranka ya daɗe". "yauwa Baba sannunmu". Ya faɗa yana fitowa daga motar ya rufe. Tsohon ya buɗe bayan motar ya ɗauki ƴar ƙaramar jakar laptop ɗinsa, sannan yay cikin office ɗin da ita. Shi kuma Turaki ya mara masa baya, tunda staffs ɗin wurin suka ganshi suke ta rissinawa su na gaida shi matsayinsa na Managing Director a ma'aikatar. Bai shiga office ɗinsa ba kai tsaye ya wuce zuwa ofishin Manager, ya ɗauki kusan 5minutes sannan ya fito ya wuce nasa office ɗin bayan Manager ya shaida masa ya tsayar musu da lokacin da zasu shiga meeting ɗin. Zamansa kenan akan kujerarsa sai ga Saktariyarsa ta shigo, ta aje record book ɗin da ke hannunta a saman table ɗinsa, ya janyo shi zuwa gabansa yay rubutu ajiki sannan ya ƙara miƙa mata. Ta ɗauka sannan tace da shi. "ranka ya daɗe PWC sun shigo tun aroud 8:30". Ya ɗago daga kan computernsa ya kalleta, yana mai ɗan ƙanƙance idonsa cikin yin nazari kafin yace da ita. "dama muna da Appointment ne da wasu this week?". "a'a ranka ya daɗe, nima dai nayi mamakin zuwansu..to amma da suka ce min daga ofishin Manager suke sai na tsammaci shi ya turo su wurinka". Ta faɗa tana buɗe wani file na daban da ke hannunta ta ciro wani envelop a ciki, sannan ta miƙa masa. "sun ce na baka wannan". Duk a cikin harshen turanci ta ke maganar. Ya miƙa hannu ya karɓi envelop ɗin ya buɗe, cikin seconds ɗin da ba su haura 10 ba ya gama karanta abin da ke jikin takardar. Bayan ya gama ya miƙa mata tare da cewa. "ki kai office ɗin Manager, zamu yi waya da shi yanzu". Ta rissina tare da karɓa sannan ta fita daga office ɗin. Don Allah share to other groups🙏 Youtube Channel-NISHADI MULTIMEDIA [8/7, 18:42] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *HalimaAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* *5* Fitarta da minti biyar akai knocking ɗin door, ba tare da ya ɗago kansa daga kan system ba yace,"yes come in". Muryar nasa ya fito a hankali yayin da hannunsa guda ke dunƙule a gefen bakinsa. Bello ƙaraye ya shigo cikin office ɗin ya zauna akan kujera, ya fuskanci Turaki da har yanzu bai ɗago ido ya kalle shi ba yace da shi. "sai yanzu ka ga damar fitowan?". Turaki na typing a Laptop yace,"kai ma dai kasan ba mata gare ni ba balle na sami me tashina da wuri". Bello Ƙaraye yay masa wani duba yace,"tun yaushe ake cewa kayi auren kaƙi. ni na rasa ruwan idon uban me ka tsaya yi da har yanzu ka rasa macen da tayi maka". Turaki yace,"Lokacina ne bai yi ba, ko kaga nayi girman da za'a dinga tarata da maganar aure ne?". Bello ya harare shi yace,"sannu motsin gado". Turaki yace,"Yauwa, don haka sai a barni na sarara". Bello ya ƙara cewa,"yanzu Asma'u ɗin ma bata yi maka ba?". "yes, she is not beautifull enough, and you know me well bana son abu mara kyau...idan kana sonta ka ƙara ata biyu na bar maka". Bello dake masa wani kallo yace,"Ba ka da hankali...let close the charpter kamin ka ɓata min rai. kuma bari na faɗa maka, ka daina discouraging mutum akan abunda kai bai yi maka ba alhalin shi yayi masa, Ishaq told me you were telling him to get rid of that girl after all kasan yayi magana da iyayen yarinyar nan...tsaya ma! just because you think the girl was too local shikenan sai akace ba za'a aureta ba?". Turaki yay guntun tsaki yace,"ka zo muyi magana akan aiki ne ko kuma zamu tsaya kan shirmen zancenka ne, da baku da aiki sai zancen soyayya, mace, aure". Har yay shiru sai kuma ya ƙara cewa,"to for what reason ma yana da degree har biyu zai je ya ɗauko yarinyar da she didn't even finish secondary school". "to kai ina ruwanka?, shi ai yasan da hakan yaje ya ɗauko ta ko". Turaki yay tsaki, Bello bai ce da shi komai ba ya fiddo laptop ɗinsa daga cikin jaka. Yay danne danne ya juyar da fuskar laptop ɗin yana nunawa Turaki. "Na sami number'n contractor ɗin, zanyi waya da shi zuwa dare". Turaki ya faɗa sanda ya gama karanta rubutun da ke jiki, sannan ya miƙe daga kujerarsa zuwa gaban wata drower da tarin takardu suke a cikinta. Bello Ƙaraye na binsa da kallo har ya taka steps, hannunsa ya kai cikin drower ɗin yana fito da wani file ƙunshe da takardu fal a ciki. Ya dawo kan kujerarsa yana duba takardun cikin file ɗin. Bayan yay musu ɗai-ɗai ya kwashi wanda zai amfani da su ya wuce cikin madaidaicn parlon cikin office ɗin, daga bisani Bello ya mara masa baya. Tsaye ya tarar da shi yana fuskantar gilashin windo, ya harɗe hannunsa guda ɗaya ta baya. Idanunsa na kafe ne akan glass ɗin kamar mai son ɗakko wani abu ajiki. Bello ya zauna kan kujera yana ƙarewa tsayuwar Turaki kallo, tsayuwar nan tasa mai cike da ƙasaita da taƙama, kana kallo zaka san an gaji sarauta cikin jini da asali. Sanyin Ac yasa idanuwan Turaki lumshewa, muryarsa a kausashe yace, "tunda naji ana talking of billions tunanina ya bani da akwai wata a ƙasa". Ya faɗa sannan ya juyo ya zauna kan kujerar da ke fuskartar Bello, ya shafo fuskarsa da duka tafukan hannunsa biyu kamin yace,"dole ne ma ba zamu yi aiki da wannan company ɗin ba". Bello ya dube shi da mamaki yace,"saboda me?". "yanzu Accounter suka fita shi da mutanen nan". "ta ina kai ka gansu?". "a bakin gate suka tsaya, shi kuma ya fita da mota ya ɗebe su". Ya faɗa ƙwayar idonsa na haskawa da dimbin ɓacin ran da ke ciki, ya ɗora ƙafafunsa kan table ɗin na tsakiyarsu, sannan ya koma ya jingina da kujerar da yake zaune. Idanunsa a kulle yake cewa,"rayuwa cike ta ke da marasa halacci, ko kaɗan bana son mutum mara gaskiya". "So now how are we going to tackle this problem?". Bellon ya faɗa shima in astonishing at what Turaki had said. "na san yanda zanyi tackiling ɗin abun, let's get out of the meeting first". *Gombe, Dukku.* *Alh. Ahmad Alfindiki Residence, 8:30am.* "Kaima ai ka sa ni, it's either na kwana gida ko kuma na wuce gidan Khalid, na tsani kwana a hotel if not necessary". Yusuf ke magana a wayan da ke maƙale a kunnensa, yasa key ya rufe motan sannan ya wuce ɓangaren Inna Wuro wato Kakarsu, har lokacin da ya shiga parlonta bai gama wayar ba. Inna Wuro na zaune kan ɗaya daga cikin kujerun parlon ta kalli Yusuf da ya duƙa yana cire takalminsa, ta taɓe baki ta ɗauke kai taci gaba da kallon tv da ta ke. "yes kusan 2 weeks ma kenan, but i think i will be coming back next tomorrow by God willing. Becox akwai patient ɗin da nake da ita acan". Yaci gaba da wayar yana ƙarasowa ya zauna kan 1 seater. "alright i will you call before then insha'Allah". Inna Wuro dai da ke kallo hankalinta ya rabu gida biyu, tun shigowarsa ta ke jera ƙwafa.

Table of Contents

Chapters

243 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243