Skip to content
NovelPress

Hausa Novels

Chapter 74

Chapter 74

Lullubin Biri Book 1 Complete Hausa Novel 1,214 words 0 views Progress saved
Download Book

leg. tsoro sai ya kamata ta dabarbarce tana ja da baya, duk ta rasa yacca zata yi da kuma abinda ya kamata tayi, taji kamar ta kurma ihu saboda yanda ya kafeta da ido yana kallonta fuskar nan a haɗe, alamar ya harzuƙa da ta'adin datayi masa. sai tai saurin duƙawa ta shiga tattara kwalban da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma tana toshe hancinta da shi, bata ankara ba kwalban ya shige mata cikin fata nan da nan jini ya fara zuba. cikin jin zafin ciwon ta furta,"wayyoo Kaka". ta faɗa tana yarfa hannu jinin na fallatsuwa a wani wurin. ganin yanda jinin ke fita sai kawai ta fashe da kuka tana faɗin,"wayyo jinina, wayyo Kaka, wayyo jinina zai ƙare". Turaki da har lokacin yake tsaye yana kallonta yana kallon jinin dake zuba, yaja tsakin takaici ya bar bakin ƙofar ya ƙaraso ciki. akan bed ya ajiye wayoyinsa sannan ya shige toilet, after 10mints ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa, ƙaramin dake hannunsa kuma yana goge sumar kansa da shi. ya kai idonsa wurin da ya barta yaga bata wajen, sai kwalban sai jinin da yaɓata wajen, ya ci gaba da goge kansa yana ƙarasawa bakin gadon ya zauna. ɗago da idonsa da zai yi ya ganta tsaye bakin ƙofa ta kama handle ta riƙe, sai aikin murɗa shi take yi duk tabi ta ruɗe, har lokacin kuma bata bar kukan ba haka kuma bata daina yarfar da hannun ba. da mamaki kawai ya tsaya yana dubanta, jinsa yake kamar ya tashi ya mammaketa don takaici. ta juyo da kanta a daidai lokacin da yake ƙoƙarin ɗauke kansa daga kanta, karaf suka haɗa ido, Turaki ya ƙara shan murr, ita kuma ganinsa babu riga yasa tayi saurin runtse ido tana ƙara fashewa da kuka. bayan Turaki ya saka kaya, ya dawo ya nemi waje ya zauna bakin gadon, ya ɗauki wayarsa yay dialling numbern Zaytuna. tana ɗagawa yace mata,"ki bada bandage a kawo min". yana faɗar hakan ya kashe. ya ajiye wayar sanda Fillo ta kira sunansa,"Hammah don Allah kayi haƙuri, jinina zai ƙare". tai maganar acikin kuka, ya galla mata harara ta ƙasan ido yana ƙara jin sabon takaicinta acikin ransa. jin ana knocking door ya taso yasa key ya buɗe ƙofar, ya karɓi box ɗin dake a hannun Ɗausiyya ya maida ƙofan ya rufe tare da ƙara sanya key sannan ya dawo ya zauna bakin gado. "zo nan". ya faɗa idonsa akanta. kamar ba zata zo ba sai kuma ta miƙe ta taho kamar me shirin faɗuwa, ganin cewar in taci gaba da tsayuwa a haka jininta duka zai tsiyaye. ta tsuguna a gabansa wurin da ya nuna mata, ta miƙa masa hannun ta runtse ido tana jan numfashi. ya kalli hannun ya kalleta sannan yace,"are you stupid?, kwalban ma da ya shiga ba zaki iya cirewa ba kika barsa a jikinki?, ke shashashan ina ce wai". cikin kuka tace,"to ai ba zan iya ba, jini ne yake fita". "jinine yake fita shine cire guntuwar kwalba ya gagareki?". ita dai bata ce masa komai ba banda kyarmar jiki da take yi, yaja dogon tsakin da yayi duka har cikin kunnenta, ya kamo hannun ya cire kwalbar sannan ya shiga treating mata ciwon, tunda yasa spirit ya goge jinin ta tsala uban ihu tana neman fincike hannun, hakan yasa ya riƙe hannun da kyau yanda ba zata ko iya ja ba balle ta iya fizga har ya ɗaure mata wajen da bandage sannan ya sakar mata hannun. zuwa lokacin tayi kuka ta gode Allah. muryarsa a tamke ba tare da ya duba irin zafin ciwon da take ji ba yace,"tashi ki gyaran waje, saura ki ƙara saka hannu tunda baki da hankali". ta miƙe sai sheƙar kuka takeyi ta ɗauko tsintsiya ta tattare wajen. tana kammalawa ta nufi ƙofa zata fita taji ya ƙara saka key ya kulle. "na gama ai". ta faɗa tana kallonsa a ɗarɗarce. ba tare daya kalleta ba yace,"kin san tsadar turaren da kika fasa?". da sauri ta girgiza kai tace,"a'a, amma don Allah kayi haƙuri bada sani na bane". ya ɗauke idonsa daga kan wayarsa ya ɗora akanta sannan yace,"balle ma da saninki kika fasa ɗin, dan haka abu ɗaya na san da shi sai kin biyani turarena, kuma a yanzun anan wajen ba sai anje ko'ina ba, if kika biyani sai ki sami damar fita daga room ɗin nan". maganarsa yasa ta ruɗe ta shiga ba shi haƙuri tana roƙonsa. tayi mugun basa tausayi amma ya ɗauke kansa kamar baya jinta. wucewar mintina biyar sai yaji shiru ɗakin, kukanta ya ɗauke kamar ɗaukewar ruwan sama, tun before ya juyo da kansa ya kalli bakin ƙofar ya fara tunanin ta yanda akayi ta fita after yasa key, sai dai yana juyowa ɗin sai ya ganta ta ɓingilar da kanta ajikin ƙofa baccin kuka ya ɗauketa kamar jaririya. zai iya cewa bai san lokacin da leɓensa ya tale da murmushi ba, banda yasan abubuwa da dama ba, to tabbas zai rantse wannan rigimammiyar yarinyar ba itace hatsabibiyar dake cusa kanta cikin haɗarin da ba nata ba. ya jima yana kallonta a hakan, matsawar ya barta ta ɗauki tsawon lokaci tana bacci a haka wuyanta sai yayi ciwo sosai saboda yanda ya barƙale, hakan yasa ya sakko a gadon yazo ya ɗauketa ya dawo ya kwantar da ita akan gadonsa, yaja blanket ya rufeta yana jin zuciyarsa na matsewa. for few minutes yana daga kishingiɗe ajikin pillow daga ɗayan side ɗin, tunani kawai yake yi kala-kala acikin ransa, daga bisani ya miƙe ya bar ɗakin, yana fitowa yaci karo da Bello na niyyar shigowa, ganin junansu yasa duk suka ɗaure fuska. Bello na ƙoƙarin ya ture shi ya shiga room ɗin, shima Turaki na ƙoƙarin ya turasa baya ya nuna masa hanyar da ta fi dacewa da shi. "Malami ban hanya". Bello ya faɗa cikin tamkewar fuska yana sa hannu ya ture Turaki gefe, ya murɗa handle ya shiga bed room ɗin. sai dai yana shiga ya fito da sauri yana dakatar da Turaki daga tafiyar da yake yi zai sauka daga benen. "Turaki me nake gani a ɗakinka?". a fusace Turaki ya juyo yace da shi,"uban wa ya kai ka shigar min ɗaki dama?". shima Bellon a fusace yace,"da sai da izininka nake shiga?, ko kuma dama Baffa ce yayi ɗakin naka ne kai ɗaya?...ba wannan ne a gabana ba Muhammad, faɗa min me na gani a ɗakinki?, warware min komai tun ban fara shakku akanka ba". Turaki yaja tsaki ya sauka a benen ba tare daya ce masa komai ba. Bello yayi ajiyar zuciya yana sa hannu a aljihu ya ɗauko wayarsa ya kira lambar Zaytuna. *Masarauta Kaltungo.* "nifa duk bayannan naki a banza nake jinsu, shekaru ba su zasu hanani cimma alwashin dana ɗauka ba Jakadiya, tunda har naga bayan Ramla to babu abinda zai hanani ganin bayan Madina, ki rubuta wannan ki ajiye, ko bayan raina zaki faɗa cewar ni Fulani nace duk wata mace da Dikko zai aura rayuwarta a hannuna take". furucin da Fulani tayi kenan a sanda idanuwanta ke sauka a ƙasa, tana jin zuciyarta na zafi da tafarfasa, tana jin yanda zuciyarta ke kuka, kukan da ta ɗauki tsawon shekaru masu yawa tana yi kuma har yanzu

Table of Contents

Chapters

243 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243