Chapter 112
Chapter 112
ya dinƙa yawo da shi yana nunawa jama'arsa da jama'ar mai martaba. Turaki kam ya koma kamar yaro, bai sami salama ba sai da suka dawo fada, dan iyakar wanda suka dawo fadan duk ƴan'uwa ne, yana jin wayarsa na ta buga ringing daga Maama sai dai babu ta yanda za'ai ya ɗauka. acikin fadar Mai Martaba ne zaune daga tsakiya akan royal chair, sai Hakimi a kusa da shi ta hannun dama, sai Baffa a kusa da shi ta hannun hagu, sannan Falmata a kusa da shi sai Boɗejo daga kusa da hakimi ta wani hakimci ƙafa ɗaya kan ɗaya cikin alkyabba me ƙallin bala'i, sai ɗaukar idon jama'a take, bakinta yaƙi rufe haƙwaran makka ɗinta guda huɗu duk a waje. Mai Martaba ne ya fara doguwar nasiha ga amarya da ango akan zaman aure, bayan ya gama ya damƙa amanarta a hannun mijinta, ya kuma yi musu addu'ar samun zaman lafiya da samun zuri'a ɗayyiba. bayan ya gama Hajiya Boɗejo ta ɗora da nata, tayi doguwar nasihar aure da babu wanda jikinsa bai amsa ba a wajen hatta Turaki, daga ƙarshe kuma sai ta fashe da kuka tana zuba musu adu'oi iri-iri. bayan ta gama Hakimi ma yay nasa, bayan ya gama Baffa yay musu tasa, sai a sanda yake yi musu nasihar ne kawai Turaki sai jin hawaye yayi ya sauko masa ba tare da sani ba, daga ƙarshe Inna Falmata ma tayi nata. bayannan kuma aka rarrabawa ƙur'ani da littafan adu'oi. daga nan kuma aka ɗauki amarya akayi cikin gida da ita ana batun gobe idan Allah ya kaimu za'a shiga sauran hidiman taron biki. Turaki na fitowa daga fada ya fice bai bari sun haɗu da Baffa ba, iyakar kyau dai yayi kyau kowa ya gansa yaga sabon ango amma sam babu wannan annurin na farin ciki a fuskarsa. Gimbiya Ilham kam tun sanda tai ƙoƙarin kama hannun Turaki taji yanda ya make hannunta taji jikinta yyi sanyi, musamman da ta kalla fuskarsa taga ya murtuke kamar wanda aka yowa aiken mutuwa, kace bai taɓa dariya ba a duniyarsa. Turaki na isa gida Hajiya Madina tasa key ta kulle side ɗinta dan bata ma so wasu ƴan bani ka iya ɗin suzo mata, ko kuma Baffa ya dawo yace zai shigo. hakan ko sai data faru, mutane suka dinga zuwa gidan suna juyawa, Mai Gadi na faɗa musu abinda Hajiya Madina tace masa na cewar basa nan, a same su acan masarautar. to haka dai ranar Hajiya Madina da yaranta suka yini cikin ɓacin rai, iyakar yin Baffa ya gana da matarsa da yaransa Hajiya ta toshe duk wannan ƙofar, sai haƙura yayi dole, dan ko a washe gari sai gidan Hakimi ya tafi yay breakfast dan shima irin Turaki ne bai iya cin abincin restaurant ba. kuma a ranar da daddare Boɗejo tazo ta tayar da wuta a gidan, kamar zata cinyesu saboda masifa akan Turaki sai yaje Dinner, har da cewa,"aini Madina ban san ke fitinanniya bace sai yanzu, ashe kin ma fi Fulani Azima haɗari, to wallahi dai akan auren jikana da jikata aniyarki ta koma miki". Maama dai ɗaga kai bata yi ta kalla Boɗejo ba balle ta tanka mata, har ta gama zazzaga masifarta da yaɓa magangunta. Boɗejo ta tasa ƙeyar Turaki a gaba tace,"wuce motar Nasiruddeen na waje suyi maka rakiya, in an hana ƙawayenka zuwa ai kana da ƴan'uwa". sannan ta juya kan su Zaytuna tace,"ku kuma ku wuce muje, haka kawai za'a tusa muku baƙin hali a zuciyarku, tsakani da Allah mene abin baƙin ciki a wannan aure banda ma dai zuciyar mutum ba ta da ƙashi. to kuyi gaba muje ba sai kunyi wata kwalliya ba, idan ban isa da wasu ba ku ai na isa da ku. ƙulla auren zumunci kuma yanzu na fara, kuma inga uban da zai sa Turaki ƙaro aure dan naji ana ƙishin ɗin haka, in ban ba'asa naje na bankawa ƴar mutane wuta ba". haka ta saka su a gaba har Khalil da su Samha da suka dawo a yau suka wuce suka tafi. wajen dinner dai iyakar haɗuwa ya haɗu, amarya da ango sun haska guri, amma ko kaɗan fuskar ango bata murmusa ba, MC ma da yay batun liƙi sai Khalil ne ya fito ya wakilce shi ya watsa bandir ɗin ƴan 500 har guda biyu. kuma fuskar ango kaɗai zaka kalla ka hasko tsantsar rashin son auren a tare da shi, Gimbiya Ilham kam da ƙyar ta iya controlling hawayenta ta dinƙa yaƙen ƙarya, saboda gaba ɗaya ta fahimci Turaki ba auren ne baya so kaɗai ba ita kanta ba sonta yake ba. bata tabbatr da hakan ba sai after an tashi daga dinner sunzo shigo mota yace,"ki bar cusa kanki gare ni, domin ni ba sonki nake ba, cusa min ke akayi. idan kuma wancan son kike tunani har kika iya amfani da shi kika sa aka ƙulla wannan auren to kinyi babban kuskure, domin ni son ƙanwa nake miki ba shirmen so irin naki ba. and again ki san da cewar baki da matsuguni a zuciyar Turaki dan already wata da ta fiki komai ta cike wannan gurbin". wannan maganganun nasa yasa tayi kuka ta gode Allah a wannan daren, kuma sai ta dasa zarginta akan Gimbiya Aisha. washe gari ma kamar ba zata je Cocktail party ba amma haka dole taje, shima kuma taga abinda yafi na jiya a wurin Turaki, don opalli ya nuna kowa ba auren so suka yi ba. ranar lahadi da za'a kaita tamkar ta shiɗe haka taji, tunanin ta inda zata fara zama da shi kawai take yi, Mai Martaba da Fulani Azima su suka kaita gidan anan Estate ɗin su Turaki, daga gidansa zuwa nasu babu nisa, gidan ya gaji da haɗuwa kamar a turai, bai san sanda Baffa ma ya gina gidan ba. shima Turaki Baffa da Maama ne suka masa rakiya, kuma banda cewar ɗanta za'a kai babu abinda zaisa taje. ko kula Baffa bata yi ba har suka je, yana ta janta da hira tai banza da shi sai Turaki da take kulawa, tana faɗa masa ya cire damuwa saboda yanda duk ya rame. acan gidan Amarya da Ango ma Hajiya Madina kallon inda Mai Martaba yake bata yi ba balle wata Fulani Azima, bata san ita Fulanin ba so take ba. haka suka gama yiwa ma'auratan nasiha da adu'a sannan suka baro su. kamar yanda sunnah ta koyar Turaki suka yi nafila tare da matarsa, bayan sun idar ya kama kanta yayi adu'a, sannan ya gabatar mata da abinci. ita taci dan shi bai iya cin komai ba, sai bayan da ta kammala ya tashi ya bar ɗakin ya wuce parlo ya zauna, tunda ya fito kuma yake ta tunanin Fillo, Allah kaɗai yasan me yake ji a zuciyarsa. ya jima zaune anan daga baya ya tuna fa cewar aure aka yi masa and amayar tana ɗaki, ko kaɗan baya ƙaunar ganin Ilham, kuma baya jin zai iya haɗa jiki da ita su kwana a shimfiɗa ɗaya, amma kuma ba shi da yanda zai yi, ba shi da wani hope, dole ne zai bi koyarwar addini, zai yi amfani da ilimin da yake da shi dan ganin bai kaucewa addininsa ba kuma bai ƙi
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243