Skip to content
NovelPress

Hausa Novels

Chapter 177

Chapter 177

Lullubin Biri Book 1 Complete Hausa Novel 1,214 words 0 views Progress saved
Download Book

dukkanninsu idan mace tana da ciki to dole ne idan aka haife cikin nan to iddar ko takabar ta yanke, Idan ma aka saketa yau kuma ta haihu Yau to iddar ta ƙare. Idan ma mijinta ya mutu a yau kuma ta haihu anjima to ta gama takaba. sai dai kuma idan akayi aure miji bai tare da mace ba, ko ya tare da ita amma bai taɓa kusantarta ba, to ba zata yi masa iddah ba duk tsayin lokacin kuwa da suka ɗauka tare, da zarar ya bayyana sakin tana iya yin aurenta ko da ace a daidai wannan gaɓar wani ya zo ya bayyana cewar zai aureta to ana iya ɗaura aurensu anan take insha'Allahu...wannan shi ne taƙaitaccen ba yani a game da tambayar da kika yi, wallahu ta'Ala a'alam"._ gama bayanin nasa yay haɗe da taruwar ruwan hawaye a idon Fillo, a hankali kuma sai taji hawayen su na sakkowa saman kuncinta, ta rumtse ido tare da cije leɓenta na ƙasa ta kifa kanta akan cinyarta, haka ɗaya ba tare da sanin dalili ba taji tana so tayi kuka, irin kukan da zata yi ya isheta, taji zuciyarta na matsewa da wani irin zafi tamkar ana hura wuta, ciwon kan da ta kwana biyu ba ta yi ba ta ziyarce ta, ta kasa danne kukan da ke neman ƴancin fita a bakinta kawai sai ta sake shi, ta miƙe da sauri ta haye upstairs tana jin wani irin wahaltaccen yanayi a tare da ita, tana shiga ɗaki ta faɗa kan gado ruff da ciki, kuka sosai take yi ta rasa ta ɓangaren da zata lallashi kanta. sai da ta kusa rabin awa tana kukan sannan ta daina, ai kuwa kanta yayi ma ta wani uban nauyi kamar zai faɗo, ta miƙe ta shiga toilet ta yi wanka a daddafe ta fito, ta buɗe wadrobe ta ɗauko doguwar riga ta atamfa ta saka, ta taka stool ta ɗaga ƙasan trolly ta ɗauko takardar sakin, ta zura hijab ɗinta tare da buɗe drower ta ɗebi kuɗi ta saka a jaka, abu biyun nan su kawai take buƙatar tafiya da su, takardar sakinta da zata zama shaida da kuma kuɗin da za su kaita Taraba. ta zauna bakin gado zuciyarta na karanto ma ta kuskurenta, ita ai duk ɗan guntun ilimin da take da shi ce take sai tayi masa iddah shiyasa har ta yarda ta zo gidansa, ashe yanzu ita kwata-kwata ma ba ta da wata alaƙa da shi, zaman haukarta na rashin iliminta kawai take yi. abun da ta kasa ganewa shi ne; me yasa ta damu da sakin nan?, me ya sa take jin kamar rabuwa da cikin gidan nan tamkar rabuwa da wani ɓangare ne na jikinta?, abu ɗaya kawai ta san yana rubuce a tafin hannunta, babu wani abu da zai hanata barin gidan nan ayau tun da har ba ta da wata alaƙa da shi, za ta tafi tabarsa nisan tafiya kuwa ta har mutuwa. sabbin hawaye suka shiga sauko ma ta, taji kamar hayaniya da ga downstairs, bata ta shi ba taci gaba da zamanta tana tunanin ta yanda za'ai ta tafi, ita ba sanin hanya tayi ba, ita ba lambar wayar kowa ba, ba ta taɓa sanin ina ne tasha ba balle ta kai kanta, anya ba zata nemi taimakon Baba me gadi ba?, dan ba zata iya zuwa gidan su Turaki ba. zuciyarta ta yarje ma ta hakan, dan haka ta miƙe tana ƙara goge hawayen fuskarta ta fita da ga ɗakin tana jin wani baƙin ɗaci a zuciyarta, tana fara sakkowa da ga steps ta hangi Nihal da wasu yara da za su yi sa'anni da ita, kuma kallo ɗaya ta yi musu ta tuna maganar Bello da yayi mata jiya cewar za'a kawo ma ta ƴan aiki, tai saurin komawa yanda ba za su jita ba, ta cire hijab ɗin jikinta ta ajiye tai saurin shiga toilet ta wanke fuskarta da sabulu, tana fitowa taga Nihal a tsaye tana ƙarewa ɗakin kallo. tayi ƙarfin halin ƙaƙalo murmushi kamar yanda Nihal ɗin ke yi ma ta. cike da zolaya Nihal ta ce da ita,"kai Antynmu ai sai muyi zaton ko honey moon ku ka wuce babu sallama, 1week ba ku leƙa mu ba". Fillo tai murmushin yaƙe ta tsuguna tana gaida ita. Nihal ta ce,"kar ki ban kunya don Allah tashi mana, ni ya kamata na tsuguna miki yanzu ai ba ke ba, matar babbar Yaya". Fillo taja yatsun hannunta ta ce,"Adda Nihal ina Maama da Mum?". ta ce,"su na kan hanyar zuwa ai, ashe ba ki da lafiya shi Hammah kwata-kwata bai faɗa ba sai yau. ya sauƙin jikin naki?". Fillo ta ɗago tana kallonta sai kuma ta ce,"naji sauƙi ai". Nihal ta ce,"kinga yanda ki ka rame kuwa". buɗar bakin Fillo zata yi magana suka ji shigowar mutum, Nihal ta gaida Turaki tana yi masa sannu da zuwa, bai ko amsa ma ta ba yayi ma ta nuni da hanyar fita ta zo ta wuce tana ɓata fuska, tun da Baffa yay masa gate da gida shikenan ya sauya musu ko magana ba yay musu up to now, sai kace su ne suka hana shi zuwa gidan. sai da Nihal ta fita tukunna Fillo ta ɗago ta yi masa kallo ɗaya ta ɗauke kanta, yana tsaye jikin ƙofa ya harɗe hannayensa a ƙirji ya zuba mata ido, kamar me son karanto wani abu a tare da ita, jin idonsa a kanta yasa ta haɗe gira sama da ƙasa ta juya masa baya. wucewar daƙiƙa biyu wayarsa da ke aljihu ta shiga ringing, ya sa hannu ya ɗauko yana picking tare da cewa Hajiya Madina,"Maama ba ta fito ba ne idan ta fito zan kira ki". muryar Hajiya Madina na bayyana damuwar rashin lafiyar da yace musu Fillo na yi ta ce,"to da ta fito ka kirani kaji ko?, nima gamu nan muna kan hanyar dawowa na tsaya her excellency ne za ta shiga office ta fito, ka dai ce kunje hospital ko?". ya shafo wuyansa ya ce,"ehh Maama ta ji ma fa sauƙi, na faɗa miki ma zatona ko Baffa ya dawo ne shiyasa bamu zo ba". ba ta ce da shi komai ba ta kashe wayar tana shaida Mum batun rashin lafiyar. "da me babban suna mu ka gama waya, ashe rashin zuwan na su ba ta da lafiya ne, ni dama dai ince cin amarci ai ba zai hana su zuwa su gaisar da mu ba muna kusa da su. yanzu kawai mu tafi gidan na su ko? duk da naji yace ai jikin da sauƙi". Mum ta ce,"ni kam ba zan iya zuwa gidan su ba, tun da taji sauƙi shikenan, ki kwantar da hankalinki please". Maama ta ce,"ni kam gaskiya sai naje na dubo su hankalina zai kwanta, sati guda ban saka me babban suna a idona ba". Fillo na murguɗe murguɗe da harare harare ta nufi hanyar toilet za ta shiga, yay amfani da sautin muryarsa wajen buga mata tsawa akan ta tsaya, duk ta yanda taso ta dake ta nuna rashin firgitarta sai da ta tsorata ta ƙame a wuri ɗaya jikinta na kyarma. ya ƙarasa shigowa ciki ya ja stool ya zauna akai, ya saita kira akan lambar Maama, sannan ya

Table of Contents

Chapters

243 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243