Chapter 19
Chapter 19
ba a lokaci ɗaya. Tana jan yatsunta hannunta tace da me gadin,"Baba ina zan shiga?, ginin ne na gansa da yawa". "ko dan gaba in kika je wuri ki dinga tambaya, ai matambayi baya ɓata". Me gadin ya faɗa yana yi mata nuni da part ɗin Hajiya Madina. Cikin sanyin tafiyarta ta wuce, kawai tsayawa tayi a bakin ƙofar dan bata san ta yanda zata buɗe ba, bata taɓa ganin irin wannan ƙofar ba, inda ma ace handle ne irin wanda ta saba gani sai ta murɗa wataƙila ta buɗe, amma wannan ma ai ba ƙofa bace glass ne kawai. Kusan 2minutes tana tunanin ta yanda zata shiga, sai gani tayi an turo ƙofar daga ciki ta buɗe. ta kalli Sameer wanda ya fito bai lura da ita ba, ya saki ƙofan ta ƙarasa rufe kanta sannan ya fara taka steps zai sauka. Fillo dai kokawa ta kama yi da ƙofar, ta tura ciki taƙi shiga, ta kuma yi ƙoƙarin kama handle ɗin ta janyota nan ma ƙarfinta ya kasa. kamar zata yi kuka ta juya taga saura steps 2 ya ragewa Sameer ya gama sauka. Cikin saurin murya tace da shi. "don Allah kazo ka buɗe min". Ko da ya juyo ya ganta kamar ba zai dawo ba sai kuma ya dawo ɗin, ta wutsiyar ido ya ke kallonta. Maama me ƴan aiki, ko aina ta samo wannan kuma oho. Yasa hannu ya janyo glass ɗin da aka rubuta open daga jikin handle ɗinsa, yay ɗan murmushi saboda yanda yaga Fillo ta kafe hannunsa da ido da alama tana so ta koyi yacce zata buɗe ne saboda gaba. Ya bata hanyar shiga yana ce mata,"ki ke shiga ta back door, in ba haka ba ƙasusuwanki akan wannan ƙofar za su ɓalle". Gyaɗa masa kai kawai tayi tukunna ta shige ciki, ai bama sai ya faɗa mata ba, dan ta gama ayyanawa daga yau ba zata ƙara dawowa ba. Yau ɗin ma saboda bata so Kaka taji babu daɗi ne shi yasa banda haka tuni ta juya, ƙofa sai kace dutsen duniya, ai da taci gaba da gwada ƙarfinta wajen buɗewa kaf ɗinta zata kakkarye. Tana tsaye tana ƙarewa haɗuwar parlon kallo tare da saƙe-saƙe cikin ranta Samha ta fito daga wani room a cikin parlon, ganinta ƙatuwa yasa Fillo saurin durƙusawa tana gaisheta a tunaninta ita ce Hajiya Madina. Murya can ƙasa Samha ta amsa gaisuwatata ba tare da ta ko kalli inda ta ke ba, ta wuce ta zauna kan kujera tana ɗaukan remote ta sauya channel. Wani abu ya tuƙe a wuyan Fillo, kenan haka Hajiyan ke wulaƙanta mata Kaka?. tausayin Kakar ya kamata, cikin ranta tana adu'ar Allah ya horewa Amir dai suyi aurensu ko sa huta da wannan bautar a ƙasan wasu balle a dinga wulaƙanta su. "gadin ƙofa aka saka ki ne?". Samha ta tambayeta bayan wucewar daƙiƙu biyar. Fillo tace,"a'a Hajiya, ban san aikin da zanyi ba ne". Samha ta ɗago ido tana ƙare mata kallo, garin kwashe-kwashen Maama yau kuma me ƙanjamau ta ɗebo musu, halitta babu kyan gani jiki sam babu tsokar arziƙi, kai da gani kasan ba'aci an ƙoshi ba. baki ta taɓe sannan ta ƙara ce mata,"Maama bata karanta miki aikin da za ki ke yi ba?". Sai a sannan Fillo ta ɗago ido tana kallonta, ashe ɗazu kallon tsoro tayi mata, yarinya ce da girman jiki dalilin da yasa tayi zaton matar gidan ce. A hankali tace,"ba'a nuna min ba". ta faɗa tana tura baki gaba. Da hannu Samha tayi mata nuni, ita kuma ta shige sum sum kamar munafuka ta nufi kitchen ɗin, sai faman takure ƙafafuwanta ta ke yi saboda sanyin AC da yay yawa a tiles ɗin, ga shi takalminta ta barsu a can waje. Turaki na tsaye a bakin friedge, ya ɗauko maltina ya buɗe ya tsiyaya a cup, ta tsuguna tana gaishe shi, zaton ta ko me gidan ne, amma bai amsa mata ba kasancewar da earpod a kunnensa duka biyun, har ranta taji babu daɗi, a yau ta ƙara yarda da cewar talaka wulaƙantacce ne indai yana ƙasan me kuɗi. Turaki kam bai ma san da shigowanta ba, ganin ya juyo daga inda yake facing tayi saurin matsawa daga bakin ƙofa ta ba shi hanya, yay ficewarsa still bai lura da ita ba dan hankalinsa ba wajen yake ba. tafi ƙarfin minti biyar a tsaye daga gefe ɗaya, haɗuwa da tsaruwar kitchen ɗin kawai ta ke ƙarewa kallo, ita dai badan-badan ba sai ta rantse gidan ƴan yan kan kai ne nan, ko kuma tace ba'a duniyar take ba gaba ɗaya. Fitowa tayi daga kitchen ɗin dan sanin abunyi, bai zai yiwu Kaka na can kwance ba lafiya ba tazo ta tsaya anan babu aikin fari balle na baƙi. tana fitowa su kai kiciɓis da Hajiya Madina, tana kallonta ta shaida ita ne matar gidan, tayi saurin durƙusawa ƙasa ta gaisheta, Hajiya Madina ta amsa fuskarta da fara'a tana ce mata ta miƙe tsaye. Fillo ta miƙe kanta a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta, Hajiya Madina tasa hannu ta ɗago fuskarta tana mata wani kallo, wani kwarjini yarinyar tayi mata, itama Fillon hakan ta ke a wurinta, shi yasa tun kallon farko bata bari sun ƙara haɗa ido ba. Allah ma ya sa ni Hajiya Madina ta girgiza da ganin yarinyar nan wanda ta rasa dalilin hakan, tsintar kanta tayi da jin wanzuwar sabon yanayi, babu shakka yarinyar zata zamar mata jigon wani abu, ta san da wannan. ta kawar da mamakin a gefe guda, Kafin ta buɗi baki tayi magana Fillo ta rigata. "Kaka Rabi ce ta turo ni na ƙarasa aiki, bata jin daɗin ne yasa ta tafi". Tayi maganar idanuwanta na kan tafin hannun Hajiya Madina da ke tallafe da haɓarta. Hajiya Madina ta faɗaɗa fuskarta da murmushi tace,"masha'Allahu sannunki, ya sunanki?". "sunana Halima". "sannu Halima, Allah miki albarka...ke jikar Kaka Rabin ce?". Ta ɗaga kanta,"ehh jikarta ce, a wurinta nake da zama". "to sannunki kinji, amma jikin nata ba tsanani yayi can ba ko?". Ruwa ya kawo idon Fillo sanda tace,"ehh na dai baro ta zata yi bacci, tace kanta ke ciwo". Hajiya Madina tace,"to Allah ya bata lafiya...kin ƙarasa aikin?". ta girgiza kanta alamar a'a. "ai yanzu na shigo kuma ban san aikin da zanyi ba". Hajiya Madina ta sauke hannunta daga haɓarta, bata san me yasa zuciyarta ke wani irin zillo ba. ta kalla kujerar da Turaki ke zaune, bai ci komai ba ta sani, kuma ba zai ci girkin kowa ba idan ba nata ba, ƙannensa ma sai an kai ruwa rana yake iya cin abincinsu balle na wata ƴar aiki, ita kuma tana so ta fita cikin gaggawa, su na da meeting na friends ɗinsu da suka saba duk ƙarshen wata. "mu shiga kitchen ɗin". ta faɗawa Fillo. Tayi gaba ita kuma ta bita a baya. tayi mata nuni da wata drower tace,"buɗe ciki ki bani ƙwai guda 10". cikin sauri Fillo ta ɗauko ta kawo mata, ita kuma ta ɓare ledar indomie super pack guda biyu ta jefa acikin ruwan zafi, sannan tasa Fillo ta yanka albasa ta kuma yi greating taruhu. In few minutes Hajiya Madina ta gama soya indomie da ƙwai ta zuba a plate, sannan ta dafa tea da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243