Chapter 171
Chapter 171
ki sha". tayi bismillah a fili ta kafa baki, ba ta sauke ba sai da ta shanye tass da ma tana jin ƙishirwa. "ko ke fa, adu'armu itace Allah ya baku zaman lafiya, Allah yayi muku albarka ya albarkaci rayuwar aurenku, Allah ya baku zuri'a ɗayyiba, ya kauda fitina tsakaninku ya haɗa kanku ke da abokiyar zamanki". kowa da ke ɗakin ya amsa da,"ameen". a lokacin Dada ta shigo, itama ta bata wani ruwan tofin adu'ar ta sha, sannan ta ba ta wani magani na su da kuma wani turare da ta fesheta da shi lungu da saƙo, ta kuma bata wata ƙaramar kwalba itama da ke ɗauke da turare aciki ta ce,"karki yarda taje hannun kowa har ki shiga ɗakinki, ki shafa turaren ciki a lokacin da zai shigo ɗakin, karki yi wasa da duk abin da muka faɗa miki da kuma abubuwan da muka ba ki, so muke kiyi zarra, ki zama tauraruwar da ke haska cikin gidan mijinki". Dadda da Adda Asma su ka kamata a tare suka fita da ita, ɗakin Hajjah aka wuce da ita inda nan Ummi ta ke da zama yanzu ita da su Kaka da sauran ƴan'uwanta, ana shigo da ita Ummi kawai sai ta fashe da kuka, aka ƙaraso da Fillo gabanta ta durƙusa. Ummi ta zura hannunta cikin alkyabbar ta kamo hannunta ta riƙe anata, sai a lokacin Fillo ma ta saki nata kuka da bai zo ba tun ɗazu. "Yanzu kin zama matar aure, kin bar ƙarkashinmu kin koma ƙarkashin wani bawan Allah wanda Allah ya zaɓa miki matsayin mijinki, haka zalika aljannarki ta koma ƙarƙashin mijinki, bauta za kiyi, bautar da za ki saka a ranki cewa ba Muhammad Turaki za ki bautawa ba Allahnki za ki bautawa, biyayyar mijinki a yanzu ita ce gaba da komai a gurinki in banda addininki, in dai har za ki yi ma mijinki biyayya to za ki shiga aljannah, faɗar Allah ce ba tamu ba, ki kula da abincin mijinki ki kula da shimfiɗarsa, karki wasa da tsafta, ki zama me haƙuri, karki ko yi rashin juriya da kawar da kai, in har kin riƙe waɗannan abubuwan riƙo me kyau to kuwa za ki kama mijinki a tafin hannunki, kina da kyau ki ƙara da wanka ƴata, Allah ya yi miki albarka Halima, biyayyar da ki ka yi min Allah yasa kema naki ƴaƴan da za ki haifa su yi miki. Allah ya sa wannan aure da ki ka yi anyi kenan sai mutuwa ce zata raba ku, Allah ya yi riƙo da hannayenki ƴata, Allah ya dasa tsananin tausayinki da ƙaunarki a zuciyar mijinki, Allah ya ba shi ikon yin adalci a tsakanin ke da abokiyar zamanki, don Allah ki zama me haƙuri a gidan aurenki kinji, da auren so da auren ƙiyayya duk sai anyi haƙuri sosai ake jin daɗin zamansa, ki girmama iyayen mijinki wannan zai ƙara ba ki fada a zuciyar mijinki, kar ki zamto me yi masa jayayya da ƙorafi hakan zai sa mijinki yaji kin fita a ransa, ki kula da duk haƙƙoƙin mijinki, ki dage da ibadah da kuma yawaita adu'ar tsari da zaman lafiya tsakanin ke da mijinki da abokiyar zamanki, kin san ba ki da lafiya dan haka ki nesanta idanuwanki da kunnuwanki da dukkan abinda zai zamar miki damuwa balle ki jawa zuciyarki matsala, sannan abu na ƙarshe da zan jaddada miki shi ne ki zama busy akan yawaita karatun ƙur'ani, wannan zai hana zuciyarki samun lokacin biyewa zugar shaidan, Allah ubangiji yayi miki albarka, ya baku zaman lafiya ya kauda fitina a tsakaninku, na yafe miki dukkan abin da kika yi min". rabuwa dai tsakanin mahaifiya da ƴarta sai ya zama abu me wahala, dan ƙam Fillo ta riƙe Umminta tana kuka me taɓa zuciya, kuma da yake itama Ummin tana da raunin zuciya sai su ke ta kukan tare, sai da ƙyar aka samu aka cire Fillo daga jikinta. suka fito aka wuce da ita part ɗin Maudo, shi da Dottijo ne zaune a parlonsa, anan aka zaunar da ita kowa ya fita ya rage daga ita sai su, Maudo ya ɗora hannunsa akanta ya dinƙa kwaranyo adu'a yana tofa ma ta, ya gama nasa Dottijo ma ya yi ma ta, sannan suka shiga yi ma ta faɗa da nasiha me ratsa zuciya, kukanta sai ya ƙaru, kuma lokacin kewar mahaifinta ta kamata, sun jima su na ma ta nasihohi kafin a fito da ita. ko ƙafar gida ba'a fito da ita ba anan ƙaton tsargidan akayi parking da motar Maudo me shegen tsada a gabanta aka shigar da ita, ana ta busa algaita da sarewa kamar wata ƴar sarki, Dadda da Inna Baraka yayyan Hayyo sai wata cousin ɗin Ummi me suna Innah Hajar su ne suka shiga motar amarya, sauran motocin kuma da mutane shida kacal suka bi bayansu, motar amarya tayi airpot sauran biyun kuma suƙa ɗauki hanyar Gombe. a gidan Alƙali aka yada zango, dan su da kansu suka turo motar ɗauko amarya a airpot, su Dadda sun sami tarba me kyau a wajen su Hajiya Madina, sun ga mutunci da karamci tsurarsa, lokacin da su Dadda zasu damƙa Fillo a hannun Mum sai ta girgiza kai tana yi musu nuni da Hajiya Madina ta ce,"ai ga mahaifiyar tasa can". Inna Hajar ta miƙa hannun Fullo akan ƙafafun Hajiya Madina tana faɗa ma ta ga amanar ƴarsu, Maama na murmushi me faɗi da jin daɗi take shaida musu sun karɓa, kuma insha'Allahu ɗan su ba zai bayar da kunya ba, Fillo sai ta rinƙa jin kamar ayau ne ta fara shigowa gidan Alƙali, kuma kamar ayau ne ta fara sanin su Maama dan duk sai take jin su sababbi a wurinta, a cikin hular alkyabbar da ta rufe mata ido banda kuka babu abin da take yi, ƙwayar idonta baƙin rubutun da ke ɗauke da adadin sakin da Turaki ya yi ma ta kawai ta ke haskowa, tana jin muryarsa na ƙara karanta ma ta a kunnenta. sai wajen ƙarfe uku sannan ƴan taraba waɗanda Dada ta zaɓa zasu zo Dinner suka zazzo, ciki kuwa har da ita kanta, tasha wanka na kece raini kamar ba tsohuwa ba, less ɗin jikinta kansa abin kallo ka ƙara kalla ne. sai ƙarfe takwas na dare tukunna aka fara shirin tafiya Dinner, faɗar haɗuwar da amarya tayi ma ɓata lokaci ne, alƙalami ma ba zai iya ba, ta yi kyau iyakar kyan da ƙaryar baki ya ce zai iya faɗa, wata arniyar doguwar riga ce da Maama tasa Samha tayo order ɗin ta daga europe aka taho da ita, kana kallo kasan kuɗi aka sa ba kaɗan ba aka saya rigar, shigar pink aka yi ma ta wanda hasken fatarta yayi bala'in ɗaukar colour ɗin, abin ba'a cewa komai sai dai masha'Allah. sabuwar mota fil wacca Mum ta bawa Turaki a ita zaa ɗauketa, Raudha da Maijidda su kai ma ta rakiya har bakin motar da Bello ne ke zaune a driver seat, aka buɗe mata bayan motar ta shiga, san da zamanta ya daidaitu lokacin balaƴaƴƴan ƙamshin turaren da ta san shi kaɗai yake amfani da shi taji ya doki hancinta, ta yi saurin ɗago kai tana kallonsa, ta gan shi yana kallon gefe guda da alama
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243