Chapter 229
Chapter 229
kunnuwan kowannen su, furucin da yay akan soyayya, sai kawai suka ji su na shuɗawa zuwa duniyar baya, wani lokaci me tsayi da ya shuɗe, kamar haka ne, kamar wannan lokacin su na zaune da ita take faɗa musu... _"ku nuna min soyayyar ku ko bayan raina Ƴaƴana, ina nufin kar kuyi kuka da rashina, adu'a za ku yawaita yi min"._ Turaki ya matsa kusa da makarar, Baffa ya kalle shi, zuwa yanzu idanuwansa ƙamas babu alamun danshi na hawaye, haka fuskarsa tayi fayau babu wani abu da zaka tsinta a ciki illa tsananin tashin hankalin da yake ciki. haka shi ma Khaleel, wanda tun ɗa zu sai ayanzu da ya ɗora hannunsa akan makarar sannan hawaye yay nasarar gangaro masa, sai dai yay saurin saka gefen rigarsa ya goge. hannun Turaki ya shiga cikin maƙarar, ya tallafo kan gawar, yasa ɗaya hannun ya yaye linkafanin ya tsayar da shi daidai wuyanta, inda fuskarta kawai suke iya gani, fuskar da suke gani tamkar zata yi musu magana. muryarsa ta fito cikin sanyi, ya shiga jero tarin adu'oin da ya san su na cikin kansa, yi yake yi yana ƙara maimaitawa, har tsawon lokacin da bai san ya ɗauka ba me tsayi, har sai da Baba Nafi'u yasa hannu ya dafa kafaɗarsa yace,"ya isa haka Turaki". shi kaɗai ne ya iya yi masa magana domin ko Baffa ba zai iya ba a wannan lokacin, shi kansa ya kifa kansa yana hawaye kamar yanda Hajiya Ramla da ƴaƴan suke yi. "ke kam taki tayi kyau Madina, tabbas ke ɗin ƴar aljannah ce, ki yafe min Madina, don Allah don Annabi ki yafe min". muryar Boɗejo suka ji ta amsa acikin ɗakin, a sanda take isowa wajen, kuma kukan da yaci ƙarfin ya hanata ƙarasa abun da zata faɗa. har aka yi sallar jana'iza Turaki da Khalil basa cikin hayyacinsu sosai, a tsaye kawai suke, hannayensu sarƙe dana juna, yayin da idanunsu ke kafe akan makarar da ke ɗauke da gawar dake gabansu. da ga bayan su kuma tarin ɗumbin jama'ar da ba zasu ƙirgu ba ne, don jama'ar gari yara da manya sun halarci jana'izar. ƙarfe shida na yamma aka kai Hajiya Madina ƙabarinta, inda ɗumin jama'ar da suka fi ƙarfin ƙirga suka yi mata rakiya zuwa gidanta na gaskiya. acikin shirun da ya ratsa maƙabarta, babu sautin muryar da kake ji na tashi sai na manyan mutanen dake cewa. "yauwa bismillah ku biyo ta nan". "yauwa jama'a a ɗan gyara". "ku riƙeta sosai". "to ku miƙota nan". "yauwa to ku ajiyeta nan, masha'Allahu!". mutanen da suka ratso ɗauke da gawar ta cikin tarin ƙaburburan dake jere a cikin maƙabartar. suka ajiye makarar a bakin ƙasar da aka tone, kusa da ramin da yake gida matabacci, kuma gida na ƙarshe ga kowanne bawa, gidan da ke jiran duk wani mai rai, gidan da yake iri ɗaya da na me kuɗi da na talaka. Turaki da Khalil na tsaye kusa da juna, tsayinsu kusan ɗaya, zuciyar kowanne na tunani kala-kala a game da mutuwar da ta riske su a yau. abun da basu taɓa zato ba, abun ba su taɓa kawo shi nan kusa ba. "Bismillah". Muryar limamin masallacin unguwar ta janyo Turaki da Khalil daga dogon tunanin da ƙwaƙwalwar su ta faɗa, suka juyo a tare suka kalle shi, sannan suka kalli gawar dake gabansu, wadda aka fito da ita daga cikin makara, a lokaci ɗaya suka tsinci kansu da tarin ruwan hawayen da ya bar idon su tun ɗazu. a hankali Turaki ya durƙusa daidai kan gawar ya tallafo kan, Khalil da Samir da Baffa da Wan Hajiya Madina da Liman suka tallafi sauran jikin, sannan suka haɗu wajen zura gawar a cikin ramin ƙabarin. lokacin da suka zura gawar acikin rabin ƙabarin, zuciyar kowannen bawa dake wurin ta matse da ƙarfin imanin dake ƙaruwar a ƙirjinsa, tabbas duk wanda bai yarda da Ubangiji ba yayi asara, asara mai girma kuwa, haka duk wanda bai tuba ba kafin mutuwa tabbas yay babbar asara. idanuwan Turaki suka tsaya cak akan farin likkafanin, yana kallon yacca ake mayar da ƙasar da aka haƙe ana rufe gawar gawar da ke ciki, har sai da hasken likƙafinin ya dusashe, yayin da tukwane da tudun jar ƙasa suka shafe shi gaba ɗaya. daga wannan lokacin kuma ƙwaƙwalwarsa bata ƙara wani tunani ba, komai da ke cikin kansa ya zame yabar shi. abin da zai ce yana iya jiyowa a duniyar da yake jinsa kamar ba'a cikinta ba, tarin adu'oin dake fitowa daga bakin liman, kafin a hankali kuma ya fara jin sautin wani abu na shiga kunnensa, sautin takun ƙafafu su na juyawa su na barin wajen. sai ya kalli nasa ƙafafun, sai yake ganin tamkar ba zai iya ɗaga su ba, tamkar sun ƙame anan kenan har sanda tasa mutuwar zata zo ta riske shi. yaji an riƙo hannunsa, da ƙyar ya iya ɗauke idonsa akan ƙabarin, ya juya ya kalli Baffa da Khalil, kafin ya ɗaga ƙafarsa a hankali ya fara tafiya da baya, a haka ya dinƙa tafiya da baya har ya bar cikin maƙwabartar, yana tafiya yana barin Hajiya Madina, yana kusantar gidan da zai koma a yau rana ta farko ya riske bata cikinsa, rana ta farko da zai koma bai ji muryarta ba na kiransa da wannan sunan da ita kaɗai ta raɗa masa, kuma ita ɗaya take kiransa da shi, Me Babban Suna!. yaji wani uban gumi ya keto masa, ya wanke masa dukkan ilahirin jikinsa, a hankali kuma ƙwaƙwalwarsa ta karanto masa kalmar innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. shikenan sun yi tazara, tazarar da ba zasu ƙara kusantar junansu ba. a lokacin da suka koma gida, tsakanin Khaleel da Turaki sai aka rasa wanda ya riga wani shiga ɗakin Hajiya Madina, an dai gansu sun shigo sun tsallake tarin mutanen dake zazzaune. a cikin ɗakin na Hajiya Madina, Khalil na zaune a ƙasa, idonsa na manne akan gadon inda tayi baccin ƙarshe a duniyarta, yau rana ta farko da ya shigo ɗakin bai ganta ba kuma ko da ya zauna zaman jiranta ba zata shigo ba, shikenan ta tafi tafiya ta har abada, sun zama marayu, yanzu ba su da uwa, wannan jigon na jin daɗin duniya. a hankali yaji hawaye na sauka akan kumtunsa, masu ɗumi da yawan da yaji kamar an buɗe bakin famfo, kukan da bai yi ba tun a ɗazu shi ya taho a yanzu, kawai sai ya ajiye dukkan dauriyarsa, yay ƙasa da kansa, ya runtse idonsa da yake ganin hoton mahaifiyar tasa na haska masa, don haka saiya shiga rero kuka babu ƙaƙƙautawa, kuka tamkar ƙaramin yaro. a wannan lokacin kuwa Turaki ya kifa kansa akan gadon, ƙamshin Maamansa na fitowa daga kan gadon na ziyartar hancinsa, yayin da yake damƙe da wannan ƙaton zanin da take cewa zanin goyon jikanta ne. _"kwana ashirin da biyu ya rage Edd ɗin nata ya cika ko?, to Allah ya raba su lafiya. kaga Me Babban suna waɗan su gadaje na jarirai na gani da suka fi wanda na siyo kyau, mu sauya shi ko?"._ maganartata ta haska acikin kansa, shekaran jiya suka raba rana su na hira da ita, kuma yawancin hirar duk akan jikokin da taƙe ta burin ganin zuwan su ne, har daga
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243