Skip to content
NovelPress

Hausa Novels

Chapter 206

Chapter 206

Lullubin Biri Book 1 Complete Hausa Novel 1,231 words 0 views Progress saved
Download Book

aure, al'adar bature duk ta ɓata mana yara suyi ta zama suƙi aure". Fillo ta ɗaga ido yanda ba za'a lura da ita ba, ta sauke su akan Turaki da ke can cousin sisters ɗinsa sun baibaye shi, tayi dariya tana kallon yanda ya riƙe wata ƴar Baby yana cewa da Mamanta ta karɓi kayarta kar tayi masa fitsari ko kashi, ta karɓeta tana faɗin taga yacca zai yi ranar da aka haifa masa tasa, ba kashi ko fitsari ba tumbuɗi kaɗai ya ishe shi, Allah na tuba kwana nawa suka rage. kuma kamar ya san Fillo na kallonsa a lokacin, sai ya ɗago karaf suka haɗa ido, ya langwaɓar da kai ta sakar masa murmushi, shi ma yay murmushin yana kanne ma ta ido ɗaya, yau duk sai yanzu tayi masa murmushi, dan tun tashinta take faman cin magani, shi kuma bai takura ma ta ba dan ya san abin da yay ma ta ne jiya. gida dai sai ya koma kamar gidan biki, don har wata walima suka haɗa wai ta murnar zuwan Mum, wacca tun bayan dawowarta bata sami zuwa ba, Fillo kam sosai taji daɗin zuwanta, kuma nan da nan duk sai ta sake sosai, irin Family ɗin nan ne masu saurin sabo, kuma masu sauƙin kai da mutunta wanda ya shigo cikin su. da yamma su na zaune a bedroom ɗin Granny wata me suna Nilfat ta shigo, ta kalli Granny tace,"duk kinga balarabiya kin maƙale mata". Granny tayi ma ta daƙuwa tana cewa,"ungo nan". Nilfat ta ce,"na gode, ai ba zan bari muyi faɗa ba, dan lallaɓaki nake na bi ki europe nima naje na samo irin wannan sulɓin fatar taki da bata tsufa". ta wuce wajen Fillo tana cewa,"ki je inji mijinki". Hajjah Yayar Granny ta ce,"kije kice masa ba zata zo ba, ashe shi ma irin Ahmad ne bai da kunya". "yaran yanzu ne fa, ai sai adu'a kawai, amma kunya ina suka ganta". cewar Granny. "to Hajjah tafiya fa zai yi, ai sallama za su yi ba wani abu yace zai yi mata ba". Nilfat ɗin ta ƙara faɗa. Hajjah ta ce,"kije kice masa yay tafiyarsa, dole ne sai sunyi sallamar, kaji min mara kunyar yaro, ko wani abu zai bata". Nilfat tayi ƙofa tana faɗin,"ni dai ban taɓa ganin inda akayi irin haka ba gaskiya, ya zai tafi ba tare da yay sallama da matarsa ba, wallah idan ni ce sai ince ta fasa zama, in ɗau kayata mu tafi, yo in ma ba sallamar zai yi ba ina laifi anan dan miji ya nemi matarsa". Fillo dai na kusa da Granny kanta a ƙasa, har ga Allah so take taje ta gan shi, tun ɗa zu rabonta da shi wai sun fita shi da wani Baffayo ɗan gidan Anty Hajar. Mum ta shigo a lokacin, ta zauna tana cewa,"wai Babana zai tafi, jirgin ƙarfe bakwai zai bi, daga masallaci zai wuce". sai ta kalli Fillo tace,"je kuyi sallama". sai ta kasa sakkowa, duk kunya ta kamata, ga shi ita ba waya ba balle tayi masa text tace ya tafi kawai, sai da Mum ta ƙara yi ma ta magana sannan ta sauko akan gadon ta ɗauki mayafinta ta fita. a compound ta tsaya tana kalle kallen inda zata gansa, Fareeda na zance daga can wajen flowers ta ƙwala ma ta kira,"Antee". Fillo ta ɗaga kai da murmushi tana kallonta. ta ƙarasa wajen na su, Farida tace,"ga wanda zan aura". "masha'Allah". Fillo ta faɗa kafin su shiga gaisawa da Modi. Farida ta ce,"mijinki ba?". Fillo ta ɗaga ma ta kai. "yana ɗakin Baffayo". "ina ne ɗakin?". "ki zagaya ta wurin shukokin nan, ɗaki na tsakiya me bishiyar ayaba a gabansa". Fillo tabi hanyar da Farida ta nuna ma ta, tun daga ƙofar ɗakin ta san Turaki na ciki saboda ƙamshin turarensa da duk ya cika wajen, ta shiga ɗakin bakinta ɗauke da sallama. Baffayo ne ya amsa sallamar, Turaki kuma ya ɗaga kai yana kallonta, Baffayo ya fita a ɗakin, ita kuma ta zagaya ta zauna akan kujerar da Turaki yake, ta shige jikinsa kamar yanda ya buɗe ma ta hannu. "yau ni kike gudu ko?". ta ɗago kai tana kallonsa ta ce,"kaima ai mantawa kayi da ni ka tafi wani wajen". yaja hancinta,"munje gidan wani Kakanmu ne, ƙanin me sunana, da naje suna ta tambayarki nace za ku zo ke da Mum". "to me ka siyo min?". "ɗa zu ba gani nayi kin saka fura agaba kina sha ba, ko irin ma ki tuna da mijinki a kusa". "to a gaban su Mum ɗin zance kazo ka sha?". "ni ma shiyasa ai da naje Alhaji ya ban abin daɗi ban iya cewa zan ragewa Matata ba". tai murmushi da kiran sunansa,"Turaki". ya ce,"na'am Halima". ta ɗan bugi kafaɗarsa,"sunan fa Ummi ne". yasa hannu ya rufe bakinsa,"Allah na tuba ka yafe ni". sai kuma ya kama kumatunta yana cewa,"to ni ma ai sunan Abba ne kike faɗa". "to ai dai ba ainihin sunansa na faɗa ba, Turaki na ce". "ehh haka ne afiruwa". ta turo baki gaba,"mene afiruwa?". "ɗan siririn mutum da za ki gansa kamar lamba ɗaya, kin san one bata da kauri kwatakwata". ta shiga kai masa dukan wasa, shi kuma yasa hannu yana karewa yana dariya har sai da ya kama hannayenta ya riƙe. "ai indai ƙiba ce zan yi". yace,"ni ma na san da wannan, aikina kawai zanyi". sai kuma ya kalli agogon hannunsa ya ce,"za ki sa nayi late, jirgi ya tashi babu ni, tun ɗazu na aika ki zo kika ƙi, da nayi tafiyata ai". "da ni kuma yau banyi bacci ba nayi ta kuka, saboda duk yau nayi kewarka ban ganka sosai ba". "ehh ba ke bace naga yau duk kina ta shareni, kawai saboda na saka kinji daɗi jiya". ba shiri tasa hannu ta rufe fuska, ya ɗauke hannun yana faɗin,"idan kika tashi dawowa ki dawo da babban shiri". "shirin me?". ya goga hancinsa da nata yana jan haɓarta,"sai kin dawo ɗin dai, ke dai kawai kici tuwon dawar Innah kiyi ƙarfi". ta cuno baki tana faɗin,"ni dai sai ka faɗa min shirin me?". "shirin karatu". "wanne karatu?". "karatun manya". "wanne karatun manya kuma?, ni ban sansa ba ai". ya ɗora hannunsa saman cinyarsa ya tallabi haɓarsa yana kallonta ya ce,"karatun da zai mayar da ke cikakkiyar matar aure". ta ɗan murguɗa baki bata ce komai ba. ya lanƙwasa yatsanta ya ce,"ni dai kici tuwon dawa da yawa kiyi ƙarfi, don karatun ba na wasa ba ne, Mum tace 7days za kuyi, ni kuma 7days yay min yawa, dan haka ki dame ta ku taho jibi". tai lamo da kanta a kafaɗarsa tana cewa,"kamar ma kar na koma ai, family ɗin ku suna da kirki sosai". "ni ma haka suke ta ce min wai nayi sa'ar mata me hankali da mutunci, anyway yanzu dai faɗa min when zaku dawo?". ta ce,"to ka zauna anan mana kaima". "kije ki faɗawa Mum hakan". suka miƙa yana manneta a jikinsa,"7days yayi yawa Fulani Nah, ki faɗawa Mum hakan". ta ce,"7days yayi kaɗan Turaki, ina so zanje inga Ummi nah, kaga babu nisa daga nan". bai ƙara cewa komai ba ya kama hannunta suka fita, lokacin Baffayo har ya tayar da mota, yay ma ta side

Table of Contents

Chapters

243 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243