Chapter 10
Chapter 10
kana tsoron kada uwarka ta tsine maka...". Yusuf yay saurin katseta da cewan,"Ammi don Allah ki daina irin wannan maganar...". Itama bai ƙarasa ba ta katse shi da faɗin,"an riga an shanyeka ai duk gaskiyar da zan faɗa a iska zaka dinga jinta". Yay shiru bai ce komai ba, ta ƙara cewa,"ka tashi ka kaini airpot". Yay saurin miƙewa yana karɓan jakar hannunta suka fita tare. Tunda suka shigo motan babu wanda yay magana, har ga Allah Yusuf naso yay hira da mahaifiyar tasa amma yana tsoron ta balbale shi da faɗa, dan yanzu da abunda yake na faɗa da wanda ba na faɗa ba duka na faɗa yake zamar mata indai tsakaninta da shi ne. Tunda yazo ma yake son mata albishir da cikin Nuratu amma yana tsoron abunda hakan zai haifar, dan bata ƙi ma tai muguwar adu'a ba tunda ba son auren nasu ta ke ba, ita duk abunda ya shafi Falmata to shikenan ta ɗaura gaba da shi, yasan da ace Nuratu ba jinin Falmata bace Ammi zata ɗan rangwanta masa akan ƙin zaɓinta da yay. Maganarta ta kutsa cikin tunaninsa. "yarinyar da na so na haɗaku ce za'ai bikinta. Da yake Allah ba azzalumin bawansa ba ne sai ya haɗata da wanda ya fika. Ɗan governor ɗin Jigawa ne, yaron ance a ƙalla ya mallaki sama da miliyan 500. Shi ɗaya ne a wurin mahaifinsa, babarsa ita ɗaya ce for morethan 35years da suke tare da mijinta...ba irin Babanka ba da shekara 15 muka ɗauka tare yaje ya ɗauko min annoba". Yusuf yace,"Allah sanya albarka a auren nasu". Aciki ta amsa masa, yana kallon yanda ta ke hararsa ta cikin window, tunda yake da ita ba su taɓa fita tare ba ta shiga back seat ba sai yau, tunma bayan auren nasu dama bata yarda ta shiga motarsa, hanya ma bata so su haɗa da shi. "Ammi Nuratu ta kwan biyu bata da lafiya". Ya faɗa cikin kwantar da murya. Ammi ta dakata daga danna wayar da ta ke yi ta ɗago ta dube shi, kamar ba zata ce komai sai can kuma a hankali tace,"bata da ƴan'uwa ne?". Ya rumtse idonsa sosai kamin yace,"tana da su mana Ammi". "ohh tou kuma kazo kana faɗa min bata da lafiya, ai su zaka je ka sama bani ba da ban haɗa dangi da ita ba". Bai ƙara cewa komai ba yay shiru, Sani Abacha International Airport ya ajiyeta, bai baro wajen ba sai da jirginsu ya tashi tukunna. Yana kan hanya abokinsa Dr Huzaifa ya kira shi, saboda haka ya yanke hanya ya biyo ta shongo estate. Slowly yake driving ɗin, Idonsa na kallon left side yana kallon wani gini da ake ƙarasawa, idonsa ya sauka akan yashin da tifa ta juye yanzu ta bar wajen. Kamar wanda ya tuna wani abu sai ya waiga yana daɗa kallon wajen da ya bari, hoton wannan yarinyar ya haska a cikin idonsa a wancan lokacin da ya taɓa wucewa ta wajen. Tana zaune a gefen yashi ta ƙudundune tana rera kuka a hankali, ta riƙe siririyar doguwar ƙafarta tana kallon wajen da taji ciwo cike da tashin hankali. Gaba ɗaya ciwon ba wani babba bane, amma kace wadda akace ƙafartata ce ta ruɓe za'a yanke saboda kawai jinin da ya fito a wajen ɗan kaɗan. sai yaga kamar yanzu ne abun ya faru, dan bai san lokacin da leɓensa ya tale da murmushi ba tunawa da yay da irin dramar da suka sha da ita akan kawai ta bari ya saka mata bandage akan ciwon da taji. _"jinina zai ƙare"._ Haka ta faɗa masa a lokacin da ya tsuguna gabanta yana tambayarta me ya faru, cikin muryar kuka, kuma duk da cewar muryar tata ɗauke ta ke da kukan da tasha, hakan bai hana daɗin muryarta fitowa ba. Ta runtse ido ma ta kasa kallon ciwon, ya koma mota ya ɗauko first aid amma ko da ya dawo sai ya tarar bata wurin, abun yay matuƙar bashi mamaki a sannan, dan zatonsa ma ko aljana ya gani ko kuma aljanu suka buɗe masa ido yau, saboda kyan yarinyar ma yafi kama da na aljanu. Kuma sai can zai bar wajen ya hangeta ta ɓoye a bayan bulo, ashe first aid box ɗin da ya ɗauko ne yasa ta guduwa. [8/8, 00:57] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *HalimaAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* *6* Yau ya kasance juma'a. Ƙofar gidan na Judge Dikko Habib cike yake da ɗumbin mutane masu zuwa karɓan sadaqa, yara da manya musamman ma magidanta marasa ƙarfi, haka gidan yake kasancewa a duk wata juma'a, zaka ga mutane babu masaka tsinke tun an idar da sallar asubahi sun bi layi su na jiran fitowar Mai gidan. Judge Dikko Habib babban alƙali ne wanda ake damawa da shi a manyan shari'ar da ta shafi cikin ƙasa da wajenta, kuma alƙalin da gwamnatin tarayya keji da shi. Dattijon ƙwarai mai halin dattako da nagarta, Yawancin zamansa a america yay, karatunsa ma tun daga secondry har matakin phd duka acan yayi. Matansa Biyu Hajiya Ramla da Hajiya Madina amma ainihin sunanta Aina'u, Ƴaƴansa 6, uku maza uku mata. Kuma kaf cikinsu babu wanda ke karatu a nigeria duka waje yake fitar da su. Turaki ne ma kawai yayi secondry a nigeria kamin ya fita US yay degree da masters ɗinsa acan. Idan yazo zai bawa kowa sadaqa zai ba shi kuɗi dubu uku, sai ma'aikatan gidan maza su bika da kwanon shinkafa, taliya guda biyu da kwalaban farin mai da manja. Judge Dikko ba ya taɓa barin wajen har sai ya tabbatar da kowa ya samu, duk kuwa da uban yawan da mutanen ke da, ba ya gajiyawa kuma ba ya ƙosawa, hakana duk nisan tafiyar da yayi duk irin muhimmancinta zai katse kome yake yi ya dawo alhamis dan kawai waɗannan mutanen da Allah ya ba shi ikon taimaka musu. Ya faɗa saveral times gani yake idan har ba shi ne da kansa ba to ba za'a riƙe amana kamar yanda ya bayar ba, saudiya kawai yake tafiya ya iya haƙura, shima kuma sai ya kira Muhammad Turaki a duk inda yake ya dawo ya tsaya akan ragamar abun, dan shi kaɗai yake ganin zai iya kwatankwacin abinda shi zai yi da kansa. Kuma a wannan juma'ar ne ma'aikatan gidan basa samun hutu ko kaɗan, dan tun daga safe har dare su na rabon abincin sadaqa. Ƙarfe goma da rabi Baffa ya dawo cikin gidan daga rabon sadaqar da ya fita, Khalil da ke ƙoƙarin shiga motarsa zai fita ya hange shi, hakan yasa ya rufe motar ya taho da sauri. Ya rissina a gaban mahaifin nasa cike da girmamawa yana faɗin,"Barka da dawowa Baffa". tare da miƙa hannu don karɓar jakar hannunsa, wadda yake zuba kuɗin sadaqa ya fita da ita. Baffan ya dube shi yace,"ba fita zaka yi ba?". "fitar ba wata mai muhimmanci bace". Ya faɗa yana ƙara miƙa hannu don amsar jakar. Baffan ya miƙa masa, shi kuma yana masa sannu tare da adu'ar Allah ya bada lada a irin ayyukan alkhairan da yake yi. Tare suka jera su na tafiya, su na entrance na shiga parlo Baffa yace da Khalil. "Muhammadu ya dawo ne?". "a'a bai dawo ba". "amma ɗazu sai naga motarsa". "ai dama ba
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243