Chapter 228
Chapter 228
mutanen cikinta na tirr da mu ba, ya Rahmanu kasa kar mu mutu da hakkin kowanne bawa akan mu, don mun san cewa baka yafe hakkin wani akan wani, ya jama'atul musulim mu yafi juna!, mu yafewa junan mu!, kar mu dinga ƙullar junanmu domin ba mu san lokacin da zamu yi tafiya me gaba ɗaya ba. "ta mutu". Khalil yay ƙarfin halin furtawa sauran ƴan uwansa da kowannen su ke tsaye yana so ya fahimci abin da ke faruwa. "Kamar ya ya wai? Mecece mutuwa kuma?". Sameer yay tambayar a rikice. "da ma haka ake mutuwar?, ɗa zu fa muka gama hira da ita ko awa ɗaya ba'a yi ba, haba this is insane, wallahi Dr ɗin nan ƙarya yake, ya za'ai ma Maama ta mutu, me tayi?, laifin me ta aikata?, don Allah Mum a kira wani likitan ya dubata, don Allah a kira wani likitan ya zo ya tasheta". idan ace ba kallon fuskar Nihal suke yi ba, za su rantse da Allah cewa ba ita tayi wannan maganar ba, don kwatakwata muryar ba tayi kama da tata ba, ta fito ne cikin wani amon sauti na ƙololuwar tashin hankali, tana rawa tamkar iska na kaɗata. haka rayuwar take dama, hanya ɗaya ce da ita, ko kabi tafarkin gaskiya ko ka kauce duk dai ƙarshe waje guda kowa yake nufa, alkhairi ko sharrin da kayi kafin ka ƙarasa, shi zai zama shimfiɗa mai kyau ko mai muni a yayin da ka isa, sai dai fatan dacewa kawai. "ka kira Baffan ku ka sanar da shi, sai ka kira min Samha da Zaytun, amma ban ce ka faɗa musu ba". Mum tayi furucin ga Khaleel, wanda yake tsaye har yanzu hawaye sun gaza sauko masa. a wannan lokacin kuwa Nihal na kan gawar Hajiya Madina, tana girgizata akan sai ta tashi, tana roƙon su akan su kira likita me hankali ya tashi mahaifiyarta, ai hirar da suka kwana jiya su na yi baya nufin wasiyya ta bar mata, ita dai azo a tashi Maama, don tace mata a ƙarshen watan nan zata fara yi mata order ɗin kayan kitchen ɗinta. a wannan lokacin kuma Turaki ya iya ɗago da kansa, ya kalli Nihal ɗin sannan ya kuma kallon fuskar gawar, sannan ya ƙara kallon zanin da aka rufe gawar hannun Fullo ke damƙe da shi, sannan ya kai ƙwayar idonsa kan Mum da ke zaune kanta a ƙasa, hawaye na saukowa suna zuba akan kayan da ke jikinta, sannan ya kalli Sameer da ke duƙe ya rufe fuskarsa da dukkan tafukan hannunsa da alama kukansa yake so ya tsayar tukunna ya ɗago ya ƙaryata mutuwar, sannan ya kalli Khalil wanda ke jingine a jikin wadrobe waya riƙe a hannunsa ya ƙurawa gawar ido, gashin idonsa ba ya ko ƙiftawa. a wannan lokacin ne kuma hankalinsa ya fara gaya masa wataƙila zai sauya ma'anar rabuwa ta mutuwa a yau, don baya tunanin akwai abin da zai raba shi da gawar nan da yake riƙe da hannunta, Maamansa ba, babu me raba shi da ita. *BAYAN AWA BIYU.* a cikin wannan awannin, labarin rasuwar Hajiya Madina ya karaɗe cikin garin gombe, da sauran ƴan'uwa da suke na kusa da na nesa. lokaci guda tarin al'umma suka shiga ɓulɓulowa su na sauka a gidan Alƙali Dikko domin yin ta'aziyya, mutuwar da ta taɓa manya da ƙanan yara. cikin gidan ya ɗauki shiru, a zazzaune ake wasu na kukan fili yayin da wasu ke kukan zuciya, domin tabbas anyi rashi, an yi rashin mace mai tsanani son mutane da kyautata musu, mai kirki da sauƙin kai, macen da ke da tsananin kyautatawa marayu, macen da ba'a faɗa da ita acikin mutane in har ba ƴaƴanta aka taɓa mata ba, macen da a tsawon rayuwarta babu wanda ya taɓa buɗa baki yayi kuka da ita, ya kuma ya faɗi aibunta. a wannan lokaci ubangijin da ke da iko da zuciyar kowanne bawansa, shi kaɗai ya san adadin alhinin da ke cikin zuciyoyin ahalin gidan Alƙali Dikko, musamman yaran, waɗanda suka ruɗe da koke-koke, banda Samha da ke ta aikin suma tana farfaɗowa ta ƙara komawa. "an gama yi mata wankan, ku faɗa musu za'a shigo da gawar ciki su yi mata adu'a". "ina Hajiya Ramlan take?". "yanzu ta tashi, Samha ce jini ya yanke mata, ana tunanin ko ɓari tayi". a lokacin wani tsoho ya leƙo parlon yace,"to ina yaran su ke ne?". "Baba Musa gasu nan fa, ku shigo da ita ɗin". ya juya fuskarsa daga waje yana kallon mutanen dake tsaye yace,"sai kun ɗago makarar da kyau fa, yawwa kai ɗan karkata ta can". mutanen maza su huɗu suka shigo parlon da gawar, da yake acan part ɗin nata wasu Kakanninta mata da su Boɗejo suka yi mata wanka. su ka ƙarasa da gawar suka ajiyeta a tsakiyar yaran da ke zaune a ƙasan carpet, wacca Zaytuna ce kawai babu sai Samha da aka yi asibiti da ita yanzu. Baffa ya ƙaraso wajen ya zauna shima, zaman nasa babu wuya kira ya shigo wayarsa, daga can ɓangaren Zaytuna da ke ta kuka tace,"Baffa don Allah kar akaita sai na zo, ya tafi ya nema mana ticket yanzu zamu taso Baffa". "Zaytun kiyi haƙuri kinji ko, ki tayi mata adu'a kawai, idan aka ce za'a jira ku lokaci zai ƙure, kinga magariba na gabatowa". bayan gama wayar ya ɗaga kai yana cewa da Yayar Hajiya Madina,"Asiya kirawo Ramla don Allah, tazo su yi sallamar ƙarshe". "Baffa don Allah ku bar mana ita a haka ba sai an kaita wani wajen ba, mu zauna da ita a haka don Allah". Yayan Hajiya Madina Baba Nafi'u yace,"tun ɗa zu kake ta surutai Sameer, ya isa haka, kai musulmi ne ya kamata ka yarda da wannan mutuwar, batun a bar muku ita babu shi domin binne gawa wajibi ne". "don Allah Baba ku bar ta ko zuwa da safe ne, ƙila fa baccin ne yay mata nauyi da yawa, ko kuma shi likitan ne bai bincika da kyau ba, amma ɗazu mu ka gama hira da ita wallahi, wallahi lafiyarta ƙalau bacci kawai tayi tace idan Saamirawo(sirika Fillo) tazo to a tasheta". Nihal ke maganar duk a gigice. Baba Nafi'u ya ƙara cewa,"ku yi haƙuri kin ji Nihal, duk wani abu da ya ke faruwa tsarin ubangiji ne, namu tawwakali ne da addu'a, don haka ku yiwa mahaifiyarku adu'a". Baffa ya numfasa a hankali ya shiga kiran sunan yaran nasa da sirikan nasa ɗaya bayan ɗaya. "Khalil, Samir, Nihal, Halima, Ilham". sannan ya kalli Turaki daga ƙarshe yace,"Muhammad ku daure zuciyoyin ku, kuyi tawwakali ga Allah, wannan ita ce mutuwar, haka take, haka kowa yake haƙura da ita, haka take riskar kowanne bawa ba sai an shirya mata ba, mu ma nan duk jiranta muke yi. yanzu lokaci na tafiya, mutane na can a waje su na jiran a fita da ita, na san abin da kowannenku yake ji, na san raɗaɗin da zuciyarku ke yi muku. ku yi mata adu'a, wannan kukan da ku ke yi da musawar da ku ke yi ba gata bane a wurinta, zallar soyayyar da za ku nuna mata shi ne kuyi mata adu'a, wannan jinkirin kaita ɗin da ake ba alkhairi bane agareta". Maganar ta Baffa ta doki
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243