Chapter 168
Chapter 168
idan ya dawo ya tarar ba ta daina ba sai ya zaneta babu ruwansa da matar aure ce". Raudha ta sauke numfashe ta ce,"i never see such a kind person me shegen kuka ma irinta, da muna saudia zatona ko dan Dada ta ce sai an saketa ne, da muka dawo kuma na kasa fahimtar auren ne bata so ko kuma kukan barin gida ne". "kin taɓa ganin amaryar da take kuka irin haka dan zata bar gida?, ita dai barta dan ta ga ƴar auta ce shagwaɓa tayi mata yawa shiyasa". AmaturRahman ta faɗa tana wucewa toilet. Raudha ta zauna kusa da Fullo tana kamo hannunta ta riƙe, ta ɗau wayarta tana kiran lambar me makeup da zata zo ta yiwa amarya anjima da za su yi Fulani Day, bayan sun gama wayar suka ci gaba da maganarsu ta abubuwan da zasu yi anjima. ƙarfe uku na rana aka fara shirya amarya, wata cousin ɗin su da ta zo daga benue tana ta complain akan rashin zuwan ango da aka ce ba zai zo ba, har sai da aka ce mata ai baida lafiya tukunna ta sarara ta hutar da yawun bakinta daga masifa. ita dai Fullo duk babu walwala, ƙwayar idonta na manne a cikin mudubi kai kace kanta take kallo, nan kuwa hoton ranar da suka je asibiti ne kawai ke haska mata. ta tuno sanda suka shiga room ɗin da Turaki ke kwance an saƙala masa oxygen, ga wasu abubuwa da akayi masa connecting, kallo ɗaya dai zaka yi masa idonka ya cika da ƙwalla haka kuma kaji tsoron Allah ya kama ka. ita da ta gansa ma sai da tayi mugun tsorata saboda kumburar da ya yi kamar an hura shi, a yacca yake ma zaka ce gawa ce, har yanzu ta kasa kwatanta abin da taji a lokacin da ta gansa da kuma abin da take ji zuwa yanzu. kawai sai ta rufe idonta tana hasko lokacin da ta gyara masa zaman hannunsa akan gadon a sanda ya buƙaci hakan, lokacin da taji ta kasa rabuwa da hannun nasa ta riƙe tayi masa irin riƙon da bata taɓa yiwa hannun wani mahaluƙi ba, har yanzu tana jin sautin muryarta a kunnuwanta da suka dinƙa fita da amo na tsananin tausayi suna jera masa kalmar sannu tamkar yawun bakinta zai ƙare, kuma a sanda take ji a jikinta kamar yana buƙatar wani abu daga gareta sai taji ya riƙo ɗaya hannunta ya zura ma ta farar takarda, wannan farar takardar da ke ɗauke da baƙin rubutu me ɗacin ɗanɗano, rubutun da take ji gwara a soketa da mashi akan abata karatunsa kuma a alaƙantata da shi, rubutun da taji ya tsayar da wani dunƙule abu a maƙoshinta ya hana ko da yawu wucewa, ita dai ta san ko kaɗan bata son Turaki, daidai da bugawar sakan na agogo ba ta taɓa jin wani abu me kama da sonsa a cikin zuciyarta ba, tausayinsa kawai take ji wanda shi ma daga Allah ne, amma ta rasa dalilin da yasa ta damu da sakin da ya yi mata, ta rasa reason ɗin da yasa take jin kamar ta mutu akan wannan sakin. ƙwayar idonta ta ƙara haska mata san da ta ɗauki tsayin daƙiƙu uku tana kallon takardar kafin ta iya ɗauke idonta daga kai ta sauke su akansa da yake kallonta da wani rauni da zata iya cewa ta gani acikin ƙwayar idonsa, ta san lokacin da idonta ya manne acikin ƙwayar idonsa, amma ba zata ce ga sanda hawaye masu azababben zafi suka shiga sauko ma ta ba, ta san dai ta ɗau tsayin lokaci tana kallonsa har sai da shi ya ɗauke nasa idon akanta ya kauda fuskarsa gefe, kauda fuskar da yasa taji kamar an tsikareta, tayi saurin miƙewa tana sakin hannunsa da ta riƙe ta fita da ga room ɗin tana danne kukan da yake cinta, kukan da har yau kowa ya rasa na menene har da ita kuwa, kuma kukan da har yau yaƙi tsagaita ma ta. hawaye su ka sauka akan foundation ɗin da me makeup ke blending ma ta, me kwalliyar taja tsakin ƙorafi tana matsawa da baya da cewar,"haba ke kuwa don Allah, haka fa jiya ma kika yi mana ki kasa akai ta westing time. idan ba za ki iya daina kukan ba kice a fasa yi miki mana ki daina wahalar da ni, ni wallah ban taɓa ganin amarya me masifaffan kuka ma irinki ba". tai maganar da muryar ɓacin rai. kowa sai ya hayayyaƙowa Fullo akan kukan da take yi sam bai dace ba, ran kowa ya ɓaci aka fara fita daga ɗakin ana barinta, Maijidda da tsananin tausayinta ta kamata suka shiga toilet ta wanke ma ta fuskar sannan suka dawo, me kwalliyar taƙi tasowa, duk da kuɗi za'a biyata masu yawa bata jin za tayi ta yin aikin wahala haka, har sai da Ammi ta shigo tayi magana tukunna ta miƙe tana jaddadawa Fillo akan kar ta ƙara ɓata ma ta aiki. sharp sharp akayi kwalliyar da tayi bala'in haska Fillo, ta dawo tamkar ba ita ba, aka fito da ita cikin shigar fulani kamar ka saceta ka gudu, Maijidda ta dinga roƙonta akan ta daure tayi murmushi ta kore damuwar fuskarta kar tayi musu irin ta jiya, duk ta yanda ta so ta yi hakan ta kasa, har sai da suka shiga parlon Maudo taji Dada na ba da labarin. "ehh mana, ai ni ban taɓa ganin ƴar banza mata ba irin wannan tsohuwar, ke ni da naje asibitin ma ban san sanda na tofar da yawu ba da na ganta, kin ganta kuwa a fige kamar figaggiyar kazar da bata kama abinci ba, naji haushin kaina ma da na zauna waje ɗaya ina ta masifa banje munyi ido huɗu da ita ba tun farko ta raina kanta, muna haɗa ido na zabga ma ta harar da ta fi tata, tana ta maganganunta ni dai na kirawo likita nace masa ga sabuwar mara lafiya nan". ba ta san lokacin da siririyar dariya ta suɓuce ma ta ba, kuma cikin sa'a Nuratu ta ɗauketa hoto a lokacin, hasken camerar yasa ta ɗago ido karaf camera woman ma ta ƙyasta ma ta, sai kawai taji abun ya burgeta hakan ya bayyanar da dukka kyawawan fararen haƙoranta, suka fito cikin wani salo na burgewa da ɗaukar hankali, idanuwanta su ka yi wa ta lumshewa suka buɗe ta kalli me hoton da irin kallon da ke tsuma zuciyar duk wani lafiyayyan namiji. tafin da aka fara ana waƙa irin ta su ta fulani sai taji a lokaci ɗaya yana tafiya da damuwar da take ciki, yana tafiya da wannan tarin hawayen da ke cikin ƙwayar idonta yana musanya shi da murmushi me faɗi. *Gombe.* "ka yi wankan?". Bello ƙaraye ya tambayi Turaki lokacin da ya sakko daga upstairs. Turaki bai ce da shi komai ba ya wuce dining, da ga yacca yake tafiya zaka san bai gama warwarewa ba, har yanzu jikin nasa da saura, duk ya bi ya rame, Bello ya taso shi ma ya isa dining ɗin yaja kujera ya zauna. "me za ka ci na zuba maka?". ba tare da Turaki ya kalle shi ba yace,"mene aciki?". Bello yana nuna masa flask na
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243