Chapter 13
Chapter 13
gaisheta kuma har haɗa ido sunyi, tana lura da yanda Kaka ke aikin jefa mata harara amma tayi fuska, shi yasa itama Kaka ɗin taita adu'a a ranta Allah yasa kar Zaytuna lura da ita balle ta bata kunya. Kaka da ta dawo daga rakiya tace da Fillo. "ke dai ki sauya hali dan gidan wani za ki je, kuma wannan halin naki dai ba halin zama uwa ta gari ba ne". Maijidda ta shigo, tayi wajenta tana yi mata dariya tare da tsokanarta akan kukan allura. Bata kulata ba tayi mata shiru, ita kuma ta miƙa mata ƴar ƙaramar waya ƙirar nokia irin ta da can wadda aka fara sakawa sunan rakani kashi, wayar duk ta jeme tasha kyauraye, banda Yami babu ma me iya riƙe wayar. "Amir ne ya kira yace na kawo miki. Wai ya kira ta Kaka a kashe". Kaka tace,"ai ita ta tsinka cajar garin shirmen banzanta". Fillo ta kalli wayar da ke kan cinyarta, sannan ta kalli Maijidda da jajayen idanuwanta da suka sha kuka suka ƙanƙance tace,"kin ɗauke min ita a jikina ko sai na ƙarasa kasheta". Sanin cewar zata aikata Maijidda tayi saurin ɗaukewa tana faɗin,"yanda Yami ke ji da wayar nan kika fasa aini za ki jawa faɗa". [8/8, 19:09] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *HalimaAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* *7* Acikin ɗan ƙaramin falon nasu, Fillo ce zaune ta takure daga jikin bango, jikinta gaba ɗaya a nannaɗe da babban mayafin da suke rufa da shi saboda sanyin da ta ke ji, kallo ɗaya za kai mata ta baka mugu mugun tausayi saboda yanda ta rame duk da cewar ita ɗin dama asali ba mai ƙiba ba bace, amma kana kallon ramarta a yanzu zaka san ta lalura ce. Fillo cikin tuƙewar wani kukan ta kifa kanta saman gwiwoyin ƙafarta, kukan da ya kusa yin rugu-rugu da zuciyar Amir da ke zaune yana fuskantarta daga ɗan nesa da ita, yana jin zuciyarsa na matsewa da wani irin zafi. Ya ɗauke ƙwayar idonsa daga kanta ya mayar kan magungunan da ya ɓallo a hannunsa, sai kawai ya janyo ledar magungunan kusa da shi ya zuba su a ciki ya ɗaure. Ya sauke numfashi very calmly yace da ita. "ba saboda na takura miki ba, saboda lafiyanki Halima...but kiyi shiru ki bar kukan na zubar kin fasa sha". zatonsa furucinsa zai yi tasirin da zai tsayar da kukan nata, amma sai yaji taci gaba da abunta kamar ba da ita yay maganar ba. Sai ya duƙar da kansa a cikin damuwar da shi kaɗai yasan me yake ji, Allah ma ya sani, da ace yana da iko da har abada Halimatunsa ba zata yi ciwo ba, haka kuma da ace da yanda zai yi ciwon nan ya bar kanta ya dawo kansa tabbas da yayi hakan ko da hakan zai zama ajalinsa, shi dai kawai ya ganta cikin ƙoshin lafiya da walwala. ya ƙara ɗago kansa ya kai kallonsa gareta, ganin har yanzu kamar ba zata daina ba yace da ita,"Halima kin san kuwa irin zafin da nake ji a zuciyata?, ki yiwa girman Allah ki daina wannan kukan wallahi ko kaɗan bana sonsa, yana taɓa zuciyata...indai magani ne nace ba za ki sha ina ce shikenan ko?". Fillo ta ɗago da kanta, idon nan ya ƙara yin loko yayi jawur, jijiyoyin kanta sun fito raɗau kamar idan kasa hannu zaka kamosu waje. Amir ya tsareta da idanu ita kuma tana saka hannu ta goge hawayen, amma da ike ita ɗin me ruwan hawaye ce tana gogewa wani na kuma sakkowa. Ita ɗaya tasan irin azabar da ta ke ji a gaba ɗaya jikinta, ita ɗaya tasan me ta ke gani a cikin barcinta tun daga waccan ranar zuwa yau. cikin muryarta da ta disashe da kuka tace,"ni nace maka waɗannan magungunan naku babu abunda za su yi min. ka daina asarar kuɗinka Amir, kawai a kira Malami yayi min adu'a". Amir dai dubanta yake da mamaki, ita ba aljanu ba amma kusan sati biyu kenan da ta ke ciwon nan ta kafe akan ita dai a kira Malami yay mata karatu, ba maganin asibiti bane maganin ciwon da ke damunta. kuma anyi anyi ta faɗa me ta ke ji tace ita babu komai zazzaɓi ne kawai. Asibiti kuma a duka test ɗin da suka mata sun ce ma babu maleria. Cikin kwantar da murya yace,"insha'Allahu kin daina shan maganin, amma ki bar kukan gaba ɗaya hakan kawai zai sa na kira Malam yay miki adu'a". Ta ɗan kafe shi da ido tana tunani cikin ranta, maganarsa da ta kutso cikin kanta ta katse abunda ta ke tunani. "amma tun da nima kusan Malamin ne nayi maki adu'an ko Halimatu nah?". Kai kawai ta gyaɗa masa, ta sani ɗin in har ba'a kira Amir Babban Malami ba to ba za'a kira shi ƙarami ba, Babansa Malami kai kafatanin gidansu ma, kwatancen gidansu ma idan za'ai gidan malamai ake cewa, kuma kusan shi ya gado mahaifinsa 100% cikin yara 28 da Allah ya ba shi. Ya taso ya matso kusa da ita, ya bar tazaran inches tsakaninsu. "me da me kike ji?". Ya tambayeta yana kai hannunsa ya taɓa goshinta. Sai ta rufe ido tana jan numfashi, so ta ke ta tambaye shi abin da Kaka taƙi amsa ma ta, ta tambaye shi makomar wanda ya ƙona asirin da ba nasa ba, kuma so ta ke ta yi musu bayanin ta ƙona asiri, ko ta samu ta waraka daga wannan masifar da ta jawa kanta. to amma ta ya?, ta ina zata fara?, da wanne irin bayani zata faɗa musu?, wacce fahimta zasu yi ma ta?, shin zama su yarda da ita ne?. Bama zata soma wannan katoɓarar ba, saboda idan Kaka ta fahimceta ba lallai Amir ya fahimta ba, kuma wataƙila idan wani yaji ta ɗaure kanta akan cewar ita ke da niyyar masa asirin. Ita dai ta sa ni ko meke damunta a halin da take ciki yanzu yana da nasaba da ƙona asirin da tayi, ba zata iya tantance irin mummunar halittar da ta ke gani cikin mafarkinta ba, ita tayi hakan bisa tausayi da kuma son taimakawa wanda ake son cutarwa, to amma kuma shikenan daga taimako?. Sai kawai ta rumtse idonta sosai, tabbas ba Muhammad Turaki kaɗai ba da akayi asirin saboda shi, tun daga kan wanda tunanin yin asirin yazo kansa, da mai zuwa ya amso asirin, da masu zuwa suyi aikin asirin, duka sun shiga uku, rubuce yake a tafin hannunta sai taci uwar uban duk wanda yay sanadin shigarta wannan mawuyacin halin. "ya kike jin ciwon kan?". Amir ya tambaya with a look of concern and sympathy. Ta haɗiye abun da ba zata kira shi da yawu ba, sannan ta buɗe ido ta kalle shi. "ina jin kan kamar ba nawa ba, kamar ma ba na mutane ba". Ya sauke numfashi kamin yace,"sannu". ita kuma ta gyaɗa masa kai kawai. Nan Amir ya kama kan nata ya shiga karanto adu'oi yana tofa mata, tsawon mintuna yana yin hakan kamin ya tsaya. Sannan ya miƙe ya ɗauko ruwan faro da yake siyo mata yanzu ya buɗe sabo ya tofa adu'ao aciki ya bata tasha, kana ya rufe ya aje mata sauran a kusa da ita. Fillo ta rufe idonta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243