Chapter 179
Chapter 179
suka karɓa, Bello kawai yake jira ya zo ya tura masa, yanzu shikenan ta jiƙa masa aiki, kwana yayi yana typing bai ko runtsa ba, haka ya dinƙa aikin babu daɗi saboda ya baro laptop ɗinsa a office. ya cije leɓensa na ƙasa yasa ƙafa zai fyaɗeta ta kife a ƙasa sai kuma ya fasa, ya buga mata tsawa da cewa,"wuce ki ɗauko ki ban". tuntuni ta daina tsoronsa, sai dai ta rasa dalilin da yasa ta kasa daina jin tsoron tsawarsa ba, tana tafe yana bin ta a baya. ta durƙusa sai kyarmar jiki takeyi ta ɗauko wayar ta ba shi, yasa handky ya karɓa gudun kar glass ya soke shi, ta yi tsaye tana zumɓura baki, ta ƙara jin saukar tsawar muryarsa da cewa,"tattaro glass ɗin". zata wuce ɗauko tsintsiya ya fincikota. "hannu za ki saka". ta kallesa taga babu alamar imani tare da shi hakan ya sa ba shiri ta durƙusa ta shiga tattara kwalban, idonsa ƙyam akan hannunta da ke zubar da jini dan tun a ɗauko wayar kwalabar ta soketa. sai da ta gama tattarawa ya wurga ma ta ɗayan handky ɗin, ta ɗauka ta zuba glass ɗin a ciki ta miƙo masa, ya karɓa yana nunata da yatsa cikin kakkausar muryar da ke shaida kashedi me girma ya ce,"kar ki kuskura, kar kiyi saken da zan dawo cikin gidana na sameki, in har kuwa na dawo na tadda ke ki tabbatar da cewa alƙiyamarki ta tsaya, dan sai kin ƙwammace ba ki taɓa sanin zuri'ar Alƙali ba balle kuma ni, and ki san da cewa sai kin biya ni wayata". yana faɗar haka ya fice fuuu ya bar ɗakin, ta bi bayansa da kallo kafin ta kifa kai da gwiwa ta fashe da kuka sosai, babu abin da take ji a zuciyarta sama da danasanin saninsa, sai da ta daɗe a haka sannan ta miƙe tunawa da kashedin da yayi mata, ta ɗauki jakarta ta fita daga ɗakin tana jin zuciyarta kamar zata buga, jiri ne ma yake neman zubar da ita dan da ƙyar idanuwanta suke kallon gabanta, tana sakkowa da ga benen ta faɗi kanta ya ƙumu da ƙarfen benen, cikin ƙarfin hali ta tashi tana daddafa bango ta iso har ƙofa ta buɗe. daidai da zuge glass ɗin ƙofar da Hajiya Madina tayi, karaf idonta ya fara sauka akan hannun Fillo da ke zubar da jini, ta zaro ido waje tana ambaton,"subhanallahi". sai kuma ta kalli Fillon taga tana hawaye ga shi kamar ba ta cikin hayyacinta, tai saurin kamota ganin tana neman faɗuwa. "Daughter lafiya?, wannan jinin fa da ga ina?" Fillo ba ta iya ba ta amsa ba, haka ba ta iya kallonta ba, Hajiya Madina ta riƙeta suka yo waje tana cewa da Nihal,"ko ma ki tayar da mota". sannan ta ƙara cewa da Fillo,"ina me babban sunan?". sai a sannan ta iya buɗe baki tace,"ya fita". san da motar Maama ta fita da ga gidan Baba me gadi ya girgiza kansa cike da tausayin Fillo, yarinya ƙarama ana neman a ɗora ma ta hawan jini, tun ranar da aka kawota ya fuskanci ba auren soyayya akayi ba, dan shi dai bai taɓa ganin Turakin ya shiga part ɗin ba sai ɗazu da ya fito a fusace kamar macijin da aka dannewa kai. direct asibiti mafi kusa suka wuce, tun tahowarsu Maama da Nihal ke jera ma ta sannu, su na zuwa cikin gaggawa Dr yay ma ta treatment ɗin wajen, ya cicciro pieces na glass yafi biyar a tafin hannunta, aikuwa tasha azaba dan jini kamar ana tatsarsa hannun duk ya caɓe, akai ma ta allurai, Nihal taje pharmacy ta karɓo maganunguna, lokacin da ta dawo an naɗe hannun Fillon da uban bandage. daga fitowarsu zuwa yanzu kuwa Maama ta kira wayar Turaki yafi sau bakwai duk ba ta shiga, kuma duka lines ɗin nasa, hankalinta duk a tashe yake da ciwon Fillon, ta kira wayar Mum ta tambaya ko Turaki ya zo gida ta ce ma ta a'a, Bello ma yace ba sa tare. kan hanyarsu ta dawowa Maama ta matsa mata da tambaya akan yacca akayi taji ciwon, ta kasa haɗa ƙaryar da zata faɗawa Maama ɗin, tai shiru ita dai sai rera kuka takeyi a hankali, har sai da taji ɓacin rai a muryar Maama tukunna ta ce,"wayarsa na fasa masa ban sani ba". Maama na kallonta ido buɗe ta ce,"fasa waya kuma sai kiji ciwo haka?". tayi shiru tana daɗa yin ƙasa da kanta, Maama ta dinƙa kallonta tana so ta nazarci yanayinta, uwar ramar kaɗai da yarinyar tayi ya isa ya shaida maka hankalinta ba'a kwance yake ba sam, dole akwai wata matsalar a ƙasa, dole da akwai abin da yake faruwa wanda basu san da shi ba, tun da me gadi yace ma ta Turaki ya fita babu jimawa ta san akwai matsalar da ke faruwa musamman da taga Fillo a wannan yanayin, babu tantama saɓani suka samu duba da yanda duk Fillon take a tsorace. _me ce matsalar?._ tambayar da ta yiwa kanta kenan, sai dai babu amsarta. hakan ya sa ta kamo hannun Fillo tana kallonta ta ce,"ɗago ki kalle ni a matsayin Umminki wacce ba za ki taɓa iya ɓoyewa damuwarki ba". idanuwanta suka kawo sabon ruwa sanda ƙwayar idonta ke shiga cikin ta Maaman, tausayin Maaman shi ya fara kamata ganin duk ta damu, kafin girma da kwarjinin Maaman su mamayeta gaba ɗaya, ba zata iya yi ma ta ƙarya ba sam saboda ta kare kanta ko kuma ta kare shi, ta sauke kanta ƙasa muryarya a hankali ta ce,"da wayar ta fashe ne shi ne ransa ya ɓaci yace sai na kwashe glass ɗin da hannuna". da tsananin mamaki Maama ta ce,"me babban sunan da kansa?, ya ce ki kwashe glass da hannunki?, cikin hankalinsa yake kuwa?". wannan furucin kaɗai ya shaidawa Fillo ran Maama ya ɓaci sosai. Maaman tai shiru ba ta ƙara magana ba sai faman jijjiga kai da takeyi, idanunta na kan waya tana ƙara trying lamar Turaki, cikin sa'a kuwa yanzu ta shiga sai dai har ta gama ringing bai ɗaga ba, ta ƙara kira nan ma bai ɗaga ba, sai da ta kira har sau uku sannan ta haƙura ta jefa wayar a jaka, cikin zuciyarta sai jinjina abin da Turaki ya aikata takeyi, ko da yake da ma ba'a sanin wani mugun halin namijin sai bayan ya yi aure. Fillo dai idonta na kan hanya, tunaninta ɗaya ta yanda zata faɗawa Hajiya Madina a sauketa a hanya, ta ga motar ta tsaya bakin wani islamic chemist, Maama ta buɗe ta fita ba tare da tace da su komai ba, ta bi ta da kallo ta glass har ta shiga kantin. a lokacin ta buɗi baki ta cewa da Nihal,"Adda don Allah ina ne hanyar tashar barin gari?". Nihal ta waigo tana kallonta ta ce,"me za kiyi acan?". tai shiru ba ta ce komai ba, lokacin Maama ta buɗe motar ta shigo, sanda ta rufo ƙofa Nihal ta ce ma ta,"Maama wai tambayar tashar da za'a bar gari take yi". Maama ta waiga taita kallon Fillo, wacce idonta ke kan hannun ciwon nata, tana nufin gidan su zata tafi kenan?, ta san ba komai bane ke damunta fa ce yarinta, bata
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243