Chapter 119
Chapter 119
ta ƙara ce mata,"dan Allah karki cutar da ni kema". Fillo tai murmushin ƙarfin hali, taji tausayin kanta na bin iska yana tafiya, yayinda na matar ke biyo iska na lulluɓeta. tace,"ba zan cutar da ke ba Mum, adu'a nake so kiyi mu fita daga wurin nan lafiya". Hajiya Ramla ta dinƙa kallon Fillo tana jin kamar wani ya taɓa kiranta da wannan sunan Mum. Fillo tasa hannu a rigarta ta ɗauko wayar ɗazu, ta kunna sannan ta kalli Hajiya Ramla tace,"Mum za ki iya faɗin lambar Baffa ko ta Maama? sai mu kira su azo a tafi damu". Mum tace,"su waye hakan?". Fillo ta ɗago ido ta kalleta sannan tace,"lambar mijinki Alƙali Dikko ko ta abokiyar zamanki Hajiya Madina". Mum ta girgiza kanta tace,"ni ban san su ba ai, ban taɓa jin sunansu ba". sai kuma ta haɗe hannayenta tace,"idan kin san sune mutanen da suka saka ni a ɗakin duhu don Allah karki kira su, sun ce zasu yi tsafi da ni ne, kuma babu abinda nayi musu". Fillo tasa hannu ta goge hawayenta, babu makawa ƙwaƙwalwarta tayi formating abubuwa da yawa, kuma ba lallai ta tuna komai ba ayanzu ƙila sai ta gani da idonta. a lokacin suka ƙara jin harbin bindiga, cikin azama Fillo ta miƙe ta kamo hannunta a rikice tana cewa,"Mum zo mu gudu kar su kama mu". Hajiya Ramla ta miƙe da ƙyar suka nausa inda basu san ina zasu ɓulle ba suna ta zabga gudu, da sun gaji sai su tsaya su huta, sannan suci gaba da gudun, gaba ɗayansu a galabaice suke. *A dai-dai wannan lokacin.* Fulani Azima zaune a gaban boka dunƙus, idanuwanta na manne acikin ruwan ƙwaryar dake gabansa yana mata bayani, tana jin zuciyarta na tafarfasa saboda baƙin ciki. "to ban san dai abinda hakan ke nufi ba, amma kwata-kwata ko aljani ɗaya ya kasa nuna mana fuskar yarinyar, amma tabbas dai aljanu sun shaida ita ke lalata miki aiki". maganar ta ƙara ƙona ran Fulani Azima, ta ɗaga murya tana saka hannu ta toshe kunnenta tace,"wacece wannan?, wacece ita da har aljanu suka kasa gano min fuskarta?". sai kuma tayi ƙasa da murya tana kallon Boka tace,"ni dai na roƙe ka da Aljani Jambus ka nuna min fuskar yarinyar nan ko kuma sunanta, nayi maka alƙawarin ko menene zan bayar ko da kuwa kaina ne". Boka yay dariya yace,"haba Azima, yanda muke da ke ai kin fi ƙarfin haka a wajena. abinda nake so ki fahimta shine yarinyar nan tafi ƙarfinmu saboda tana tare da tsari a jikinta". sai yasa wani mifici ya rufe ƙwaryar sannan ya buɗe yace,"leƙo ki gani". ta leƙa kanta ta hango wata mace a tsaye doguwa siririya, amma baka ganin komai nata sai ɗan banzan duhu. yace,"to kinga ni babu ta yanda zamu ga fuskarta haka kuma sunanta ɓacewa yake akan aljanunmu". fuskar Fulani Azima na shaida mamaki matuƙa tace,"to saboda me boka?". sai yasa hannunsa acikin ruwan ya zuƙo hoton, daidai inda hannun Fillo yake yace,"ba lallai ke ki gani ba amma ni ina iya gani, wannan azurfar ta yatsanta azurfa ce ta tsari wadda ba zata taɓa barin wani aljani ya ganta ba balle har ya sami damar shigarta, bayan haka kuma ɗan autan aljanu ya faɗa min cewa yarinyar na kasancewa kullum cikin yin adu'oin tsari, bata minti ɗaya bata ambaci sunan Allah ba haka kuma bata min ɗaya bata ambaci adu'ar neman tsari ba. saboda haka babu yanda zamu yi da ita gaskiya, kuma shugaban Aljanu ya shaida mana muddin yarinyar na tare da Turaki babu abinda asirinmu ya isa yayi masa, domin ita ɗin kamar sila ce ta kariya a tare da shi". kan Fulani Azima yay matuƙar ɗaurewa, ta dinƙa hasaso tsayin yarinyar tana so ta kwatanta shi da na Ilham amma sam babu haɗi, tsayin Ilham bai ko kusan nata ba. to wacece wannan ɗin?, tabbas ya zamar mata dole taje gidan Alƙali Dikko da ƙafafunta, idan aljanu sun kasa ita ba zata gaza ba domin ba ta taɓa barin wani ya shiga gaban al'amarinta, dole sai taga bayansa ko waye. ta numfasa tace,"shikenan me girma boka, yanzu ya batun mu na janyo hankalin Alƙali Dikko kaina?". Bokan ya bushe da dariya yace,"kin haƙura kenan, ai nayi zaton har yanzu kina kan bakanki na cewar son gaskiya kike so Dikko yayi miki ba sai anyi amfani da asiri ba gudun lalacewa wataran". tayi shiru kamar ba zata ce komai ba sai tace,"mu bar tuna baya. yanzu dai a san abinyi akan Mai martaba, a kashe shi kawai na huta da aurensa da ke kaina. shi kuma Alƙali ayi aikin da za'a gama da rayuwarsa kawai, ina nufin ya saki kowa ya kamani ni ɗaya hatta kuwa da mahaifiyarsa. tashin farko abinda nake so shine Alƙali ya fita daga hayyacinsa yaywa Madina saki uku sannan duk ya kori ƴaƴansa, daga baya kuma sai ya dawo kaina ya mallaken ta yanda zamu yi rayuwa da shi har a bada. da wannan buƙatar ta biya sai a raba auren Ilham da Turaki, kuma ta yanda nake so mutuwar auren ta kasance Dikko yaje gidan da kansa ya umarci Turaki da ya saki Ilham". Boka ya bushe da wata mahaukaciyar dariya yana ɗaga hannu sama yace,"buƙata taki ta biya Azima, duk yanda kika nema haka za'ai, kuma komai da kika nema zai faru tabbas, angama da wannan buƙata taki ki jira kwanaki biyu kacal". Fulani Azima ta saki wani murmushi na jin daɗi da kuma nasara, sannan ta miƙawa Jakadiya hannu. cikin rawar jiki Jakadiya tasa hannu cikin jaka ta ɗauko yari da sarƙa da zobe ta saka a tafin hannun Fulani Azima. har yanzu murmushi bai ɗauke a fuskar Fulani Azima ba ta ajiye sarƙar a gefen boka tace,"wannan kyauta ce na baka. kuɗinta kimanin miliyan goma ne, kyauta ce kawai ba kuɗin aikinka ba". Boka na murmushi yace,"godiya nake". tace,"sai muje ga lissafin abinda zan bayar akan aikin". ya ɗaga kansa sama yana kallon reshen bishiyoyi na tsawon daƙiƙa kafin ya sauke yace,"da farko za ki bayar da miliyan goma, sannan za ki kawowa jikokin Aljanu baƙin jaki guda biyar, sannan za ki haƙa kabari ki yanko mana zuciyar jariri fari wanda ana haihuwarsa ya mutu, sannan kuma muna buƙatar yatsa ɗaya na ita mahaifiyar Dikko". rufe bakinsa kenan sai suka ga jan ƙyalle ya faɗo gabansu ɗaure da wani dunƙulen abu. da tsananin mamaki yake kallon abin na tsawon daƙiƙa biyu kafin ya kai hannu ya ɗauko ƙyallen, ya ɗauko shi zaren da aka ƙulle shi na warwarewa. mamakin dake tare da shi bai gama sakinsa ba yaga baƙar kurciya ta faɗo kan hannunsa a ma ce, sabon mamaki tsantsa ya kama shi. ya ɗau kurciyar ya haɗe da wannan ƙyallan sannan ya juyo yana kallon Fulani Azima wadda idanuwanta ke a warwaje tana binsa da kallo. taji yace,"ya akai haka?". tace,"me ya faru?". yace,"me na faɗa miki shekaru ashirin da biyar da suka wuce kafin nayi miki aikin Ramla?". cikin saurin baki da rawar murya tace,"kace kar na kuskura inyi sakacin da asirin nan zai karye, domin duk ranar da ya karye ba zanji da daɗi ba". tana yin shiru yay wani guntun murmushi na tayata jimami sannan yace,"ban labarin yanda aka yi bayan barinta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243