Chapter 68
Chapter 68
ta kalli Nihal, sannan ta kai idonta ga Zaytuna wacce tayi tsaye ƙeƙam. sai kuma ta dawo da idonta ta sauke akan wayar tana kallon call ɗin dake tafiya, Hammah aka ce mata alhalin ga ƙannensa anan tare da ita. cikin neman fitar hayyaci tace,"to wace me magana a wayar?, wai Hammanku ya suma, to aina?, garin ya?". ta wurga tambayoyin ga Samha. duk su ukun suka maimaita,"Hammah ya suma?". Hajiya Madina ta ɗaga musu kai kawai hawaye na sintiri a saman fuskarta. "hello, dan Allah wake magana, ina me wayar yake dan Allah?". Nihal ta faɗa acikin wayar bayan ta amshi wayar daga hannun Samha. babu amsa sai kuka dake tashi kawai, Zaytuna ta silale a wajen, Nihal tayi kanta da sauri. Samha ta ɗau wayar ta kai kunne, dan tuni Hajiya Madina tayi mutuwar zaune, ta koma kamar me paralize idonta a wuri ɗaya kawai yake, jinta take kamar rayuwarta ta ƙare, kamar shikenan ta gama aiki. daga ɓangaren Fillo tace,"Hammah ne ya suma". Samha ta waiga taga sauran sisters ɗinta suna nan, ɗaya ta suma ɗaya na ƙoƙarin ganin ta sumen ta farfaɗo. to wace ke faɗin Hammah ya suma?. sai ta dakewa faɗuwar gaban da take ji tace,"to waye yake magana, kuma wanne Hammah ɗin?". Fillo na ƙara jijjiga Turaki tace,"ni ce Fillo, Hammah Turaki ne ya suma Maama, tun ɗazu yaƙi yay motsi kamar ya mutu". a matuƙar razane Samha ta miƙe tsaye tana faɗin,"what! mutuwa?, dan uwarki ke kina ina?, ta ya kika san abinda ya faru da Hamman'mu?". jin furucin Samha yasa jikin Fillo yin rawa a lokacin zuciyarta na faɗa mata shikenan tata kuma ta ƙare, ita dama ta sani ita za'a ɗorawa alhakin faruwar komai. "Fillo aina?, aina ya suma?". Hajiya Madina da ta amsa wayar take tambaya kuka na ƙwace mata. "Maama ɓangaren su Adda Zay...". bata ƙarasa ba taji alamun faɗuwar waya a ƙasa. kuma zata iya cewa rabin second ne ya kawosu, dan ganin su kawai tayi tsaye akanta. Hajiya Madina ta fizgo Fillo ta miƙe tsaye, ta zabga mata mari a fuska, marin da yasa jinta da ganinta suka ɗauke na wucin gadi. kamin ta dawo dai-dai ta ƙara ɗauketa da wasu marikan har uku. "uban wa ya buɗe room ɗin nan?". babu abinda Fillo ke ji a lokacin balle ta iya bada amsa. "ba magana nake miki ba, ban yi muku iyaka da wannan room ɗin ba?, bance duk sanda zaku yi aiki babu ruwanku da taɓa wannan ɗakin ba?, wa ya baki key ɗinsa?, me yasa baki hanasa shigowa ba?, kin buɗe baki kin yi min magana ko sai nasa ƴan sanda sun kamaki kin ƙare rayuwarki a bayan kanta?". Fillo na kuka tace,"wallahi Maama bani na buɗe ba, nazo wucewa ne...". bata barta ta ƙarasa maganar ba tasa bayan hannunta ta kifar da ita a ƙasa, Fillo ta zube a ƙasan tiles kanta na dukan bango, lokaci ɗaya taga giftawar wasu taurari acikin idanuwanta. abunda kawai zata ce ta ƙara ji shine Hajiya Madina ta mata gargaɗin cewa,"duk abunda ya sami ɗana, duk abunda ya sami lafiyar ɗana sai naga bayanki Fillo, tabbas sai kin ƙwammace ina ma baki zo duniyar nan ba". daga nan bata ƙara jin komai ba kamar yanda bata ƙara ganin komai ba na tsawon wucewar minti goma sha biyar. kuma sanda ta dawo hayyacinta daga buguwar kan da tayi, sai taga babu kowa a ɗakin sai ita ɗaya. tsawon minti biyar tana kuka, a hankali ta dinƙa kewaye ɗakin da kallo, babu komai acikinsa face shirgin takardu dake cikin locker, sai kuma gadon jarirai irin wanda ta taɓa gani a ɗakin Fulani, sanda Kaka ta zauna yiwa Gimbiya Zahra wankan jego. wanne abu ne acikin ɗakin da ya haddasa shigar Turaki situation ɗin da ta zo ta same shi aciki?, ina abunda yasa ba'a so a buɗe ɗakin?. ta kalli komai kuma bata ga komai ɗin da zai zama dalili ba. taimakonsa tayi, kuma taimakon take da niyyar yi masa, amma ga da abinda aka saka mata da shi, ya za'ai ta manta?, waye zai taushi zuciyarta akan abinda ta ƙudurce na ramuwa?, Amir ne kawai, kuma yanzu babu Amir a cikin rayuwarta, tsawon watanni huɗu sai taji tana kewar Amir a yau. sai ta runtse ido tana jin zafi a zuciyarta, ta miƙe tsaye da ƙyar tana dafa bango saboda hajijiyar da take ji, ko'ina na ɗakin take bi da kallo, so take taga illarsa, ba zata taɓa barin ɗakin nan ba sai taga illarsa da kuma dalili, wannan dalilin da ya haifar da komai. ta miƙe da ƙyar ta tafi tana jan ƙafarta dake yi mata zugi har ta ƙarasa gaban enlargement. kallon matar take yi da kyau cike da nazari da son gano wani abu amma ta kasa, abu ɗaya ta fahimta matar nan na da alaƙa me ƙarfi da Turaki, saboda tsananin kama, kamannin da suka zama kamar an tsaga kara, sai dai irin alaƙar da take tunani zuciyarta na faɗa mata cewa ba ita bace, wannan matar bata yi kama da wacce ta ajiye ɗa kamar Turaki ba, shekarunta kaɗanne, kuma ko da auren ƙauye aka mata baici ace ta haifi ɗa kamarsa ba balle har ta haife shi, ta haifi Zaytuna. ba ma wannan ba, idan ma tayi tunanin ita mahaifiyarsu ce to Hajiya Madina fa?. ta dafe kanta da take jin kamar zai fashe tana saurin dafa gadon jariran, bata buɗe idonta ba har sai da ta daina jin juwar, idonta ya sauka acikin gadon jariran, kan award frame dake kan bargon jariri, tasa hannu ta ɗauko tana kallon award frame ɗin, tayi concentrating akan hoton jiki da sunan jiki. *her Excellency RAMLA MUHAMMAD TURAKI*, sunan da yake rubuce a jiki kenan. wai wace wannan matar?, mene alaƙarta kuma da sunan Turaki?, *MATARSA!*, haka zuciyarta ta faɗa mata, kuma tabbas hakan yake, amma ina take?, mutuwa tayi?, rabuwa suka yi?, take anan zuciyarta ta warware mata dalilin da yasa ba'a son buɗe ɗakin, da kuma dalilin da yasa Turaki shiga critical condition. saboda wannan ɗakin na da alaƙa da ita shiyasa ba'a so a buɗesa, sannan ganin hotonta na fama ciwon da ta jiwa Turaki a zuciyarsa, wannan ciwon da tabonsa ya kasa goguwa daga garesa. wanne irin ciwo ne?, me tayi masa wanda ya kasa mantawa?. ta ƙara ƙulle idonta for 1minutes sannan ta buɗe tana ƙarewa gadon jariran kallon, ta tabbata wannan room ɗin shine silar komai, kamar yanda gadon jariran nan ke da alaƙar komai, kenan idan tunaninta ya bata dai-dai *ƊA* ne silar komai, jaririnsu!, to ina jaririn?, kuma itama uwar tana ina?, ta mutu ne?, ita ɗan da suka mutu?, kenan wannan shine ciwon dake manne a zuciyar Turaki?. sai kawai Fillo ta sauke numfashi tana hurar da iska a bakinta, ta koma ta isa gaban englargement din ta cirosa, sannan ta dawo ta ɗauko award frame ɗin ta fice da su daga ɗakin. *6hours pass, Miyyetti Hospital, Room 05.* cikin vip room ɗin, Turaki ne jingine a jikin pillow ɗin da aka saka masa a bayansa, goshinsa ɗaure da bandage, an naɗe wurin da ya ji ciwo da shi sanda yake dukan kansa ajikin glass. gefensa kuma wata farar tsohuwa ce kamar balarabiya a kan kujera,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243