Chapter 240
Chapter 240
ɗanta da ya zama kamar abokinsa, kasancewarsa irin yaran nanne masu saurin sabo. Maijidda tace,"wallahi kaga wata tahfeez aka buɗe a bayan layin nan, shine aka kaisu can". "har friday suke zuwa kenan?". Turaki ya tambaya. tace,"ehh juma'a zuwa lahadi, tun safe sai yamma". "masha'Allahu, Allah ya bada ilimi me albarka". ta amsa da,"amin amin". "to bari mu wuce, a gaida min da abokina". tayi ƴar dariya tana faɗin,"Musaddiq sarkin magana, zai ji insha'Allahu, da sun samu hutu ai zan kawo muku su, sai su yini". sai ta saka hannu tana share ƙwallar fuskarta tace,"Allah ya jiƙan Fillo". Turaki da Ƴaƴansa jiki a sanyaye suka amsa da,"amin ya Rahman". tukunna suka yi mata sallama suka wuce, inda suka ɗauki hanyar gidan Me Martaba domin zuwa duba Fulani Azima, wacca har yanzu ta nan kwance rai a hannun Allah, gaba ɗaya halittarta ta sauya ta koma tamkar ta ƙadangare, sai ka rantse da Allah ba mutum ba ce tun asali, wasu gashi sun tsatstsafo mata a jiki, idanunta sun yo waje ƙwayar kamar zata faɗo ƙasa, bakin da hancin sun shafe a waje ɗaya, kai abun dai babu kyan gani da kwatance. ga duk wanda ya ganta sai ya tausaya mata ya zubar mata da hawaye idan bai san abun da ta shuka ba, wanda kuwa yasan me ta aikata muddin ya ganta sai jikinsa ya mutu gaba ɗaga, tsoron Allah ya ƙara shigarka, kaji gaba ɗaya duniyar ta fita a ranka, balle kuma kaji kana son sha'awa ko mallakar abun da ke cikinta. Maama da ke kallon bakin titi tace da Turaki,"Abie don Allah zan bayar da sadaƙa". Turaki yay parking a gefen hanya, ya zaro ɗari biyar a aljihunsa ya miƙa mata ta karɓa sannan ta buɗe mota ta fita. "na gode Abie". ƴar tafiya kaɗan tayi daga inda motar tasu ta tsaya, ta tsuguna agaban almajirin ta saka masa kuɗin acikin robarsa tare da faɗin,"Baba kayi adu'a Allah ya kai ladan ƙabarin mahaifiyata". tsohon ya shiga kwaranyo mata adu'a iya adu'a, daga mahaifiyartata har ita kanta da sauran ahalinta. ta ɗaga glass ɗinta tasa tissue ta goge hawayen da ya cika mata ido, kafin ta yunƙura ta miƙe jiki a sanyaye ta bar wajen nasa. tana cikin tafiya tayi karo da mutum, ba wai don bata ganin gabanta ba, sai don hankalinta da ya bar jikinta a lokacin. ta sunkuya ta lalubo gilashinta ta saka, sannan ta kalli mutumin da ta tsorata da ganin nasa, tayi saurin matsawa gefe tana ce masa,"kayi haƙuri don Allah". muryartata ƴar ƙarama kuma ƴar siririya me zaƙi ta fito ta shiga kunnen Amir ta ratsa jikinsa, ya kasa ƙifta idonsa akanta, kallon mamaki kawai yake yiwa yarinyar gabansa, wacca gaba ɗaya yasan bata kai shekara sha bakwai ba. abun da ya sani shi ne ya san wannan halittar, sai dai bai yi tsammanin zai sake ganinta a haka ba duba da tsawon shekarun da aka ɗauka, ya sani Fillo na da ƙaramin jikin da ba lallai shekarunta masu yawa su nuna a jikinta ba. to amma duk da haka abin da matuƙar mamaki ace ita ce a gabansa haka, babu wani alamar girma a tare da ita, after all shekaru goma sha bakwai ɗin da ya ɗauko bai ganta ba. jikin Maama na rawa ta daɗa ce masa,"zan wuce". Amir yay ajiyar zuciya bayan ƙare mata kallon tsab da yayi, tabbas wannan ba asalin Fillon da ya sani ba ce, wannan me kama da ita ce sak babu wani banbanci, sai dai in ace banbancin halayya, me hakan ke nufi kenan?, wata ce photocopy of her ko kuma ƴarta ce?. lokaci ɗaga matacciyar zuciyarsa da babu tsoron Allah acikinta taji ta kwaɗaitu da yarinyar, yaji sha'awarta ta ratsa duk wani ɓargo na jikinsa, take kuma ya fara tunanin ta yacca za'ai ya shiga rayuwarta a irin matsayin da ya saba shiga rayuwar sauran ƴan mata?, ya shiga rayuwarta kamar dai yanda ya shiga rayuwar me kama da ita. _(hmm Allah ya kyauta, ya kuma kiyashe mu daga sharrin zuciya, dama haka abun yake, ance wasu ko zasu je lahira su dawo halinsu ba zai taɓa canjawa ba, sai dai muyi adu'ar Allah ya tsare daga sharrin mugwayen mutane.)_ sai ya sauke idonsa akansa yana kallon jikinsa, wannan sam ba wancan Amir ɗin ba ne me ji da tashen ado da ƙwalisa a zamanin baya, wannan wani Amir ɗin ne na daban, wanda halittarsa ta sauya tun yana cikin prison, ya dafe ya zama mugun baƙi, yay wata muguwar rama kamar me cutar S, ya haɗa uwar ƙasumba a fuska kamar dodo, haka kansa ma ya tara uban gashi kamar mahaukaci, duk yayi duƙunduƙun kayan jikinsa duk a yayyage, ga uban ɗoyi da ke tashi a jikinsa kana ji kasan kwanan bola yake yi. warin jikin nasa ya doki hancin Maama, take ta duƙa a ƙasa saboda aman da ya taho mata, ta shiga kyalaya amai kamar hanjin cikinta zasu fito. Amir ya duƙa a gaban nata shi ma, zuciyarsa na harbawa kaɗan kaɗan, abu ɗaya yake tunani wanda yake jin har in ya rasa zai iya shiga wani hali, halin da yafi wanda yake ciki muni, muddin bai samu ya kusantu da yarinyar ba zai iya rasa lafiyar jikinsa. don haka zuciyarsa na ingiza shi ya kai hannu zai taɓa Maama tayi saurin miƙewa tana ja da baya. "mene haka?, na fa baka haƙuri". ya miƙe yana lashe leɓe, a hankali yace,"Ki tsaya na taɓa jikinki don Allah ko ya ya ne, idan na taɓa zan haƙura na barki ki tafi". Maama ta shiga girgiza masa kai tana ja da baya, yanzu kam ya gama tabbatarwa ba Fillon da ya sani bace, kuma ko da ace ita ɗin ce ma ba zata taɓa gane shi ba, don kwatakwata ya fita a Amir ɗin da mutane suka sansa, shiyasa har yanzu ma Ƴan sanda suka kasa kama shi bayan wani laifin da ya ƙara aikatawa lokacin da ya fito a prison. "sau ɗaya yarinya, sau ɗaya kawai za ki barni in taɓa ƙirjinki, ki tausaya min wallahi a bola nake kwana". yayi maganar da kana ji kasan ƙwaƙwalwarsa ta fara taɓuwa, lokaci kaɗan ya rage ya fara hauka tuburan. san da Maama ta kai ƙarshe ajikin wani ƙarfe, lokacin Ayan da Turaki suka iso waje, tana ganinsu ta ƙwala kiran Abie, Ayan yasa hannu ya juyo da Amir, da yake irin tsayin mahaifinsa yayo sai ya zamana tsayinsa yay daidai da na Amir ɗin. cikin zafin nama Ayan yasa hannu ya wanke fuskar Amir da zazzafan mari, ya damƙi ƙwalarsa yana jijjiga shi har sai da ya kai Amir jikin ƙarfen da ke bayansu ya buga kansa a jiki. "kai ba mahaukaci ba ne zuciyata ta faɗa min hakan, ubangiji yayi min baiwar gane mutane a kowanne hali suke ciki. sai na kasheka tun da ka yi yunƙurin taɓa min ƙanwata". ya faɗa yana ta buga kan Amir ajikin ƙarfen, Turaki kuwa na gefe rungume da ƴarsa a jiki zuciyarsa sai zafi take yi masa, idan har yace zai kai hannu ya taɓa Amir to bai san me zai ya faruwa ba, don wataƙila kafin ƴan sanda su iso wajen ya kashe shi. ɓangaren Amir kuwa abu guda ɗaya ya sani, ba zai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243