Chapter 61
Chapter 61
aka cire nasa kenan, dama leda 1 da rabi ake buƙata, Dr Yusuf ya bada rabin. Turaki ya numfasa yay tattaki ya ƙarasa gaban Fillo dake tsaye har yanzu bata buɗe idonta ba, wataƙila tana jira ne taji ya fita daga kitchen ɗin sannan sai ta buɗe idon, ko kuma tana jira ne ya bata umarnin buɗewar, tunda ita bata da umarnin kanta sai na wani, ya lura da hakan tun farkon zuwanta. sai dai yana zuwa dab da ita taji gabanta yay mugun faɗuwa, allon ƙirjinta ya girgiza, taji kamar ta arta a guje. so take tasa hannu ta toshe hancinta saboda ƙamshin turarensa da ke shiga hancinta, ba saboda rashin daɗinsa ba, idan tace ƙamshinsa babu daɗi tayi ƙarya, wannan ƙamshin yana ɗaya daga cikin ƙamshin da zata iya cewa da wuya a samu ƙamshi me daɗi irinsa. sai dai da ace tana da iko, da ace tana da iko da Turaki da ta haramta masa sanya wannan turaren, da tasa ya bar ƙasar nan yaje wata ƙasar sun wanke duk wani sauran ƙamshi na irin turaren nan dake jikinsa, ba ta son ƙamshin ta tsane shi, ba don komai ba sai don an haɗa asiri da shi, wannan asirin da yay sanadin zuwanta cikin dajin da ta kusa mutuwa. ranar da Turaki ya tsareta da tambayar me ya kaita wancan wurin yana kama hannunta taji ƙamshin, ƙamshi ne da ba zata manta da shi ba, ta jima tana zuƙar ƙamshin a lokacin dan tabbatar daga inda yake fitowa, tunaninta ko asirinne ya kuma biyota, da ga baya ta ankara da cewa ba ƙamshin kowa ba ne sai nasa, that means ya tabbata kenan asirin nan nasan ne, kuma an haɗa asirin ne da turaren da yake sawa...saboda haka yanzu fatanta guda ɗaya ne, Allah ya bata wata dama da zata hana Turaki saka wannan turaren, ko kuma Allah ya ɓatar da turaren daga duniya gaba ɗaya. jin takalmin Turaki gaba ɗaya akan kafaɗunta tai firgit ta buɗe ido ta sauke kallonta akan ƙafafunsa dake cikin takalmin shigowa kitchen. ta haɗiye wani busashshen yawu sannan ta iya buɗe baki tace,"kayi haƙuri ban san me kake cewa ba". ya fito da hannayensa daga aljihu ya tamke fuska yace,"na miki kama da dodo?". da sauri ta girgiza kanta alamar a'a. yace,"to me yasa duk ranar da kika ganni kike rikicewa ki bi ki firgice, ko ina kama da aljaninki?". nanma ta girgiza kai cikin sauri tace,"a'a". yace,"to ina jinki tsoron na mene?". a hankali tana shirin yin kuka tace,"bana so a ɗaga min murya ko kuma a min tsawa". yace,"ni kuma haka nake miki ko?". bata ce komai ba tayi shiru. sai taji yay ƙasa da muryarsa yace,"mene wancan abun da kike haɗawa?". ta ɗaga ido ta kalli robar da take dama kunun tace,"kunun shinkafa ne, Adda Samha tace na dama mata". ya matsa daga gabanta ya ƙarasa wurin yana faɗin,"an gama?". tace,"a'a zan zuba madara ne". yace,"zo ki ƙarasa". sai tai ɗan jim bata motsa ba, ya juyo ya wurga mata wani kallo da niyyar ya doka mata tsawa sai kuma ya taushi zuciyarsa ya sauke murya ƙasa yace,"nace kizo ki ƙarasa ko". ta taho kamar me ciwon ƙafa, ta fasa madarar ta ɗaga gwangwanin tana zubawa hannunta nata rawa, madarar rabi ce ta shiga rabi duk ta zube a ƙasa, haka har ta juye gwangwani ɗaya sannan ta ƙara fasa wani, zata zuba sai taji ya kama hannunta ya karɓi madarar ya zuba da kansa ya jujjuya. yana gama juyawa ya tura mata cup ɗin da ya ɗauko gabanta, bai magana ba amma ta fahimci me yake nufi. sai tace,"zan zuba siga". ta faɗa tana nufar drowern dake sama, ya bita da kallo yana tunanin ta inda wannan ƴar a bar dake iyakar cikinsa zata iya ɗauko abu a wancan drowern dake luluƙin sama. ya lissafa yaga ko da abu zata taka sai ta ɗora me tsayi tukunna tsayinta zai kai, lissafin nasa ya ƙare a kallon siraran ƙafafunta dake yawo a cikin zani, babu makawa ta taka wani abun ta faɗo sai ƙashinta yay breaking in to pieces. ta ɗauko doguwan kujera zata taka ta hau sai ganinsa tayi ya ɗauko roban ya miƙo mata, tana so ta kalle shi amma tana tsoron idonsa, tasa hannu biyu ta karɓa ya wuce ya bar mata wajen. zata zuba sugar ɗin taji yace,"a little bit". sai ta dakata da zubawan. yana ganin hakan sai yace,"ɗan kaɗan". kaɗan ɗin ta zuba, kuma data zuba sai data ɗago ta kalle shi, ba tai magana ba amma kallon nata ya bayyana masa abinda take nufi, itama kuma shirun nasa ta gane cewar yayi. ta zuba kunun a cup ɗin da ya ijje mata sannan ta ɗauko ƙaramin plate ta ɗora cup ɗin akai ta ɗora spoon, ta ɗauka zata fitar masa da shi taji yace,"give me". da sauri ta miƙa masa ya karɓa dan ta gane me yace, bata manta karatun ɗazu ba da teacher nasu ya faɗa musu ma'anar give me da hausa. yana karɓa ya fice ya bar kitchen ɗin, da fitarsa ta sauke wata wawiyar ajiyar zuciya, ta ɗauki tea flask ta juye kunun aciki ta ɗauka ta fita da shi, tana fatan Allah yasa Turaki baya falon a lokacin. samunsu tayi duk suna dining suna lunch, tace da Samha. "Adda Samha nan zan ajiye ko ɗakinki zan kai miki?". Samha bata kalleta ba tana wani shan ƙamshi tace,"ajiye anan". ta zagaya ta gefen da Nihal ke zaune ta aje, sannan tai tsaye ƙeƙam a wurin. tana jin idon Hajiya Madina akanta, duk sai take jin wani iri da kallon, ta ƙara yin ƙasa da kai. "Idan kin kawo abu kike tafiya bayan kin ajiye ba sai kin jira an miki izinin tafiya ba, kinji ko?". tace,"tom Maama". Hajiya Madina tace,"da sauran abincin a kitchen ko zaku ɗiba anan, ko kuma wani abun zaku dafa?". tace,"akwai saura Maama". tace mata,"to kije ku ci". har zata tafi Zaytuna ta kalli cup ɗin dake gaban Turaki, ya shanye rabin kunun ya bar saura. taga idan an barsa asararsa za'ai, kuma wannan na flask ɗin yanda suke da son kunun shinkafa ba zasu bar ko kaɗan ba, kuma tasan Fillon da ta haɗa bata rage ko kaɗan da zata sha ba, tasan abinda zata iya aikatawa. dan haka tace mata,"zo ki ɗauki wannan". Fillo ta zagayo gefen da take, ta ɗau cup ta riƙe. "ki shanye shi karki zubar". ta wuce ta koma kitchen ɗin, ta tarar Ɗausiyya ta zuba musu abincinsu a wani ƙaton roba, da dukkan alama Ɗausiyyan na da shegen ci, kuma bata saba cin abinci a ƙaramin kwano ba. ta ɗauki wani cup ɗin separately ta juye kunun da Turaki ya rage, bayan ta wanke cup ɗin ta maida shi ma'ajiyarsa tabi bayan Ɗausiyya suka fita. **** Boɗejo na zaune a tamfatsetsen falon na gidan Hakimi, wata maid nayi mata tausa. da sallama aka shigo falon, Boɗejo ta ɗauke kanta ga barin kallon tv ta koma kallon ƙofa. ganin masu shigowa ta buɗe baki cike da jin daɗi tace,"Ilham". ta faɗi sunan tana me cike da mamakin ganinta. Ilham da ƙawarta suka ƙaraso ciki, ita ta ƙarasa inda Boɗejo take ƙawartata kuma ta zauna akan kujera. "bari in
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243