Chapter 124
Chapter 124
cewa komai dan duk a ruɗe ta-ke. Daddy yace,"kiyi haƙuri Hajiya ki daina kukan kiyi mata adu'a, insha'Allahu matsalar ba babba bace". Inna Wuro ta ƙwanƙwasa glass tace da Daddy,"buɗen bus ina kwaso kayan jaririyar Yusuf da na yo mata tsarabarsu, da tsada na siyo dubu sha biyar duk guda ɗaya". Daddy yace,"kiyi haƙuri mu dawo tukunna kinga a condition ɗin da yarinyar nan ta-ke kar jininta ya ƙare". ta zabga salati tace,"Amadu yanzu har ƴar sarkin aljanu ta fini matsayi a wurinka, saboda kana tare da aljanu ba zaka iya jin maganata ba, to kaje ni dai ba abinda zance wallah sai dai Allah ya saka min". Daddy ya fito ya ɗauko jakar kayanta ya dire mata. ta kalli me gadi tace,"ɗaukar min muje, ni dai ba inda zan bisu, waye yake taimakar wasu aljanu, rabon ai su girgiza motar tasu akan titi ne suyi haɗari, in ko haka ta faru babu uban da zanyi jinya, suna gani aljanar da ta shiga jikin Yusuf akan son ɗaya daga cikinsu irin baƙar wuyar da suke ba shi. ɗazu ma ina bakin ka'aba har yana ce min wai in yi masa adu'a aga yarinyar nan da ta ɓata, kai baka ji ba kamar zai yi kuka da yana maganar, ni ko nace wallahi ba zan ba sai dai nayi adu'a Allah yasa su fita daga jikinka". Mum dai kuka kawai take yi har suka isa asibiti, suna isa Daddy ya kira Yusuf sai ga shi kuwa cikin hanzari ya ƙaraso, Allah yasa yana night duty, nan da nan aka shiga da Fillo Emergency room. *A dai-dai wannan lokacin.* Turaki na zaune acikin motar Dsp ya kifa kansa akan stearing, wayarsa dake aljihu ta shiga ringing cikin sauri yasa hannu ya ɗauko da dukkan fatansa daga gida ne za'a ce masa Fillo taje. sai dai ganin akasin lambar da yake tunani sai yaƙi ɗagawa ya aje lambar a gefe, kiran ya ƙara shigowa bayan katsewar na farko, cikin ransa yana tunanin me zai sa wannan me kiran ya kirawosa at this time. kamar ya sha re sai kuma ɗayan ɓarin zuciyarsa yace ya ɗaga, yana ɗagawa kuma daga ɓangaren Dr Yusuf yace da shi. "idan ba damuwa kuzo asibiti da gaggawa ga yarinyarku an kawo mana ita emergency, accident ɗin ma har yafi na da muni, jinin da ta ke buqata this time around yana da yawa, so please cikin gaggawa muna buƙatar kuzo". ai babu wani batun ƙarashen jin abinda Dr Yusuf ke faɗa ya wurgar da wayar akan kujerar me zaman banza, ya duba jikin motar yaga da key ajiki dan haka ƙofa kawai ya janyo ya rufe yaja motar a 360 yana jin kamar ya ɗauki motar ya dire a cikin asibitin. *Vote, share and comments.* [8/31, 00:51] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *36* Allah kaɗai ya kaisa lafiya zuwa Asibitin Miyetti saboda irin mahaukacin gudun da yake yi, yana isa asibitin direct office ɗin Dr Yusuf ya faɗa, yanda yake a matuƙar rikice haka shima Dr Yusuf ɗin yake. yana ta aikin sauke numfashin yake kallon Dr Yusuf idonsa tamkar zai faɗo yace,"tana ina Dr?, a wanne hali ta-ke ciki?". Dr Yusuf yaja dogon numfashi ya sauke, ya rufe idonsa for a while sannan ya buɗe ya sauke su akan Turaki yace,"an shiga da ita situation room, and she is in critical condition, wanda yake da kamar wuya...". "da kamar wuya me?". Turaki ya faɗa cikin ɗaga murya a sanda Dr Yusuf yay shiru da maganar da yake, ya zagayo ta gabansa a firgice yana daɗa cewa,"kaci gaba da min bayani Dr, da kamar wuya me?". Dr Yusuf ya kalli gefe guda tsananin damuwarsa da tashin hankalinsa na ƙara bayyanuwa yace,"da kamar wuya ta rayu". Turaki get in to a state of shocked, looking at Dr Yusuf with anxiety, like he did'nt understand what he said, ya buɗe baki zai yi magana Dr Yusuf ya dafa kafaɗarsa yace,"abinda yake nan shi nake sanar maka, bance ba zata rayu ba, but da kamar wuya tayi rai". cikin wani bala'in tashin hankalin da yafi na ɓarawon da aka kama Turaki ya damƙe hannun Dr, sai kuma a hankali kuma cikin mutuwar jiki yace,"Dan Allah Dr ta rayu, na roƙe ka dan Allah, ko menene kayi dan ta rayu ni kuma nayi maka alƙawarin duk abinda ka biɗa daga gare ni muddin bai fi ƙarfina ba zan baka, amma dan darajan Allah karka bari ta mutu". yanda yayi maganar dole yay mugu mugun baka tausayi. Dr Yusuf yace,"Allah ne kaɗai me rayawa da kashewa, zamu yi iya kar bakin ƙoƙarinmu wajen ganin mun ceto ranta, saboda gaskiya akwai matsala babba ma kuwa". Jikin Turaki ya ƙara mutuwa, yaji zuciyarsa na wani irin motsawa yana jin kamar ya mutu ya huta. yace,"wacce matsalace da har zata fi ƙarfin ku Dr?". Dr Yusuf yace,"a binciken da muka yi akwai abinda ya gigitata ya kuma ɗimautata da har yaja a lokaci ɗaya zuciyarta ta taɓu, kuma ta kai ga matakin ƙarshe na stage d, yana zama da wuya akai wannan matakin kaga an rayu sai dai kuma wani iko na ubangiji. yanzu fatan da zamu yi guda ɗaya shine in har Allah yasa ta farka to karta farka da tunanin wannan abin da ya girgizata ya haddasa taɓa zuciyarta a lokaci ɗaya, idan har hakan kuma ta kasance to tabbas farkarkawarta bugawar zuciyarta gaba ɗaya, daga nan kuma shikenan tata ta ƙare". ƙwayar idon Turaki ta kaɗai, yaja da baya ya tafi yana neman madafa saboda jinsa da yake yana neman yanke jiki ya faɗi, yay saurin dafe bango yana kifa kansa ajikin bangon yana jin jikinsa gaba ɗaya ya ɗau shaking. bai san me yake ji ba, bai san ta yanda zai kwantata yanda yake ji ba, haka bai san halin da yake ƙoƙarin shiga ba. Dr Yusuf yayo tattaki yazo kusa da shi ya tsaya tare da dafa kafaɗarsa yace,"yanzu taimako guda ɗaya ta-ke da buƙata a wurin mu shine jini...". tun bai ƙarasa bayaninsa ba Turaki ya damƙi hannunsa suka nufi hanyar fita, cikin gaggawa suka fito a tare suka nufa situation room ɗin da Fillo ta-ke. tana kwance kamar gawa, kallo ɗaya Turaki yayi mata ya kasa dauriyar riƙe hawayen dake cikin idonsa, kawai ya sake su suka sauko, kamar ba namiji ba, kamar ba jarumi ba, hawaye yake sosai kuma masu zafin gaske waɗanda yake jin zafinsu tamkar zasu ƙona fatarsa, gwargwadon irin zafin da yake ji a zuciyarsa wadda shima yake jin tana gab da taɓuwa. yasa hannu kamar ƙaramin yaro ya shiga goge hawayen sannan ya kwanta akan gadon da Dr Yusuf ya nuna masa, muryarsa ta fito da wani amon sauti da ba nasa ba yace,"in har da buƙata a kwashe duka jinina a saka mata". Dr Yusuf yay guntun murmushi ganin kamar Turaki ya zauce, yaji tausayinsa matuƙa kamar yanda shima yake tausayin kansa. kuma nan da nan akayi connecting jinin Turaki zuwa jikin Fillo. tun jonawar ya juyar da fuskarsa zuwa kan gadon da ta-ke, lokacin an samu gogge jinin duk da ya ɓata mata jiki, kallonta yake tayi yana mai matuƙar tausayinta a cikin ransa, yana kuma lissafin cewar da zarar ta farka komai na wahalarta yazo ƙarshe, zai zamar mata bango kuma jigo na
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243