Chapter 221
Chapter 221
cikin aljihu sannan yace da ita,"ki sauko ƙasa ki same ni, ina so zan yi magana da ku". taja blanket ɗin ta gyara kwanciyarta kamar bata ji me yace ba. ya juyo yana kallonta,"ba magana nayi miki ba kika koma ki kwanta?, me kike ji da shi ne yanzu?". ta ƙara jan blanket ɗin ta rufe har kanta, yana tsaye yana ta kallonta yana ƙoƙarin sarrafa ɓacin ransa, ya fi ƙarfin minti uku a tsaye Fillo bata ko motsa ba balle yasa ran ma zata tashi ne, ya jijjiga kansa ya fita ransa a mugun ɓace. yana sauka ya tarar Ilham ta shigo a lokacin, tana tafiyar yauƙi ta wuce ta zauna kan kujera, sai kallon parlon take yi tana taɓe baki kamar wacca taga kashi, mamaki take yi sosai har cikin ranta, bata taɓa zaton kaya masu shegen kyau da tsada ba ne aka zubawa Fillo. kusan zata ce kuɗi daidai ne da nata, kuma in har ba son zuciya ba colour ɗin funitures ɗin Fillo sun fi nata kyau sosai ma. sai da aka kwashi kusan mintuna goma kafin Fillo ta sauko, sanye take da hijab har ƙasa, fuskarta wasai kamar bata da damuwar komai, sai ma bacci da ya fara nuna alamarsa a fuskartata. tun da ta taho Ilham ke kallonta idanuwanta kamar za su faɗo ƙasa, zuciyarta tayi mugun bugawa da wani masifar kishi, ta haɗiye yawu da ƙyar a maƙoshinta, dama har haka Fillo ke da azababben kyau bata sani ba?, a yau dai ba zata so zuciyarta ba kam Fillo ta ci uwar ubanta a kyau, kyan nata har tsoro ya bata, yarinyar ta koma kamar ba ita ba, ta ƙara fresh da kyau me matuƙar ɗaukan hankali, sai ƙyalli take yi, ga shi kallo ɗaya zaka yi mata kasan tana ɗauke da ciki, bata san lokacin da wani uban gumi ya wanke mata wuya ba, ta damƙe hannunta a jikin kujerar tana ji kamar ta tashi ta bar parlon. Fillo ta wuce ta kashe tv, sarai ta san Turaki kallon news ɗin yake yi, ya bita da kallo, tun ɗazu yake a hasale da ita, ya lura ta ɗauki salon rashin mutunci, dole zai taka mata burki tun kafin akai ga nisa, don ba zai ɗauki wannan banzan halin ba, har ta dawo ta zauna kusa da shi bai ɗauke idonsa akanta ba, so yake ya karanci ma'anar murmushin da yaga tana yi tun da ta sakko. "i'm sorry Jannaty, haɗewa nayi da shaf'i da wutri shiyasa na ɗan ɓata lokaci, i hope hakan bai ɓata maka rai ba". tayi maganar tana kallon Ilham ta ƙasan ido, wacca ta cika tayi fam tana kallon yacca Fillo ta wani maƙale a kusa da Turaki. Turaki ya sauke numfashi ya dube su gaba ɗayan su, ba tare da ɓata lokaci ba ya shiga yi musu nasiha akan zamantakewar su, ya faɗa musu yacca yake so zaman su ya kasance, ya faɗa musu abubuwan da yake so su kiyaye gudun ɓacin ransa da na su. daga ƙarshe kuma ya tsara yadda kwanakin kowacen su zai kasance, sannan ya ba su damar jin ta bakinsu, Fillo na wasa da yatsun hannunta ta ce,"duk yanda ka yanke Jannaty ni kam yayi min". ya kalli Ilham, wacca ke kallonsa fuskarta na bayyana rashin amincewarta akan hakan, sai da ya ɗaga mata gira ya ce,"ehen, ko kina ciwon baki ne?". ta kawar da kai gefe guda tana cin nagani ta ce,"da dai ka ƙara, kwana biyu sai kace a zamanin da, ko gidan ƙawata kwana huɗu ake yi musu su da suka fi mu jimawa ma kenan". Turaki yay mata mugun kallo kafin ya ce,"to kwana biyun na yanke ba zan ƙara ba, nan gidana ne ba gidan ƙawarki ba ne". ya danne ɓacin ran da ke ingizo shi, ya ci gaba da yi musu nasiha sosai, irin nasihar da kowaccen su sai da taji a zuciyarta, bayan nan yay musu adu'ar zaman lafiya, kafin nan ya rufe taron na su da adu'a. cikin ƙarfin hali Fillo ta danne bala'in abin da ke taso mata ta ce,"Allah ya amsa dukkan adu'oin da kayi mana ranka ya daɗe, insha'Allahu ta ɓangarena ba zaka taɓa samun wata matsala ba, zan kiyaye dukkan abin da baka so, haka zan yi ƙoƙarin aikata duk wani abu da kake so domin farin cikinka, na yi maka alƙawarin hakan muddin numfashina". sai kuma ta kalli Ilham tace,"abokiyar zamana ina yi miki barka da dawowa, ina fatan zamu haɗe kanmu mu zauna lafiya kamar yanda mijinmu ke so, ni dai ta ɓangarena ba ki da damuwa na ɗauke ki tamkar ƴaruwa ta jini. bismillah gaisuwar musulunci". ta faɗi hakan tana miƙawa Ilham hannu don su gaisa, but sai Ilham ɗin taƙi miƙa mata nata, ta yi mata kallon sama da ƙasa tare da jefa mata wani irin wulaƙantaccen kallo. ɗan runtse idanun Fillo tayi tare da yin murmushin takaicin da babu wanda zai fahimta, bata san cewa ita ma ba har zuciyarta ba, yanda bata so ta haɗa hannu da ita haka ita ma, don ko ace ma ta amince su gaisa ɗin cikin dabararta zata aiwatar da abin da zai hana hakan, ai ba don Turaki a wajen ba kallo bata isheta ba. Ilham ta miƙe a zafafe zata fita ta bar parlon Turaki ya dakatar da ita. "ta wurinki zan fara samun matsala kenan ko?". Fillo ta miƙe ta ce,"zan wuce ɗaki, Allah ya bamu alkhairi ya tashe mu lafiya, sai da asuba ranka ya daɗe". tana faɗa ta wuce upstairs cikin natsuwa, Ilham ma ta bar parlon kamar wacca iska ke tunkuɗawa. tun da Fillo ta koma ɗaki taji bacci ya ƙara ƙauracewa idanuwanta, ta gaza danne abin da take ji a zuciyarta don ta samu ta saita kanta, gaba ɗaya zuciyarta a cunkushe take, bata taɓa zaton zafin kishinta ya kai har haka ba sai yanzu, tayi saurin faɗawa toilet tayi alwala tazo ta tayar da sallah. salloli tayi ta jerowa, gani take kamar idan tayi kuskuren sallamewa zata iya yiwa kanta rauni. bayan ta idar tayi zamanta akan dardumar tana tasbihi, lokaci zuwa lokaci sai ta sharce ƙwallar da ke sakko mata.. zuciyarta zafi take yi mata sosai, hatta kanta jinsa take yi tamkar zai rabe gida biyu, gaba ɗaya jin duniyar take babu daɗi sam, wataƙila in ace yau ba zata yi kwanan gidan nan ba da zata iya samun sassaucin raɗaɗin da take ji a zuciyarta. a can ɓangaren Turaki kuwa tun komawarsa ya tarar Ilham ta rufe ƙofa, bai ko bi ta kanta ba ya wuce ɗakinsa, sai dai tun da ya koma zuciyarsa ta gaza yi masa daɗi, tazara!, irin tazarar nan da bai taɓa zaton zata kasance tsakaninsa da Fillo ba, ko da sukai shariyar juna ya kan shiga duk dare yaga sleeping beauty face ɗinta. ya zata ji yau zata kwana a ɓangarenta ita ɗaya ba tare da motsinsa a sashin nata ba?, sai yay shiru kawai tare da rufe idonsa, haka kawai ya ji ya damu sosai akan halin da yasan babu makawa tana cikinsa yanzu. ya san yay mata rashin kyautawa, bai kamata ya shareta ba har ya canja mata ya zamar mata wani kalar mutum na daban da bai raineta akan hakan ba.
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243