Chapter 101
Chapter 101
na tayaku da adu'a, amma ni ban san aina zan ganta ba". yace,"adu'an ma mun gode. bye". da sauri tace,"da gaske sai next year?". ta tambaya tana tsare shi da ido. sai taga kamar yayi murmushi sannan ya ɗaga girarsa alamar ehh. ta sake cewa,"to kana kula da kanka?". ya girgiza mata kai alamun a'a ba tare da yay magana ba. tai ajiyar zuciya kamar zata ce wani abu sai ta fasa, haka ɗaya take jin bata so ya yanke kiran, haka ɗaya take ji kamar idan ya kashe wayar shikenan ba zata ƙara ganinsa ba, hakama kamar ba zata ƙara jin voice ɗinsa ba. ya katse shirun nata da faɗin,"kin daina jin baccin?". ta ɗaga kanta,"ehh ya tafi. ba zaka jira Adda Zaytuna ɗin ta fito ba?". ya girgiza mata kai baice komai ba. tace,"tom shi abokinka ɗin da ku ka tafi tare fa?". yace,"ba shi wayar zanyi?". ta tura baki gaba tace,"ince masa me?, tambaya nayi ko yana kula da kai". Turaki na murmushin leɓe yace,"ai ba wanda ya biyasa kuɗin kula da ni. shima ta kansa yake". tace,"to magani fa?". yace,"haka kawai ake shan magani da ma?". Tace,"ai kai baka da lafiya". daga ita har shi ba wanda ya ƙara cewa komai, tana ta gyangyaɗi riƙe da waya yana kallonta, ƙarshe sai kashe wayar yayi ganin kaman tayi nisa a gyangyanɗin. Zaytuna na fitowa ta sameta akan gadon ta ɓingile tana bacci riƙe da waya a hannu, ta tasheta ta gyara kwanciyarta akan gadon. washe gari Fillo dai bayan sun gama aiki, leson teacher nasu ya tafi ta kama hannun Ɗausiyya tayi mata rakiya ɓangarensu. tana shiga ta faɗa jikin Kaka ta rungumeta cike da murna, Kaka tace,"ai ce nake kin koma can gaba ɗaya?". Kaka tayi maganar itama cike da jin murnar ganinta, kamar sun shekara basu ga juna ba. Maijidda ta kama hannunta ta jata zuwa cikin ɗaki tana cewa,"yarinya zo kiga kayanki. wallah sunyi kyau harda irin shaddar ƴar gidan Mamu aciki". Fillo dai tunda ta zauna gaban ƴar ƙaramar akwatin, kallon yacce Ɗausiyya da Maijidda ke aikin fito da kaya kawai takeyi. ita dai ji take kamar bata murna bata farin ciki da ganin kayan, kuma kamar tana farinciki ta dai rasa taƙamemen abinda take ji ɗin. har la'asar suna zaune, Maijidda da Zakiyya itama Jikar Yami da tazo hutu har Ɗausiyya suna ta tsara abubuwan da zasu yi lokacin biki. Zakiyya na cewa,"ke Fillo kike cewa ai kar a fara shiri yanzu, lallai baki san halin lokaci ba. to wallah yanzu za kiga wata biyun tayi, gwara duk abinda kika san zaki yi ki fara shi tun lokaci bai ƙure miki ba". Maijidda ta janyo Fillo jikinta ta raɗa mata abu a kunne tana dariya, Fillo tayi tsaki tana tureta. Maijidda suka tafa ita da Zakiyya suna tsokanar Fillo da cewar,"an matan Amir an kusa shiga sahun manya". Fillo dai babu wanda tanka. Yami ta shigo ta ƙwalawa Fillo kira ta fito, tazo ta durƙusa tana gaida Yamin, itama Yami na tsokanarta da cewar ai tayi zaton kunyar ba zata ƙara barinta shigowa ba har ai auren. kunya ta ƙara kama Fillo, Yami ta miƙa mata robar wani magani tace,"shanye wannan yanzu". ta karɓa ta shanye da ƙyar duk ba wani rashin daɗi ne da shi ba. sannan Yami ta ƙara ce mata,"kun gama jarabawar?". tace,"za dai mu fara Yami". tace,"to za ki ke samun shigowa kullum ko na haɗa miki magungunan ki tafi da su?". tai shiru bata ce komai ba tana kallon tulin wasu takarcen magani iri-iri, dama tun washe garin da aka kawo kayan Maijidda ta fesa mata labari wai Yami tasa a kawo mata magungunan da zasu gyarata tun daga sokoto da niger, ita dai haushi ne ya tuƙeta a lokacin saboda taƙi jinin taji ana cewa,"maganin mata ko kuma maganin gyara mace". Yami ta ware wasu ta zuba a leda tace,"gasu nan ki tafi da su, basu da ɗaci babu bauri babu komai, su zama sune ruwan shanki kinji ko. wannan kuma haɗin zuma ne itama kike sha akai-akai, dan Allah Fillo karki mana asarar kuɗinmu, in kin mayar da hankali kinyi amfani da su kanki kika taimaka". ita dai Kaka na daga gefe tana jinsu, bata ce komai ba har sai da Yami ta gama sannan tace,"da ki haɗa mata da wannan ruwan tsarkin ko, tunda naji Babuwan tace shima da wuri zata fara amfani da shi". Yami tace,"kinga kuwa na manta, shi da tace ma ya rage wata biyun zata fara amfani da shi". nan dai Yami ta haɗa mata duk abinda ya kamata ta kuma yi mata bayani. wajen biyar da rabi na yamma Hajiya Madina ta kira Fillo tace taje ta ɗauko mayafinta tazo ta rakata anguwa. wata sabuwar shadda da Maama ta ɗinka musu ita da Ɗausiyya ta saka, shaddan ash colour me duhu, an mata ɗinki me kyau ajiki kai ba kace ɗinkawa akayi dan a bawa ƴan aiki ba. tana zaune a parlo Hajiya Madina ta sauko daga stairs, waya ce riƙe a hannunta suna vedio call da Turaki, tana faɗa masa irin yacca kowa ke missing ɗinsa har Baffa, tana basa labarin Ilham ma jiya ta ke cewa zata biyo shi sai taji cewar baya Hong kong yanzu. irin yacca suke hirar kamar ba ɗa da uwa ba. Bello a gefensa yace,"Maama ni ba kuyi missing ɗina ba kenan, alhalin ni ke kulawa da shi". cike da tsokana Maaman tace,"Bello ke kuma wa acikin kayan miya, a'a Hammanmu dai shi muka sani, hatta ƴan aikin gidan nan sunyi kewarsa, yaushe rabon yay nisa damu irin haka, wlh gidan duk ba daɗi". ta miƙawa Fillo jakar hannunta tana cewa da Turaki,"tom zan fita ne, zanje wajen wannan matar da na faɗa maka nasa ta nema min marayun da za'a ke taimaka musu kullum, to shine zanje naga inda take da zama". Turaki yace,"ok to Allah ya taimaka ya bada lada, Nihal ce kusa da ke?". tace,"a'a su duk sun fice ai, ana bikin ƙawar Zaytuna sunje dinner party, ka san Baffanku ba so yake ba shisa nace suje mata da wuri su dawo da wuri, yafi ace basu je ba gaba ɗaya". Turaki ya sauke numfashi kaɗan yace,"Maama ke ɗaya kuma za ki fita?, ki bari mana gobe sa raka ki". tace,"ni da Fillo zamu je, bani ɗaya zan tafi ba me Babban suna". yace,"yauwa hakan yafi ai". sai kuma ya shafo wuyansa yace,"Maama please ko za ki bata ta kaiwa Salihu(me gadi), akwai saƙo dana bar masa, ina so naji ko yay concluding abin". ta miƙawa Fillo wayar tace,"kaiwa me gadi da sauri". Fillo ta miƙe tana ajiye jakar hannunta akan kujera, Hajiya Madina tace,"no tafi da jakar ai yanzu zan fito". Fillo dai tunda ta amsa wayar ta fito bata kalla screen ɗin ba, tafiyarta kawai take yi shi kuma yana ta kallon fuskarta da ta haska. ta kaiwa me gadi wayar ta dawo bakin mota tana jiran Maama, wucewar minti biyu sai ga me gadin ya dawo mata da wayar ta karɓa tana kallon screen ɗin, ganinsa yasa ta gaida shi. ya amsa yana ƙarewa kwalliyarta kallo duk da ba wani kwalliya tai ba, farar powder kawai ta sha sai lip balm. tace,"in mayarwa da Maama wayan?".
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243