Skip to content
NovelPress

Hausa Novels

Chapter 129

Chapter 129

Lullubin Biri Book 1 Complete Hausa Novel 1,221 words 0 views Progress saved
Download Book

cewar,"ina fatan bai cuce ki ba?". bata iya amsawa da baki ba sai Kai da ta ɗaga kawai. anan taji Ummin ta sauke ajiyar zuciya me nauyi, kafin ta furta,"Allah ya daɗa kare min ke, ya kareki daga sharrin duk wani abin ƙi. dan Allah kiyi haƙuri ƴata da abinda nayi muku, ban da bakin ce muku komai domin nasan ni ɗin me laifi ce, amma yanzu na dawo gareku sai mutuwa ce zata raba mu, ina roƙonku dan Allah ku yafe min, ki yafe min Autata". Fillo tace,"ni ba kiyi min komai ba Ummina". sai ta ɗago kai tana kallon Ummin tace,"Ummi to ya akai...". kuma karantar fuskarta kawai Ummin tayi ta bata amsa ba tare da ta ƙarasa ba. "Dr Yusuf, shi ya shigo da ni nan yay min nuni da ke, shine sabon ɗan da Allah ya bani wanda ya kula da ni shi da matarsa kusan shekara guda, ba ƙyama, ba hantara, sun ɗaukeni kamar mahaifiyarsu, duk da ni nayi musu laifi na ɓoye musu cewar ina magana tsawon lokacin da muka ɗauka, haka nayi ta wahalar da su da aikin rubutu a takarɗa kuma basu taɓa ƙosawa ba". maimakon kallon Ummi sai Fillo ta koma kallon Dr Yusuf, babu ko ƙyafta ido, kenan shisa watarana da yazo hira wajenta yace mata yana ganin me kama da ita sak, in ace zata yarda da ya kaita ta ganta, tave masa ba wani nan wasa yake yi, ashe Umminta ce ma, Umminta ya taimakawa har yake kyautata mata da irin halin karamcinsa. _"sun ɗauke ni kamar mahaifiyarsu"._ haka Ummin ta faɗa, ƙwarai yau ta ƙara tabbatar da cewa Dr Yusuf na musamman ne, kuma ya zama dole ta saka masa da taimakon mahaifiyarta da yayi, kamar yanda ta san cewa yafi ƙarfin duk wani abu da zata basa, haka bata san irin kyautar da zata yi masa ba domin nuna masa godiyarta, but zata tambaye shi kyautar da yake so tayi masa ko da ace za'a kai ga matakin da sai ta ɗaga zoben azurfarta ta siyar. Dr Yusuf ya sakar mata murmushi, itama ta mayar masa tana sauke idonta ƙasa tace,"Ubangiji Allah yay maka sakayya da gidan aljannah akan taimakawa Mahaifiyata da kayi, Allah ya rabaka da iyaye lafiya"...haka ta dinƙa jera masa adu'a kafin tace masa,"dan Allah Dr a wurin da ku ka tsinto ni ba kuga wata mata ba?". Dr Yusuf yace,"ai ba tsinto ki mukai ba, kawo ki akayi". ta ɗan dube shi da mamaki tace,"bai gudu ba?". yay murmushi kafin yace,"ƙanina ne yanzu haka yana waje tare da su Daddy nah, itama matar da kike magana tana waje, ƙila zuwa yanzu ma su Kaka sun iso dan anyi musu waya tuni". ai rufe bakinsa kenan t a saki hannun Ummi ta diro akan gadon tana ce da Ummi,"ba inwa Kaka albishir". bata jira cewarta ba ta fito da gudu daga ɗakin tana ƙwala wannan kiran sunan na,"Kaka ga Ummina". ba tare da ta lura da jama'ar da suke cike a wajen ba balle tabi ta kan dalilin da yasa akayi wannan dandazon. kuma cikin sa'a tana fitowar tayi karo da su Kaka na shigowa, idonta a rufe ta doka wani uban tsalle ta ɗafe Kaka tana ihun murna tana faɗa mata Ummi ce. Kaka lamarin sai ya nemi ya bata tsoro dan sai take ganin kamar ko Fillo ta samu matsala ne, ta tafi zata faɗi dalilin ɗafe jikinta da Fillo tayi sai taji an saurin riƙota ta gefe. Kaka ta fashe da kuka tana cewa da Fillo,"Fillo ashe dama Amir ne ya ɗauke ki, ashe yaron nan ba mutumin arziƙi ba ne, ashe Amir azzalumin bawa ne, ashe duk wannan kyawun halayyar tasa yardararmu yayi saboda cimma wata manufa tasa, ashe baƙin *BIRI* ne shi ya *LULLUƁE* kansa ta yanda ba zamu shaida mugun ƙudurinsa ba, Allah ya isa tsakaninmu da shi, ko yafiyarmu kaɗai ta ragewa Amir shiga aljannah ba zan yafe masa ba, sai Allah yay mana hisabi da shi, kuma insha'Allah sai yaga sakayya, sai ubangiji ya bi mana hakkin cutarmu da yayi tun anan duniya. yanzu muna kan hanya Khalil ya ɗauko mu ance an kawoki asibiti rai hannun Allah muka ji sanarwar an kama waɗanda sukai garkuwa da ke, wallahi tallahi ban shaida muryar matsiyacin ba sai Yami ce ta shaida, sai kuma da naji an ambaci sunansa, yanzu haka ance gobe za'a kai su kotu Hajiya Madina tace sai yayi zaman gidan yari". sai ta fashe da kuka sosai tana ƙara cewa,"yasa na siyar duk da wani abu da ku ka mallaka a wajen mahaifiyarku, sai da ya tsiyatamu tass Fillo, biyar ɗin kanmu bamu da ita a yanzu, yasa muka ɗauki dukkan yarda da amana muka ba shi?, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, gaba ɗaya tsoron kowa nake yi Fillo, ta ya yanzu zaka iya tantance fuskar mugun mutum da ta mutumin kirki bayan mugwayen na amfani da fuskar mutanen ƙwarai?, Allah ya tawarwatsa rayuwar mutane irinsa a duk inda suke, adu'ata ɗaya Allah yasa bai lalata miki rayuwa ba". Fillo ta zame daga jikinta, tasa hannu ta goge hawayenta tace,"bai ida mugun nufinsa ba Allah yaɓullo min da hanyar guduwa, Kaka bana son kukanki dan Allah ki daina, ki manta da zaluncin da Amir yay mana ki barsa da Allah, indai duniya ce ga shi gata nan, yau ba ranar kukan baƙin ciki ba ce ranar kukan farin ciki ne, irin wannan hawayen nawa nake so kiyi ba irin wanda nayi a sanda na san cewar Amir Birin da ya lulluɓe kansa da mayafin da ba mai iya ɓata shi bane. Ummi ta dawo Kaka, Allah ya bayyana mana ita, dan haka ki kalla gabas ki yiwa jalla wa'azza godiya". Kaka bata bar kukan ba tace,"ke wai kina hauka ne, a ina kika ga wata Ummi?". Ummi dake riƙe da Kaka ta gefe ta kwanto a kafaɗarta tace,"gani Dada". "Halimatu". Kakan ta kira Ummi da mamaki matuƙa. "na'am Dada". sai Kaka ta rungumeta tana hawayen farin ciki itama,"Halimatu ina kika je?, dama kina raye Halimatu?, ƴata na yafe miki domin nasan ba komai ya saki barin gida ba sai baƙin cikin mugun miji, amma tsayin wannan lokaci ina kika shiga Halimatu har na ganki haka lafiya ƙalau?, kai Allah maji roƙon bayinsa". Ummi tace,"tashin farko Kawu Nasir ne ya bani goyon baya harma ya ɓoye ni a gidansa, daga nan labarin da yawa, amma waɗan can mutanen da kike gani ɗansu ne ya tsince a sanda na faɗa cikin wani hali, kusan shekara yanzu suke bani duk wata kalar kulawa". nan da nan kuma duka Families biyu sai suka manta da damuwar da ake ciki, a shiga babin farin ciki. dan kamar yanda su Hajiya Madina suka mance da lamarin su Fillo haka suma su Kaka suka manta da lamarinsu, dan suma waje suka samu suka zauna, Kaka sai kwarara adu'a take yi da godiya ga su Yusuf, tunda Ummi ta shiga faɗa mata irin alkhairan da suka yi mata. da ƙyar iyalan Dikko suka safafawa Hajiya Ramla suka bar jikinta, ta bisu da kallo tana cewa Hajiya Madina,"ranki ya daɗe yanzu duka waɗannan yaranmu ne?, har waɗannan samarin?". ta faɗa tana nuna Khalil da Sameer. Hajiya Madina tace,"ƙwarai kuwa". nan da nan ta

Table of Contents

Chapters

243 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243