Chapter 170
Chapter 170
a sanda ka faɗa cikin cakwakiya ta biyu, ban san ka aikata ba kuma ba kai shawara da ni ba a sanda zaka aikata ba, dan haka karka kuskura ka neme ni". yana gama faɗar hakan ya fice, Turaki ya bi bayansa da kallo kafin ya tashi ya wuce ɗakinsa. babu abin da yake so yanzu irin yaje gidan su, amma Baffa ya ajiye ƙaton soja a bakin gate ya ce duk ranar da yaga wata fuska ko da mai kama da tasa ne a kama shi a ɗaure. washegari da safe yana kwance a ɗaki aka murɗa handle ɗin ƙofar ɗakinsa, motsin ƙofar yasa shi buɗe ido yana kai dubansa ga me shigowar, ganin Maama yasa shi miƙewa zaune da sauri, ta iso wajensa tana jin tausayinsa na ratsata, ta zauna a kusa da shi ta dafa shoulders ɗinsa ta ce,"ya ƙarfin jikin naka". ya ce,"da sauƙi sosai". ta bi shi da kallo sosai tana lura da yanayin jikin nasa, babu kumburin ko kaɗan duk ya sace, ramar ce dai kawai da tayi masa yawa. ta sauke numfashi ta ce,"Bello ya ce min ba ya gari shiyasa na taho, ina drugs ɗin naka?". yana kallonta ya ce,"ƙarya yake yi, fushi yake da ni shi ne ya tafi". Maama ta girgiza kai tana murmushi ta ce,"Allah dai ya kyauta muku, anjima ne za ku shirya ai". ta miƙe tana isa table ɗin da yake tsakiya ta ɗauko magungunansa ta dawo ta zauna, ta ɓallo ta zuba masa a baki. "ka sha ka ƙara jin ƙwarin jikinka, anjima akwai dinner. su ma suna kan hanya sun taho kawo Fillo, amma ba nan ɗin zasu kawota ba direct, za su sauka a wurinmu after an dawo da ga dinner sai mu kawo maka ita, hakan ai ya yi ko? baka da lafiya ban zauna nayi shawara da kai ba me babban suna". shi dai bai iya cewa komai ba, Samha ta shigo ta dire basket na kayan abinci, ta zuba a plate kamar yanda Maama ta umarceta. kamar wani ƙaramin yaro haka Maama ta dinƙa feeding nasa, bayan ya gama ci ta cika masa bathtube da ruwan zafi ya shiga yay wanka, sanda ya fito ba ta ɗakin, bayan ya gama shiryawa zai fita sai gata ta dawo. "ai ba fita zakayi ba, koma ka kwanta ka huta. alfarma ɗaya nake so a wurinka me babban suna, ka cire damuwa don Allah, ka ɗauko rigar walwala da farin ciki ka saka, yau babbar rana ce a wurinka, ranar da ta ke zaɓinka". ya ce,"Maama Baffa...". ta dakatar shi tana faɗin,"sau nawa zan faɗa maka in dai batun Baffanku ne ka ajiye shi a gefe, kai fa kujera ne a wurinsa kana zaune zai neme ka, duk wannan hawa saman da ya yi na ɗan lokaci ne, tsohuwarsa na hucewa zai huce, space kawai yake buƙata, kai ma kuma da ma kana buƙatar space ɗinsu, mu kanmu da ka gani ba ya kula mu, jiya ma ya bar mana gidan ya kaɗa inda bamu sa ni ba". Turaki ya ja ajiyar zuciyar zai yi magana ta ƙara katse shi,"Bello zai zo maka da kayan da zaka saka anjima, Khalil zai riga ku zuwa can wajen dinner ɗin". ya gyaɗa kansa kawai kamar yaro bai ce komai ba har ta fi ce. *Taraba* tun safe da Fullo ta tashi tana yin sallar asuba ta shiga toilet ta rufe kanta, a ƙasan tiles ta zauna tana ta kuka ta damƙe takardar sakinta a hannunta, so take ta yi musu bayani amma ta rasa ta inda zata fara. Sai da Ummi ta shigo sannan da ƙyar ta buɗe toilet ɗin ta shiga ta fito da ita, ta bi su Maijidda da duk suke kwance kan gado suna ta baccin gajiya, dan ba su tashi a event ba sai 11 na dare, kuma suka dawo gida suka ƙara ɗorawa da wani ba su suka kwanta ba sai 3, shiyasa sallar asuba ma duk da ƙyar suka yi. Ummi ta zaunar da ita akan darduma ta ɗauko Alqur'ani ta bata ta ce,"kiyi ta karantawa za ki ji sauƙin koma me ke damunki. tun da dai ni da nake mahaifiyarki ma ban isa ki faɗa min matsalar da ke damunkin ba, to ga maganin kowacce kalar damuwa nan ki ta karatu, ƙarfe sha ɗaya naji Dada na batun jirginku zai tashi". Fullo dai kallonta kawai take yi, har Ummi zata fita sai kuma ta ƙara cewa da ita,"in ma kina tsoron faruwar wani abu ne a auren naku ki yi ta ambaton innalillahi wa'inna ilaihir rajiun, Allah zai sanya komai ya zamo mafi alkhairi a gare ki, ni dai har zuciyata bana jin komai a game da tarewar nan taki ba, kullum adu'a nake ina faɗawa ubangiji, kuma na gamsu da son da yaron nan yace yana yi miki". Ummi ta fita ta barta, ita kuma ta buɗe suratul Yusuf ta shiga karantawa, kamar almara sai ta fara jin duk wata damuwa da fargaba da komai yana tafiya yana barinta. ƙarfe takwas Ummi ta dawo ɗakin, hannunta riƙe da tray wanda ke ɗauke da kayan breakfast, ta ajiye a gaban Fillo, ita kuma ta aje alqur'anin hannunta ta miƙe ta shiga toilet ta wanko bakinta ta dawo, tare suka yi breakfast ɗin ita da Ummi, su na ci Ummi na yi ma ta ƴan nasihohi akan sabuwar rayuwar da zata tsinci kanta, da maganganu tausasa da duk suka sanya sauran damuwar da ke tare da ita barinta. ƙarfe tara Ammi ta shigo ɗakin nasu tare da me makeup, ta tarar su Maijidda da Amatullah sun sa Fillo a gaba sai tsokanarta su ke, saboda ta daina kukan da ta ke yi sai su ke cewa ashe dama so take yi akaita gidan miji shiyasa ta ishe su da kuka, yau kuwa ga idonta nan ƙyam sai ƙyallin farin ciki da yake yi, ita dai tana zaune babu wanda ta tankawa. Me makeup ɗin ma sai da ta tsokaneta, Ammi na kallonsu duka ta ce,"to bara ta bar muku ɗakin sai inga wa zaku takurawa". ta kamo hannun Fillo suka bar ɗakin suka wuce sashin Lamiɗo ɗakin matarsa Diyam, anan aka zaunar da Fillo don shiryata, simple makeup aka yi ma ta amma tayi masifar kyau, gyaran jikin da akayi ma ta na 4days sai ka rantse an ɗauki watanni ana yi, sai faman shining take yi kamar fatar kifi, fatarta ta zama kamar madara tsabar kyau. riga da skirt na material me tsada cikin lefen da akayi ma ta na gida, sai aka ɗora ma ta alkyabba me mugun kyau red colour. Dadda ta shigo ɗakin, ta shigo tana faɗin,"kaiii Diyam ɓangarenki ai gaba ɗaya ya karaɗe da ƙamshin amarya". ta ƙarasa tana buɗe fuskar Fillo ta ce,"Masha Allah, Tubarkallah. Lallai Muhammad Turaki ya yi da ce da kyakykyawar ƴar mu, ai danasani na ƙayyade masa sabon sadaki". zuciyar Fillo ta buga, tasa hannu ta dafe takardar sakin da ke maƙale acikin brezier ɗinta. Dadda ta ce da ita,"ungo sha wannan". Fillo tasa hannu ta karɓa tana yatsine fuska, zata yi gardamar da ta saba Dadda ta ce,"ke wannan ba magani ba ne ruwan tofi ne Dottijo ya bayar a kawo miki, ma za yi bismillah ki kafa baki
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243