Skip to content
NovelPress

Hausa Novels

Chapter 72

Chapter 72

Lullubin Biri Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
Download Book

Hajiya Madina ta ƙara fita hayyacinta gaba ɗaya, ta mance ma da wani abu ciwo dake jikinta balle xafinsa, dan idan ma tace zata bi ta kan ciwon tausayin Zaytuna da Turaki ba zai barta ba. cikin wannan hali da suke ne na jimamin ɓatan Ramla kowa ya ƙara tabbatarwa da Alƙali Dikko yayi sa'ar mata a duniya, situation ɗin da Hajiya Madina ta shiga a silar ɓatan Hajiya Ramla ba zai faɗu ba, yanda kasan wacce uwarta ta mutu, abinci wannan bata ci sai an mata da gaske, kuka kuwa da ace ruwan hawaye na ƙarewa tuni nata ya jima da ƙarewa. Hajiya Madina macece ta gari, me kyawun zuciya, wacce babu algus a tare da halinta, wacce take zaune da kowa lafiya take kuma nuna kowa nata ne, bata ƙyamar kowa kuma bata munafurta kowa, dan sau tari akan cewa da Hajiya Ramla matsalar kishiyarki ɗaya ne, bata iya munafurci ba. ita kanta Hajiya Ramla tasan tayi sa'ar abokiyar zama, abunda kowa ke faɗa mata kenan tunda aka auro Madina, shi yasa suke zaune lafiya babu fitina, babu faɗa balle tashin hankali, kansu a haɗe kamar waɗanda suka fito ciki guda. tunda aka haifi Turaki Hajiya Madina ta mayar da shi kamar ɗan cikinta, idan ba sani kayi ba ba zaka taɓa cewa ba ita ta haife shi ba, an aurota dalilin rashin haihuwar Ramla, to kuma sai Allah ya nuna ikonsa ko da ta shigo gidan itama sai da ta shafe shekaru masu yawa bata ko yi ɓarin ciki ba, har Allah ya bawa Ramla ciki ta haifi 2wins maza, ranar suna yaran akasa musu sunansu Muhammad da Lateef, Muhammad shine aka saka masa sunan mahaifin Ramla suke kiransa da Turaki kamar yanda ake kiran mahaifin nata, shi kuma Lateef shine yaci sunan mahaifin Dikko zasu ke kiransa da Abi, to kuma a ranar sunan da daddare sai Lateef ɗin ya rasu. sai da Muhammad Turaki ya shekara huɗu ciff a duniya sannan Hajiya Madina ta haifi nata yaron wanda yaci sunan mahaifinta Ibrahim suke kiransa Khalil, shekararsa biyu shima Ramla ta ƙara haihuwar ƴa mace me suna Zaytuna. part ɗin kowacce daban amma baka ganinsu ba'a tare ba, in kuwa ka gansu separately to dare ne yayi za'a tafi makwanci, amma da zarar safiya tayi sun tafi breakfast side ɗin Baffa, har sanda wani acikinsu zai yi baƙo, ko kuma idan Hajiya Ramla zata tafi office, idan wannan tayi ba daidai ba ɗaya zata gyarawa ƴar'uwarta kuma su amshi gyaran cikin sauƙin kai. wucewar sati da watanni anata saka ran ganin ko Hajiya Ramla zata dawo amma shiru kake ji, da haka har aka shafe shekara guda, kuma a lokacinne aka sallama da cewar ta rasu. dalilin da yasa Hajiya Madina ƙara jan Turaki da Zaytuna a jikinta kenan saboda tausayin maraicin su na uwa, ta rungume su a ƙirjinta tamkar ita tayi naƙudarsu, babu ranar da bata kallonsu bata zubar da hawaye ba har suka girma, ƙarshe ma sai ya zamto tana nuna musu tsantsar so da kulawa fiye da waɗanda ta haifa a cikinta, son su take yi domin Allah ba da wata manufa ba. haka kuma kwata-kwata bata nufar yaran da sharri, abinda zai samesu sai ya ɗaga hankalinta wanda zai sami Khalil ko Samha bai ɗaga mata hankali ba ko kusa, don gani take tamkar in wani abu ya samesu lallai Allah xai tuhumeta domin amana ce da tayi alƙawarin ta ɗauka, ta ɗauki alƙawarin zata riƙe su kamar yanda Ramla zata riƙe su, kuma tayi alƙawarin ba zata kalle su da sunan ƴaƴan miji ko ƴaƴan kishiya ba sai ƴaƴan da ta haifa acikinta. bayan shekara goma a wata rana ta laraba sai ga message a wayar Baffa, saƙon da Hajiya Ramla ta turo musu kan cewar tana nan a raye bata mutu ba, kuma ko da xa'a ɗauki tsawon shekara 100 kar su taɓa sawa a ransu cewa ta mutu, tana nan a raye nesa da su sai dai ba zata taɓa dawowa gare su ba har abada. wannan saƙon ya girgiza kowa, kuma wannan saƙon shi ya haddasa jin haushi a zuciyar Zaytuna, take jin tana tsananin fushi da mahaifiyarta, tana jin yau ko da ace za'a kawo mata gawarta ba lallai ne ta dubeta ba. saɓanin Turaki da saƙon ya ƙara haddasa masa damuwa a ransa, lokacin shekarunsa goma sha shida, yana can europe wurin Kakarsa ta wurin uwa, kuma tun daga lokacin har kullum tunaninsa guda ɗaya ne, a wanne hali Mum take ciki?, ya lafiyarta take?, menene damuwarta?. abu ɗaya har kullum ransa ke basa akan barinta gidan shine, wataƙila tayi fushi da shine, tayi fushi da shi akan tana tunanin cewar shi ya haddasa kamawar wutar ɗakin, alhalin shi bai san da komai ba, bai ma san da cewa wutar ta kama ba sai da tayi magana, time ɗin da ta fito ɗaga toilet tayi wanka tana tsane jikinta da towel, shi kuma yana zaune akan gadonta yana homework ɗin da Hajiya Madina ta basa, sai ji yayi Mum ɗin na tambayarsa aina ya sami ashana har yayi mata ta'adi, ta tambayesa ɗin tana yowa wurin da labulen ya ɗan fara ci zata kashe wutar. yana iya tuna yacca taja tsaki a sanda ta kama labulen da sunan zata watsa ruwan dake hannunta, sai yaga kawai ta tangarar da jug ɗin ya faɗi ya fashe, ta wuce ta isa wadrobe ta ɗauki abaya ta zira ta fita ta barsu a daidai lokacin da wutar ta fara ci sosai, yaji tsoro ya sakko akan gadon yabi bayanta da gudu, sai kawai ta hankaɗosa ciki tana doka masa tsawa bayan ta ambaci ainihin sunansa da bata taɓa faɗa ba tunda ta haife shi, taja ƙofar ta rufe tasa key ta cire ta tafi da shi. wannan ɗalilin ya barwa kansa, kuma har kullum yana roƙon Allah ya haɗa fuskokinsu kamin ya kai ga kushewa ya roƙeta ta yafe musu, ya faɗa mata gaskiyar cewar bai san komai ba akan kamawar wutar. "Hammah Hakimi na magana a waya". maganar Zaytuna ta dawo da shi duniyar tunanin da ya tafi. ya karɓi wayar yana karawa a kunnensa tare da yin sallama. sun ɗau lokaci suna waya Hakimi na tambayarsa yanayin lafiyar tasa, kafin daga bisani suyi sallama. washegari ƙarfe goma na safe akayi discharge nasu suka koma gida. kuma suna komawa inda ya fara dosa bayan sunyi lunch shine ɓangaren ma'aikata, dalilin ganin tun dawowarsu bai ga gimlawar Fillo ba, tun da suka dawo yake ta zuba ido ko zai ga ta wuce amma ko inuwarta bai gani ba, kuma yana ta sauraren yaji wani yayi zancenta har da Maama amma sai yaji ba wanda ya ambaci ko da sunanta. [8/27, 20:15] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* _Please avoid any mistakes._ *25* "barka da shigowa ranka ya daɗe, Allah ya ƙara maka lafiya magajin me gida". adu'ar da ma'aikatan ke tayi masa kenan tunda ya shigo ɓangaren su. yasa hannu a aljihu ya ɗauko bandir na kuɗi ya bawa shugabar ma'aikatan wato Yami, ta duƙa har can ƙasa tasa hannu biyu ta karɓa suna ƙara yi masa adu'oi na fatan alkhairi. tun da ya nufi ɗakin Kaka aka je aka sanar mata, kamin ya ƙaraso tuni ta daɗa kimtsa

Table of Contents

Chapters

243 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243