Chapter 137
Chapter 137
da tayi picking tukunna ta kara masa a kunne. daga can ɓangaren Boɗejo tayi sallama suka gaisa da Baffa, tana kuka ta-ke shaida masa halin da Fulani Azima ke ciki, shi kansa Baffa da ya dawo a jiya jikinsa yayi matuƙar sanyi ya kuma tsorata ainun da yanda ya sami Fulani Azima, ya ƙara jin tsoron Allah da kuma tsoron sharrin duniya, saboda yanda ta dawo kamar ƙwarangwal halittarta dai babu kyan gani a yanzu, har ƙwalla sai da yay musamman da ya fahimci tana so tayi magana da shi, to amma shi har ga Allah ba zai iya bata wannan damar ba saboda ba zai iya zaman kusa da ita ba dalilin mugun ɗoyin da take yi, mijinta kansa sai ta window yake ganinta balle kuma shi, yana ji ma ana batun dawo da ita gida saboda su kansu asibitin sunce ba zasu iya da ita ba. cikin sigar kwantar da hankali Baffa yace da Boɗejo,"kiyi haƙuri, adu'a zamu cigaba da mata Allah ya bata lafiya". ta ƙara sautin kukanta tana faɗin,"Dikko ni ƴarta nake tausayi, a jiya yarinyar nan Ilham tayi suma yafi biyar, ko abinci bata iya ci Dikko, aljanun da bamu santa da su ba sai tashi suke, yau baka ga yanda suka farfasa mata jiki ba". ta faɗa tana kuka sosai. Hajiya Ramla dake jiyo komai ta sauke numfashi tana jinjina al'amarin sakayya, ita dama tun can bata da niyyar tonawa Fulani Azima asiri akan abinda tayi mata, abunda zuciyarta ta yanke mata kawai shine zata barta da Allah sai kuma sun haɗu acan lahira, amma anan dai ba zata taɓa faɗar cewa ga wacca tai silar barinta gida ba, duk da cewar tunda ta dawo ta bada labari kowa ke cewa aikin asiri ne, to amma ko kusa bata yarda ta bar hakan a zuciyar mutane ba, duk da Hajiya Madina taso ta ɓaro komai ɗin dan har sunan Fulani Azima sai da ta ambata tana cewa wallahi sai taci ubanta zata kawo ƙarshen makircin matar, to da ƙyar dai ta tausheta ta bar maganar. Boɗejo na kukan sosai tace,"Dikko ka bawa Ramla wayar ina so nayi magana da ita". "tom shikenan, amma ki daina kukan hakan dan Allah". tace,"Dikko ina ni ina daina kuka kuwa yanzu, ai ni da barin hawaye har sai Azima ta mutu, amma indai zanke ganinta a wannan halin hankalina ba zai kwanta ba kamar yanda hawayena ba zasu tsaya ba, wallahi ma ni daka ganni na yafe mata duk wani kalar rashin kyautawa da tayi min". Baffa ya miƙawa Hajiya Ramla wayar, suka gaisa da Boɗejo, tai ƙasa da murya tana cewa. "kiyi haƙuri Ramla ƙarar ɗanki na kawo miki, wallahi yaron nan azzalumi ne baya tsoron Allah kwata-kwata, kinga dai ko maƙiyin Azima yana zuwa ya dubata amma shi tunda ya kawo matar tasa ya yasar anan bai ƙara waigowa ba, tace min ko kiranta a waya ma baya yi, idan ita kuma ta kira shi suna gaisawa ɗan banzan yaron nan zai kashe wayar baya ko tambayar lafiyarta balle ta uwar dake cikin wani hali, to dan Allah ki faɗa min wannan mijin aure ne, kuma wallahi ƙarya yake yi yace baya son Ilham, dan dai kin ɓata ne lokacin yarintarsa amma da ko ke sai kin aura masa Ilham, to ni dai yanzu abinda nake so daga gareki tunda kin isa da shi kisa yazo wajen matarsa ko da ba zai zo duba Azima ba dan wataƙila sharrin da tayi masa ne bai manta da shi ba, ba haka ake ba sam wallahi, ya kamata yazo ya kasance da ita ya kwantar mata da hankali da irin salon ma'aurata, to da yake dai shi ɗin baida addini shisa, kuma rashin hankali da tunani ke damunsa, duk da nasan Madina ce take zuga shi wallahi, kuma zan dawo ne zata gamu da fushina da bata taɓa gani ba". Hajiya Ramla ta tari numfashinta da cewa,"a'a Boɗejo Maamansa ai ba zata hanasa zuwa ba, ita kanta ina mai tabbatar miki da bata san da wannan rashin tunanin nasa ba da tuni ta tsawatar masa, amma zan faɗa mata insha'Allahu". Boɗejo tace,"to ai dama Madina ta gama hanadameki ke da ƴaƴan, sai yanda tayi da ku. ke yanzu Ramla baki da ikon sawa da hanawa ga ƴaƴanki dake kanki sai dai Madina?, ni ko a tarihi ina na taɓa jin wannan yardar dake tsakanin kiahiyoyi, ai tun a auren nan na san Madina ba haka ta bar mutane ba, to ni dai wallahi tallahi zan baɗawa idona toka, in mance da cewar Turaki jikana ne in maka shi a kotu, Allah sai nayi ƙararsa akan zaluntar Ilham da yake dan ubansa, ina na taɓa jin kalar wannan auren me cike tsantsar zalunci da rashin adalci, wato yana nufin ma bai damu da ita ba ya huta da ƙaya kenanan tunda yanzu bata kusa da shi". Hajiya Ramla ta kwantar da murya tace,"kiyi haƙuri Boɗejo zai zo insha'Allahu". "ke ni rufe min baki sokuwar uwa kawai wacce wata ta fita iko da abinda ta haifa". tai maganar a fusace tana kashe wayar cikin ɓacin rai, daga can ɓangarenta sai masifa take yi a asibitin muryarta ta karaɗe ko'ina, faɗawa me martaba take cewar yazo ya kaita kotu na ƙasar nan wallahi sai ta kai ƙarar Turaki akan wofuntar da matarsa da yay, sai taga ubansa Alƙali d ya tsaya masa. Baffa ya dubi Hajiya Ramla dake riƙe da waya tai shiru fuskarta na bayyana rashin jin daɗi, ya karɓi wayar daga hannunta wannan yasa tayi firgigita ta dawo daga gajeran tunanin da ta lula, ta sakar masa murmushin da bai fito daga can ƙasar zuciyarta ba, Allah ma ya sani ko kaɗan bata farin ciki da wannan auren tun a ranar da ta san Ilham ƴar Fulani Azima ce, kuma in ace taso a ranar ko minti ɗaya Turaki ba zai ƙara ba da auren Ilham akansa, sai ta sa ya saketa, to amma babu yanda zata yi tunda har ubangiji ya riga ya shirya faruwar hakan, tsoronta ɗaya kar Ilham ta cutar mata da ɗanta tunda shi hali ana tsotsarsa a nono. muryar Baffa na bayyana ɓacin rai yace,"a zatona tunda har an riga anyi auren kuma yayi haƙuri shikenan komai ya wuce, ashe ƴan banza ya mayar damu, to wannan yaron sai na saɓa masa, naga alamun sai mun saka ƙafar wando ɗaya da shi, sai nayi fatali da wannan son da nake masa in har bai riƙi matarsa da kyau ba, shikenan sai ace ni ne ban isa da yarana ba, ita yarinyar ba biyayya tayi ba ta haƙura da zama da shi har take kyautata masa, ko dan ubansa an faɗa masa ita so takeyi, zai gamu da fushina tabbas, zai haɗu da ni". Hajiya Ramla ta sauke numfashi a sanyaye tace,"ai duk da kun aura masa wacce yake yaso da hakan bata faru ba, haka itama da kun bata wanda take so da hankalin ƴarku ya kwanta, da mijinta ya girmama halin da mahaifiyarta ke ciki. to amma ya zamu yi tunda me faruwa ta riga ta faru, wata matsalar dai muke ƙirƙirarta da kanmu yayinda ta zamar mana damuwa sai mu kirata da ƙaddara, kuma ma dai banda rashin adalci har ba'a ga
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243