Chapter 216
Chapter 216
nan ina Abuja, shi ma ɗan banzan Bellon da ya biyewa Baffa ya mayar da shi can abujan, ai sai da na faɗa masa ya dage ya barsa su ci gaba da aikinsu anan. ban ma san munafikin dai da ya bayar da shawarar buɗe wani kamfani ba tare da saninmu ba, ko da yake yanzu ai mu ƴan banza ne a wurin Baffa, duk ya mayar mu ƴan wofi, wannan fitinanniyar tsohuwa duk ta bi ta hargitsa mana zama, Allah ya shiryeta kawai, yanzu tun da dai an mayar da auren sai ta bar hankalin kowa ya kwanta". ta kamo kunnen Nihal da ke shigowa ta murɗe,"ke, ke, ke, ki kiyaye ni fa". "Maama wallahi Hammah ɗin ne fa ya koro ni, wai daga nace ba za'a bawa masu jeran kayan Ilham abinci ba". "mtsww Allah ya sauƙa, to Mum ɗin ku tace ki wuce ki karɓo mana kayanmu tun ranki bai ɓaci ba". "ehh yanzu zan tafi, Maama to sauran kuɗin ai za ki cika min". "nawa ne?". ta ɓoye ƴar dariyarta tana leƙo jakar Hajiya Madina dake saman gado ta ce,"jiya na ƙara kai ɗinki na set uku, su zan saka ranar da za'a kai amare, balance ɗin dai har na ku yace 35k za'a bayar". "idan kuma babu naki fa?". "20k". ta zauna bakin gadon ta ɗauko jakarta, ta ƙirgo kuɗi 20k ta miƙawa Nihal ta ce,"ga namu ɗin, naki kuma bari nayi miki kwatancen ɓangaren Baffa ko kuma na ba ki lambarsa kawai, sa 08065....". kowa a ɗakin yasa dariya hatta Zaytun da ke kuka tun ɗazu, Nihal ta fara shagwaɓa tana zama kusa da Hajiya Madina ta shiga yi mata kirari da kalallameta. Umman Nadiya ta ce,"gaskiya ya kamata dai a bawa Auta kuɗi ta karɓo nata ɗinkin ita ma, ba wani sai taje gun Baffa". Hajiya Madina ta ce,"wannan ƴar fa da kike gani tun da biki ya taho ta fara fashin kuɗi, daga shekaranjiya zuwa jiya kawai tayi min fashin kuɗi sun kai kusan 100k. tsabar rashin sanin darajar kuɗi jiya makeup ɗin 20k akayi mata, ɗaurin aure kawai ba wani event ba. her Excellency kuwa ce tayi sai jiya ta ankare da ATM ɗinta, ta manta shaf ta bawa Nihal tun ranar da aka je jeran kayan ɗakin Samha, ƙarshe dai ta talauta ta babu ko sisi a account ɗin nata, to ni dai na bata shawara nace ta makata a kotun alƙali Dikko kawai, ina dalili yarinya duk ta bi ta yashe mu". "Allah Maama kina da kuɗi, to ki ban 5k sai Mum ta cika min 10k ɗin". "yo Nihal ko da Kakar ki Boɗejo uwar masifa kike tafe ai biyar ba zan ba ki ba, don haka ki tashi ki kama gabanki kawai, kije can wajen Uwaki ta ba ki". Zaytuna ta ce,"ke yarinyar nan wai me kike yi da kuɗi?, Maama ɗa zu ma fa tasa Hammah Bello ya turo mata 20k, ina jinta kuma again tana bin Khaleel tana yi masa ƴar murya". Nihal ta tura baki gaba ta ce,"daga yau ba zan ƙara tambayar mijinki kuɗi ba balle ki zo kina min tonon silili, kina terere da ni mijinki ya ban dubu ashirin. shi ma Hammah Khaleel ɗin da ya ban sai da ya faɗawa duniya ya bani, shiyasa zan mayar masa da kayansa, to wai ma idan baku bani ba waye zai ban? Hammah ne kaɗai a gidan nan zaka tambayrsa kuɗi ya baka kai tsaye babu ƙurewar tambayoyi". Hajiya Madina tace,"ba kya tambayar na hankali ne shiyasa, tambayar ƴan fashi kike yi, ban san ba kuma ko jari za ki kafa da kuɗaɗen mu". "Maama to ki ban don Allah, haba Maaman Hamman'mu, Maama me haƙorin maka guda biyu, Maama ƙawar Boɗejo, Maama ta hannun dama na". Hajiya Madina tayi dariya ta make hannunta dake kan haɓarta,"zan ci gidanku Nihal, naga alama kin mayar da ni Kakarki". sai kuma ta ɗauko kuɗi a jaka ta bata ta ce,"ga 5k nan daga haka ba zan ƙara ko ficika ba". Nihal ta rungumeta tana yi mata kiss,"Allah ya bar min ke uwar marayu har ma da masu uba, i love you so much. Allah yaja mana da ranki". lokacin Samha ta shigo ɗakin, bayanta wasu yara ne su uku ke biye da ita, Hajiya Madina ta bita da kallo, cikin sigar tsokana ta ce,"don Allah Umman Nadiya kin taɓa ganin amarya mara kunya irin wannan?". ta nuna Samha da ta wuce wadrobe ta buɗe tana ɗebo kaya. "ina irin ƴar ƙwallar nan da ake yi ta ranar ɗaurin aure, to in faɗa miki yarinyar nan dai bata yi ba, jiya Zaytuna na kuka ita tana wage haƙora talatin da biyu a waje, duk sai ta bani kunya...". Samha ta katse maganar Hajiya Madina da cewa,"kai Maama, ni yaushe akayi hakan, Allah ma nafi Adda kuka". "yo camera ai ba zata yi ƙarya ba, za'a kawo bidiyo ko bayan raina Umman Nadiya za kice na faɗa". Samha tayi murmushi ta ce,"Maama ina tawa atamfar?". "ki ka bani ajiya?". "Maama daga wurin Mum ɗin fa nake tace Adda ta taho da kayan nan". Zaytuna ta ce,"nawa kawai na ɗauko na bar miki naki acan, kiyi sauri kije ki duba in ba haka ba a ɗauke, kin san ɗakin Mum wasarairai take da shi, na nemi sarƙata sama ko ƙasa na rasa". cikin sauri Samha ta fita bayan ta ce da yaran su biyota da kayan da ta ba su. Nihal ta matsar da bakinta kusa da kunnen Hajiya Madina tace,"Maama gulma zan miki, kin san me Hammah yaywa Fillo kuwa?". Hajiya Madina tayi saurin mayar da hankalinta gareta. sai kuma Nihal ɗin ta tashi da sauri tana cewa,"kai ba ruwana, ba za'aji mutuwar sarki a bakina ba". ta faɗa tana saurin ficewa ta bar ɗakin. Hajiya Madina tabi bayanta da kallo, kafin ta mayar da hankalinta kan maganar da Mama Bilki ke yi mata. "Zaytuna za'a fara kaiwa kenan?". "ehh ita za'a kai gobe, jibi akai Samha sai gata mu karɓo amaryar Khaleel, ita anan zata zauna tare da mu, wancan matar ta me Babban sunan kuma yau za su kawota". Tana faɗa ta miƙe ta fita ta bar ɗakin, don hankalinta bai kwanta ba da maganar da Nihal ta fara yi mata, duk yanda akayi an sami wani misunderstanding tsakanin Turakin da Fillo, dan ta lura tun jiya da aka mayar da aurensa ya zama wani kalar masifaffe, da asuba ma tana jin Khaleel na complain ɗin faɗan da ya kama yi musu na babu gaira babu dalili, to tsoronta kar ya sauke fushinsa akan baiwar Allah, ita da ba ita tasa aka mayar da auren ba, wacca ita ta ma fi shi takaicin mayar da auren, don ta lura da hakan a tare da Fillo, kawai don dai yarinyar na da haƙuri yasa bata nuna ba, sai ka ɗauka ma ko bata san ciwon kanta ba shiyasa take ta hidimarta ko a gefen yatsarta. fatan ta ɗaya Allah yasa ba Boɗejo ba ce taje ta kunna musu wuta a gida. ko kuma halin jiya ya maimaita musu, don ance jiya ma kafin ɗaurin aure kusan rufe Fillo da duka yayi. **** "yauwa bayan kin auna fulawanki sai ki zuba butter, ki kwaɓa yeast ɗin da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243