Chapter 103
Chapter 103
masa halin da take ciki, sai dai kamin yace komai Hajiya Madina ta yanke jiki ta faɗi a lokacin, dalilin abinda taji Ɗan Usaini na faɗawa me gadin wajen. "to ni dai bana ce hakan ba ne, zargi kawai nake da hasashe. kaga bakin bishiyar can anan naga motar tayi parking, kuma wallahi tun lokacin da zan tafi fitsarin naji hankalina bai kwanta da motar ba, to kuma sanda nake dawowa sai naga motar na barin wajen, sai na bita da kallo har ta ɓacewa ganina, kasan Allah ba wai don saboda ɓatan yarinyar nan ba, jikina kawai naji bai aminta da motar ba, Ya Rahmanu dai yasa ba ƴan garkuwa bane suka yi gaba da yarinyar nan". da hanzari akai kan Hajiya Madina, da ƙyar aka iya kamata aka sakata a mota sai asibiti. Tunda suka isa asibitin aka karɓe ta aka shiga bata taimakon gaggawa saboda yanayin yadda ta ke a sume, su na tsaye cirko-cirko a ƙofar ɗakin aka shiga da ita suna jiran suji me likitan zaice in ya fito, ba'a fi mintina biyu ba ya fito yana ƙarasa zare gloves ɗin hannunsa a lokacin ne kuma Baffa ya iso wajan da hanzarinsa. ganinsa yasa Ɗan Usaini nufarsa, sai dai ko ta kansa Baffa bai bi ba yay wajen likita. "Likita ya jikin matata?" Baffa ke tambaya yana kallon likitan da yake goge hannunsa da hand sanitizer. ya kalla Baffa yace,"Patient ɗin ku jininta ya hau sosai, akwai abinda ya firgita ta lokaci ɗaya shiyasa BP ɗinta yayi high, wannan dalilin ya saka ta suma, but yanzu an saka mata drip kuma da izinin Allah da ta farka zata dawo dai-dai." Ɗakin Baffa ya shiga ya tarar da ita a kwance tana bacci, ya zauna gefenta ya kamo hannunta yana ta kallonta, tausayinta yayi matuƙar kama shi, ya sa ni fiye da hawan jini ma za'a iya faɗa indai akanta ne, saboda ita macece da bata iya saka abu a ranta ba, tana da saurin ruɗewa nan da nan musamman akan ƴaƴanta, haka ma akan wanda ta damu da shi, ta kan kasa juriya da dauriya. ya san tana matuƙar son Fillo, dan ko da yaushe suka zauna tana yawan masa labarin yarinyar, irin tarbiyar yarinyar da hankalinta da natsuwarta da kamun kanta, har ta kance masa ita ina ma ace yarinyar ta zama rabon wani acikin Khalil ko Turaki. kuma sau tari tana faɗa masa insha'Allahu zata yi iyakar bakin ƙoƙarinta wajen ganin yarinyar ta samu wadataccen ilimi domin itama rayuwarta ta inganta, yarinyar ba kalar yaran da za'a banzatar da rayuwarsu ba ne. Hajiya Madina bata farfaɗo ba sai bayan sallar isha'i, kuma tana farkawa idonta ya sauka akan Baffa dake waya da wani police yana shaida masa ɓatan Fillo, sai dai suna haɗa ido yay saurin sallama da police ɗin gudun kar taji a ƙara samun matsala. ta kama hannunsa tana faɗin,"Baffa yarinyar mutane, ƴar mutane ta ɓata a hannuna Baffa, me zance da iyayenta Baffa?, me zan faɗawa mijin da zata aura Baffa?, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, wallahi wallahi banda masaniyar inda tayi, Baffa wallahi da nasan hakan zata faru ba zan fita da ita ba". daga yanayin yanda take maganar kasan bata cikin hayyacinta. sai kuma tayi shiru tana kallonsa kamin cikin sanyin murya tace,"Baffa an ganta ne?, Ɗan Usaini ya nuna motar mutanen?". ta faɗa tana sakin kuka me ban tausayi. Baffa Ya kama hannunta sosai, ya kwantar da murya yace,"Please stop crying, Insha'Allahu za'a ganta very soon, ba wai ɓata tayi kamar yanda muke tunani ba insha'Allah". tace,"Baffa ta ya?, Ɗan Usaini fa yace yaga motar da bai yarda da ita ba, kuma fa lokacin ne ta fito ta kawo min wayata, Baffa me kake tunanin ya faru?". Baffa ya ƙara sauke numfashi sannan yace,"ki bar wannan tunanin Madina. kuma insha'Allah cikin daren nan zamu ganta, nayi report mawa police and zasu fara aikin nemanta yanzu". sai ya ɗauko wayarsa yay dialling numbern Inspecter Sise, yana ɗagawa yace da shi,"ta farka, wanne irin bayani kuke buƙata daga wajenta?". Inspecter Sise yace,"ka bata wayar muyi magana". Baffa ya kalla Hajiya Madina sannan yace da Inspecter,"tana da saurin ruɗewa, please a san irin tambayar da za'ayi mata". tambayar kayan dake jikin Fillo da kuma yanayin yarinyar da kamanninta da yanda akayi ta fito duk su Inspecter ɗin yaywa Hajiya Madina, kuma duk ta ba shi amsa, sai dai daya tambayi hoto tace gaskiya bata tunanin yarinyar na da hoto ma. daga nan kuma inspecter ɗin ya ƙara cewa da Baffa zasu yi arresting Ɗan Usaini domin shima zai iya zama suspect nasu. motar police tazo asibitin cikin ƙanƙanen lokaci, aka sawa Ɗan Usaini handcuff aka wuce da shi, hankalinsa a tashe yana ta rantse-rantsen shi wallahi bai san komai ba akan ɓatanta, yaje kama ruwa lokacin, ai masa rai wallahi baida hannu. To har wajen dai sha ɗaya na dare babu wani batu na ganin Fillo ko alamun ganinta, tun Baffa yana ganin ɓatan kamar da wasa har ya dawo ya ɗauke shi da gaske, a sannan kuma shima hankalinsa ya fara tashi. Hajiya Madina dai har lokacin banda kuka da ambaton Allah babu abinda takeyi, ƙememe kuma taƙi yarda aje gida a tambaya ko ta koma, sai Khalil kawai ta yarda Baffa ya kira ya gargarɗe shi akan kar ya bar kowa yaji zancen, kawai dai ya san yanda zai shiga wajen Kaka su gaisa ya gani ko yarinyar ta koma, shima kuma letter ya kira ya sanar musu bata nan. a sanda waɗanda suka ɗauke Fillo suka fito daga cikin gari, lokacin ne kuma suka ƙara speed na motar, gudu na fitar hankali suka dinga shararawa akan titin da babu kowa, gudu na ganganci kamar basa son rayukansu. sai da suka yi tafiya a ƙalla ta awa guda sannan suka shigo cikin wata unguwa, daga nan kuma suka fara tafiya with normal speed gudun jan hankalin mutane zuwa gare su, har suka yi nisa sosai sannan suka sauka daga kan titi suka shiga wani layi, haka suka dinga wuce gidaje da shaguna, sai da suka zo kan wani incomplete building tukunna sukai parking motar, ɗaya daga cikin su ya fita ya buɗe gate suka shiga da motar ciki. compound ɗin gidan ƙato ne, sai da suka je har entrance na shiga cikin gidan sannan sukai parking a wajen. na gaban motar shi ya fata fitowa yana cire face mask ɗin fuskarsa da ya dame shi, sannan wanda yay driving motar ya fito, sai ɗayan da ya rage a baya ya cicciɓo Fillo kamar wata jaririya, shima ya fito sannan suka nufi cikin gidan a tare da sauran. Babban parlo ne da ba'a gama ginasa ba but ansa tiles anyi filasta paint ne kawai ba'ayi ba sai ƙarashen wearing, suka wuce zuwa wani dogon corridor inda ananne zaka tarar da jerin ƙofafi na rooms, a ƙofa ta ukun ƙarshe suka tsaya, ogan nasu shi ya buɗe sannan wanda ke saɓe da Fillo a kafaɗa ya fara shiga, yana shiga ya kwantar da Fillo kan wani ƙaramin gado kamar gawa. Madaidaicin bedroom ne da shi kaɗai akai completing gininsa acikin ɗakunan dake gidan kusan guda 7. ogansu ya ƙaraso gadon ya zauna daga gefe, yasa hannu ya mammari fuskar Fillo don
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243