Chapter 23
Chapter 23
barni ni ɗaya". Turaki yace da shi,"sai ka jira Maaman ta dawo tunda ƙorafi ya kawo ka gidan". Bello yay murmushi bai ce da shi komai ba suka shiga taɓa hira shi da Zaytuna. idon Turaki ya kai kan Fillo da ke durƙushe a wurin har yanzu, wani haushi ya kama shi, tunda ake ƴan aiki a gidan nan ba'a taɓa bagidajiyar yarinya irin wannan ba, shi bai san ba ma ko hankali ne bata da shi kwata-kwata. "ke sai ance ki tashi ki tafi sannan za ki gurgura ƙafafunki ki tafi, ko kuwa kin zauna jin hirar da ba taki ba?". kanta a ƙasa yake, kuma hankalinta ba'a garesu yake ba dan hirar da suke ma bata ji, banda yanzu da maganar tasa ta shigeta, tasan da ita yake, ba tare da ta ɗago ba tace,"ina jira a bani umarnin tafiya ne". rai ɓace yace,"kiyi ta zama har a busa ƙaho". ile kuwa yaga ko motsawa bata yi ba, wani sabon haushi ya turnuƙe shi, duk yanda akai ko aji bata taɓa shiga ba. Fillo dai cikin ranta faɗi ta ke yi akan me zaisa ta tashi ba'ace taje ba salon ace tayi ba dai-dai ba, bata manta da wani lokaci ba lokacin da suka zauna a masarauta, Fulani ta bada aike a kaiwa Yarima Mansur, ita Kaka ta bawa ta kai, ta sameshi a wanjen shaƙatawa shi da abokinsa, data ajiye musu zata tafi ai cikin tsawa ya maido da ita da cewar uban wa ya bata izinin tafiya, akan haka har kusan horar da ita akayi, to dan dai Kaka na da matsayi ne a wurin Fulani. to ita kuwa yanzu me zai sa ta kuma maimaitawa, ai jini ba wasa bane, shi da Yarima Mansur duk abu guda ne, balle shi wannan ɗin da ta ke ganin yana da girman izza. "tashi kije kinji, ki zauna ɗakin baya inda abin buƙata za'a kiraki a waya". Zaytuna ta faɗa tana dubanta. Fillo ta tashi cikin sanyin jiki ta wuce, Zaytuna ma ta fita daga part ɗin zuwa nasu. Bello yana kallon Turaki yace,"Beb ɗin da ta tashi tana da hankali, itama ƴar'uwarku ce?". Turaki yay masa wani kallo,"me yasa baka da hankali ne Bello?". Bello yace,"tambaya fa nayi". Turaki yaja dogon tsaki yace,"baka iya bambamce ƴan aiki ne kai, ko kaga tayi kama da Baffa ne ko Maama". ganin yanda yasha murr Bello yace,"sorry maida wuƙar, ban zaci maid bace saboda surarta na kalla ba kayan jikinta ba". Turaki ya jefa masa wani banzan kallo,"kana nufin muma a rame muke kamarta?". "thats is not what i mean, kuma itama ai ba rama bace da ita, halittar jikinta ce a haka". ba tare da Turaki ya sake kallonsa ba yace,"wataran sai ka rasa idonka akan kallon mutane". Bello yay dariya sosai, daga haka kuma suka ɗora hirarsu ta abokai tare da ƙara tattaunawa akan batun aikinsa da Maama har yanzu ta dage akan ba zai koma ba. *Dubai, 12:00am.* Nuratu ce a ɗakin zaune kan kujera, gefenta tarin drugus ne sai ɓallo su take yi tana zuba su a hannu. ta miƙe ta ƙarasa friedge ta buɗe ta ɗakko ruwa mara sanyi ta buɗe, sannan ta ƙarasa wurin gado ta zauna a gefe. zuciyarta fal da tausayin matar da suka ɗauko a asobiti suna kulawa da ita, ta kai hannu ta ɗago kan matar daga pillon da take kwance. sai a sannan matar ta buɗe nauyayyun idanuwanta ta zuba su kan Nuratu tare da sakar mata murmushi. "sannu Mommi". Nuratu tace da ita tana sakar mata nata murmushin. kai kawai ta ɗaga mata alamar yauwa. matar da suke kira da Mommi ta buɗe baki Nuratu ta zuba mata maganin, sannan ta kurɓi ruwan da shima Nuratu ta bata, ta haɗa ta haɗiye maganin. lokacin Yusuf ya shigo ɗakin, ya ƙaraso ya zauna akan bedside drower, cike da girmamawa haɗe da ladabi ya gaisheta, yana tambayarta sauƙin jikin. kasancewar bata magana sai da ta amsa musu da kai. Yusuf yace,"Mommi yanzu ina ke miki ciwo?". ya tambaya da tsantsar kulawa, ta kalle shi ta sakar masa murmushi tare da girgiza kai alamar babu komai. ya ɗan lumshe idonsa sannan yace,"masha'Allahu, Allah ya ƙara miki lafiya". ta jinjina kai alamar ta gode, sannan ta kamo hannunsa ta riƙe cikin nata, tana shaking nasu alamar nuna godiya a gare shi mara iyaka. ya dubi Nuratu yace,"Mar'atussaliha ki shirya Mommi mu fita outing ta samu taga gari, zaman wuri ɗayan zai isheta haka". Nurata tace da shi,"tom ur excellency". har ya miƙe tsaye zai fita kukan da Mommi ta saka ya dakatar da shi, wannan fashewar kukan nata ya haifar musu da tashin hankali. inda ya koma ya zauna shi da Nuratu suna aika mata tambayar me ya faru. sai dai shiru bata ce komai ba illah hawayen dake daɗa sakko mata, kuka biyu takeyi, kukan baƙin ciki da farin ciki. abunda Yusuf da matarsa suke yi mata iyaka abunda Ƴaƴan cikinta zasu yi mata kenan. _su waye su?, aina suka tsintota?, ina ne nan wurin da ta ke sabuwar rayuwa?._ tambayoyin da suke yawo cikin kanta kenan tun daga ranar data farka a asibiti zuwa ranar da suka ɗaukota suka dawo da ita gidansu. so ta ke tasan amsar waɗannan tambayoyin sai dai ba ta da bakin da zata yi magana, haka kuma bata san ta yanda zata gwada musu ba har su fahimceta. tunawa da wani lokaci yasa ta ɗora hannu a kunnuwanta ta toshe. domin tana jin faruwar abunne kamar a yanzu da ta ke zaune. [8/12, 07:57] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *HalimaAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* *2* "Maijidda na kasa gane wajen". Fullo ta faɗa a sanda ta ke ƙarewa babban filin wurin kallo. Dukkan tunaninta da hasashenta ta ɗora shi a wurin na fiye da daƙiƙa biyar amma sam ta kasa ta fahimci inda akai haƙan ramin. Maijidda na tsaye itama ta ƙarasa bakin kujerun wajen(resting chairs) ta zauna. Ta ajiye digar da ke hannunta sannan itama tabi wajen da kallo cike da nazari da kuma son tunanowa. "wallah Fillo nima na kasa tunawa kin san an kwan biyu...amma wai ajiyar me ki kayi ne a wurin nan?". Fullo bata ce da ita komai ba, sai baki da ta zumɓura mata ta harareta kaɗan. ta zauna bakin tudun da ke wajen tare da naɗe ƙafafunta, kamar wadda ta shiga ajin makarantar allo. Yatsanta manuniya akan leɓanta na ƙasa tana ƙarewa faɗin wajen kallo, da kuma tsirran ciyayin da suka firfito a ƙasar wajen. Cikin zuciyarta tana ayyana ya za'ai ta manta wajen nan, bayan tasan tsawon watanni biyar da aka ɗauko bata ko zo wurin ba, hoton gun na haska mata acikin idonta a duk san da ta tuno, abu ne da bai shafeta ba bai shafi wani nata ba amma ta kasa mantawa da shi a cikin ranta. Ita dai ta san ta kuɗuri aniyar tarwatsa alƙadarin waɗanda su kai aikin dama wanda ya saka su. Abunda ta ke son sani a yanzu shi ne waima waye Muhammad Turaki?, mene alaƙarsa da waɗanda suke neman ganin bayansa?, wanene shi a cikin gidan nan?, me yasa tsawon shekaru takwas da ta ɗauka tana rayuwa a cikin gidan nan bata taɓa ganin ko da gimlawar inuwarsa ce ba sai yau?,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243