Chapter 43
Chapter 43
yake ɓoyewa idan yaje neman aure. tunda ta haihu ta bar zamansa ta koma zaman ƴaƴanta, ba zata iya tafiya ta bar ƴaƴanta a wurin uban da bai san darajar ƴaƴa ba sam, ba zata iya tafiya ta bar ƴaƴanta su gantale ba, gwara ko Hayyo zai kasheta ta zauna ta kula da su, ko da ace sai dinga gutsirar naman jikinta ne, zatai ta haƙuri tana jurewa har Allah ya raya mata yaranta ta aurar da su, daga lokacin sai ta tafi ta bar masa gidan, ta bar masa Yasir tunda shi namiji ne, kuma tasan zai sami kulawa a wurin Yayansa Abdulhamid. Hayyo ya zuƙi sigarin hannunsa ya feso mata hayaƙin yace,"a fito min da tabarma". ta juya cikin parlon tana sa hannu ta goge hawayenta. Hamid na zaune ya kasa ƙarasa cin abincinsa saboda baƙin cikin da takaicin rashin kyan hali na mahaifinsa, ya kalli Yaya da tsananin tausayi, ya sauke ajiyar zuciya yana tuno da tasu mahaifiyar, itama haka tasha fama, dan zai iya cewa ma har yanzu Yaya bata ɗanɗani baƙar kuɗar da tasa mahaifiyar tasha ba a wurin Babansa. adu'a yake kullum, kuma yasan adu'arsu ta karɓu, lokaci kawai zasu jira sai dai idan ba'a raye, but dole-dole za'a zo time ɗin da mahaifinsu most regret all his past, lokacin da Allah ya shirye shi kenan. ya miƙe tsaye jiki a saɓule ya karɓi tabarmar da Yaya ta ɗauko, yana kallon yanda hawaye ke bin kuncinta zuciyarsa na tsinkewa. muryarsa can ƙasa gudun kar Hayyo ya jiyo shi yace da ita. "Yaya dan Allah ki bar kuka, komai lokaci ne kuma komai yana zama tarihi...kin san abinda zai kuma biyo baya idan yaga kina wannan kukan". ya faɗa tare da goge mata hawayen. tace da shi,"na gode Hamid". yace,"abincin nasa na kitchen ko?". ta ɗaga masa kai,"ehh yana ciki, cikin wannan filas ɗin daka siyo mana da azumi". Abdulhamid ya fice hannunsa riƙe da tabarmar. Hayyo na jingine da jikin bango yana ta zuƙar tabarsa cikin ƙwarancewa da jin daɗi. Hamid ya shimfiɗa masa tabar, Hayyo ya zauna har lokacin bai ko kalli Hamid ba. "sannu da dawowa Abba". kamar yanda ya tsammata dama babu amsa, dan shi zai iya cewa rabon da magana ta haɗasu da mahafin nasa tun azumi wata biyu kenan, haka ɗaya babu siɗi ba saɗaɗa, ko ya gaishe shi baya amsawa, hakana duk maganar da zai yi masa ba zai tanka masa ba. dan haka ya miƙe jiki a saɓule ya nufa soro inda ɗakinsa yake, ya ɗauko ƴar ƙaramar radio sabuwa ya dawo ya durƙusa gaban Hayyo. ya kamo gidan radiyon daya san nan ne zaɓin Hayyo, ya ajiye a kusa da shi. lokacin kuwa ana labaran siyasa, cikin ran Hayyo yaji daɗi sosai, dan shi a rayuwarsa daka masa kyautar kuɗi ma gwara ka basa radiyo, tana saka shi nishaɗi musamman idan labaran siyasa ake. amma ba zai taɓa nunawa Hamid yaji daɗi ba balle ma har wata adua ko godiya ta shiga tsakaninsu. jiya da shekaranjiya da bai saurara shirye-shiryen da yake ji ba duk jinsa yayi kamar mara lafiya, saboda tsohuwar radiyonsa taɓaci tun ranar da akayi wani mamakon ruwan sama, ta shige cikin ruwan daya cika ɗakinsa dalilin zubar da yayi. kuma babu kuɗi hannunsa dalilin ma da har ya ɗau wannan kwanakin babu ita. kuma yasan Hamid ya siyo radiyon ne saboda shi, tunda akan ƴan ƙanan yaran ya sauke ɓacin ransa na lalacewar rediyon, dan duk sai daya bi ya zane yaran, ko yau da safe da zai fita yaga shatin wayar daya tsulawa Maimuna a fuska bai baje ba, amma bai ko bi ta kanta ba tunda ƴaƴa ne da basa gabansa, su rayu ko su mutu babu abinda yay masa zafi, haka suyi lafiya ko rashinta ko a gefen yatsansa. ai yasha faɗawa ƴaƴansa da ku da shegu ɗaya na ɗauke ku, shi yasa bana wani ganinku da ƙima. zai fi muku ma ku nemi wani uban ko kwa ɗanji daɗi, amma a hakan dai Hamid yace masa a hakan kuma muke ƙaunarka Abba, muke alfahari da kai, duk tsanani ba zamu taɓa barinka ba, kuma zamu yi duk iyakar ƙoƙarinmu wajen ganin mun faranta maka, wajen ganin bamu saɓa maka ba. zamu maka biyayya, kuma zamu tsare mutuncinka. acikin radiyon aka sako waƙar ɗan ƙwairo, Hayyo ya kama bin waƙar yana buɗe flask na abincin da Yaya ta aje masa. kamar wanda yaga kashi daya ga shinkafar, amma a haka ya cinyeta tas. da yamma Yaran suka dawo daga makaranta, tunda sukai sallama suka ga Abban nasu a tsakargida suka kama raɓe-raɓe jikin bango. suna mugun tsoronsa, sunfi sakewa idan babu shi a gidan, idanma fita yayi sukan manta da shi. wataran Maimuna ta cewa Yaya ita gwara ma ace bata da Baba akan dai ta nuna Abba ace shine Babanta. a lokacin Yaya taita mata faɗa da cewar kata ƙara jin wannan zancen a bakinta, amma duk da haka Maimuna a makaranta bata amfani da sunansa, sai dai sunan Yayansu, Maimuna Abdulhamid haka ta ke using. *VISION APARTMENTS, Zurich, Switzerland.* a tsaye take a gaban windon parlon, windon dake ɗauke da manya manya gilasai, kalarsa ta haɗe da yanayin yanda hasken garin yake a lokacin. lokacin yammaci ne, yanayin garin na nuna cewa ruwan sama bai jima da ɗaukewa ba. sanyin danshin ruwan na ratsowa ya shigowa cikin parlon, wanda ya gauraye da sanyin ac da kuma ƙamshin dake cikin parlon. hakan ya haɗu ya bada wani sanyayyan ƙamshi me daɗi, kalar komai na parlon ruwan toka ne. sanye take da baƙin wando wanda ya ɗameta, hannayenta dake ɗauke da bangles acikin aljihun wandon, riga ce me ƙaramin hannu milk daga ciki sai ta ɗora rigar sanyi me kauri akai, irin rigar sanyin nan me gashi a hularta. hular ta rufe kusan rabin fuskarta. fara ce sosai, me kyan fuska, hancinta har baka, idanuwanta manya. jelar gashinta ta zagayo ta gefen wuyanta ta sauka akan kafaɗarta, hakan zai shaida maka kitso ne guda ɗaya tal a gashin nata. kallon gilashin windon take tana ganin yacca sauran ruwan sama ke sauka akansa. sam ba haka taso ba, ba haka taso lamarin ya tafi ba, sai da ta rufe ido ta buɗe sannan tace. "ba haka muka tsara ba, ba shirin da muka yi ba kenan. abunda muka tsara shine Turaki zai mutu a wannan ranar kuma a wannan lokacin cikin wannan dajin, lissafin da mukayi kenan, mun lissafa tarihinsa zai shuɗe ne cikin ƙanƙanan lokaci, zamu goge hotonsa da sunansa da duk wani abu daya dangance shi daga wannan zuciyoyin guda biyu...to amma me yasa komai ya rushe?, lissafin da mukai ya hargitse?". da shi take magana, saurayin dake zaune akan kujera yana fuskantarta, fari ne shima, me kaurin jiki, me siririn saje. shekarunsa ba wasu masu yawa bane, ƙananun kaya ne jikinsa blue jeans and red t-shirt long slip, sai facing cap baƙa daya saka. tarin gashin girarsa ya kusa haɗewa, kallonta kawai yake tunda ta tsaya a gaban windon, har zuwa yanzu da take magana da shi. "kina nufin laifina ne kenan?". a zafafe ta juyo ta fuskance shi tana ɗage hular rigar sanyin ta koma baya ne. "ƙwarai laifinka ne, idan da ace ba lusaran mutane
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243