Skip to content
NovelPress

Hausa Novels

Chapter 30

Chapter 30

Lullubin Biri Book 1 Complete Hausa Novel 1,216 words 0 views Progress saved
Download Book

karatu a gidan nan, ba ke ɗaya bace akwai wata sabuwar ƴar aiki da za'a kawo anjima za kuci gaba da aiki tare. bana son fitina Halima, bana son kuskure, ki kula da hakan. karatun boko da arabiya zai ke yi muku. ki tsaya ki maida hankali, domin akwai aikin da nake so kiyi min, aiki ne na masu ilimin boko, idan kin mayar da hankali, idan har kinyi nasarar samunsa Halima za ki sha mamakin yarda zan mayar da ke, duniyarki zata sauya, za ki zama abar kwantance, bayanki zai zama tarihi, idan kuma akasin hakan, tabbas ina mai tausaya miki da asara mafi girma da za kiyi a rayuwarki". Fillo so ta ke ta ɗago ta kalleta amma ta kasa, jan yatsunta kawai ta ke. "ungo wannan". sai a sannan ta ɗago tasa hannu biyu ta karɓi takardun. "ki adana su, zuwa ƙarfe biyar na yamma akwai wani zaizo ya karɓa, baƙi ne dogo yana da ƙasumba...ba shi kawai nace kiyi, kije masa da fuskar mutumcinki Halima...nasan kin gane lissafina". Kan Fillo a ƙasa tace,"tom Hajiya". "bani lafayata fara". Fillo ta miƙe ta ɗauko ta kawo mata. ta cikin mudubi Hajiya Madina ke ta kallonta, zuciyarta na me jin so da tausayin yarinyar. bata bar kallonta ta cikin madubin ba tace,"zo ki saka min wannam fil ɗin". Fillo ta matso zuwa bayanta ta karɓi fil ɗin a hannunta sannan ta saka mata kamar yanda taga Zaytuna nayi mata a duk sanda ta saka lafaya. ita ta ɗaukar mata jakarta suka fito a ɗakin, suna saukowa ta ke faɗa mata,"akwai key ɗin ɗayan bedroom na Hammansu acikin drower na mirrow, idan mun fita kije ki gyara masa. dan Allah ki gyara me kyau, ki kaɗe duk wata ƙura". "tom Maama, sai kun dawo Allah ya kiyaye hanya ya dawo daku lafiya" har bakin mota tai mata rakiya, Khalil ne zai ja motar dama, ta shiga tana tambayarsu, "ina Hammanku da Nihal?". Sameer yace,"Hamma ba lallai yasan mun fito ba, amma naga Nihal tayi wajensa da nake fitowa". "kira min shi". Sameer ya ɗauki waya ya kira shi, sai dai kamin ta kai ga yin magana ma yace gashi nan fitowa. Fillo kuwa tana komawa key ta ɗauka ta fito ta wuce ɓangaren Turaki, ɓangarensa dake jikin na Baffa. tana shiga parlon taji maganarsa na tashi a parlon. tayi saɗaf ta ɓoye ta wajen wani corrido, dan har ga Allah ita ba so ta ke suke haɗuwa ba saboda bata son wannan tsawar da yake sakar mata, yana sakata tana tunawa da moment ɗin da ba son tunawa da shi ta ke ba. kuma har zuwa wannan lokacin tana ƙyale shi ne kawai saboda darajar mahafiyarsa, banda haka da tuni ta nuna masa tafi ƙarfin ya dinga zaburar da ita dan kawai tana aiki ƙarƙashin arziƙinsu. shi da Nihal ne wadda taji tana roƙonsa akan dan Allah ya bawa Maama haƙuri. maganar ta ke tana karyewa saboda kukan dake fita daga bakinta. ta leƙo taga Turakin na tsaye ne ya harɗe hannayensa ta baya yana fuskantar gabas, kansa a sama kamar me tunani. ita kuma Nihal gwiwoyinta na zube a ƙasa a gabansa. kafin ya juyo gareta yaci gaba da magana bayan shirun da tayi. "arziƙi da talauci duka na Allah ne, idan Allah ya baka arziƙi ba yana nufin kafi kowa bane acikin bayinsa, kuma ba wai an baka dama ba ne dan ka wulaƙanta wanda bai da shi ba, shima idan Allah yaso yana iya ba shi nasa rabon, ko kuma ya ƙwace daga hannun kai da kake wulaƙanta talaka ya bawa wanda ka raina...but kin san me nake so ki fahimta?". Nihal ta ɗago da kanta tana kallonsa, sannan ta girgiza kanta alamar a'a. shi kuma yaci gaba,"Mama uwa ce da yau ba zata so ace ƴarta ta shiga gidan da zata wahala ba, wannan haka yake ga kowacce uwa...burin iyaye ne ace ƴaƴansu sunyi aure sun zauna a inda zasu ji daɗi, dan haka Maama bata hana alaƙarki da shi ba ne saboda yana talaka ba...". tun bai kai ga ƙarasawa ba ta katse maganarsa,"Allah Hammah tace makusarsa a wajenta shine talaucinsa, banda haka babu abinda zai hana ta barina mu'amala da shi...kuma ni wallahi Hammah ina sonsa, shi kaɗai zuciyata ke da muradin aure". ya kai hannu ya shafo wuyansa yana mai lumshe ido ya buɗe. "ba za'a hanaki aurensa ba dan kawai yana talaka, idan har na gari ne to ba shi da wani aibu a idon Baffa...saboda haka ki kwantar da hankalinki, ta shi muje". ta miƙe ya kama hannunta suka fita. Fillo ta sauke ajiyar zuciya, duk yacce ta ke tunanin mutumin nan ba haka yake ba. shi ɗin me kyau ne, kuma ta fahimci yana da kyan zuciya. contact 08024976578 [8/27, 20:15] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* *13* Hakimi wato Alhaji Babba zaune akan royal chair ɗin da ke tamfatsetsen parlon da ya gaji da tsaruwa da kayan alatu, duk wani kayan jin daɗi na mo re rayuwa an zuba a wannan parlon, haka idan har kai farin shiga ne a zuwa gidan, to tabbas zaka iya rantsewa ba'a ƙasar nigeria kake ba. farin rawani ne akansa, kana masa kallo ɗaya zaka san jinin sarauta ya gama ratsa shi. kamar yanda tarihi ya gabatar, an kafa Masarautar Gombe a shekarar 1804 a lokacin jihadin Fulani wanda Buba Yero mabiyin Usman ɗan Fodio ne. Buba Yero ya mai da Gombe (Abba) hedikwatarsa ​​domin yaƙin da ake yi da matsugunan Jukun na Pindiga da Kalam, daga nan kuma yayi ta kai hare-hare har zuwa Adamawa da ke gefen kogin Benue. a lokacin sarki Alhaji Bukar Dukku shi ke riƙe da sarautar garin gombe, bayan rasuwarsa ne kuma babban ɗansa Hashim Bukar Dukko ya karɓi sauratar, wanda ya riƙe sarautar tsawon shekaru masu yawa. Sarki Hashim Bukar ya ajiye ƴaƴa a ƙalla guda takwas kuma dukansu maza, kuma duk su takwas ɗin sun fito ne daga tsatson mace guda ɗaya Sarauniya Falmata, wacca a lokacinsu ne aka kafa tarihin sarkin daya zauna da mace ɗaya tal a karagar mulkinsa har rayuwarsa ta ƙare ba tare daya mallaki ko da ƙwarƙwara ba. cikin ƴaƴa takwas daya bari sune Adam, Ishaq, Lateef, Harun, Ibrahim, Yusuf, Isma'il, Shu'aib. akaf cikin yaran babu wanda ya samu kulawa me girma da gata daga wurin mahaifinsa irin babban ɗansa Adam, kasancewar tunda Sarauniya Falmata ta haife shi sai da ta shafe shekaru shida kafin ta ƙara samun wani cikin, lokacin har sun yanke tsammani da samun wani rabon, kuma daga haihuwar Yarima Ishaq shikenan ta shiga jero haihuwar ƴaƴa har sai da ta jera 8 gaba ɗaya. duk da ƙarancin shekaru da Yarima Adam ke da shi a wancan lokacin, hakan bai gaza fahimtar cewar shi wanene ba, ya san daga tsatson daya fito, domin a ko da yaushe mahaifinsa na faɗa masa cewar gaba da bayansa shi ɗan sarauta ne dan ko mahaifiyarsa ma ƴar sarki ce. bayan tarin ƙauna, soyayya, gata da kulawa wadda Yarima Adam ya samu a wurin mahaifinsa da mahaifiyarsa, sai kuma na ɓangaren al'umma. waɗanda suke ƙasƙan da kansu a gare shi matsayinsa na ɗa ɗaya tilo a wurin Mai Martaba da suke jin basu da tamkarsa. hakan kuma ya haifar da aƙida ta

Table of Contents

Chapters

243 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243