Chapter 161
Chapter 161
a tsakaninmu kuma ba zanyi ba, ka sakar min jikata kawai, yanda ake jinka ɗan gwal kai da matarka itama haka take ƴar gwal ba daga sama ta faɗo ba". ya ƙara cewa,"Dan Allah Dada...". Dada tayi ɗiff ta kashe wayarta, ta jefar da ita a ƙasa tai ɗakinta, Raudha tabi bayanta da kallo cike da takaici, yaushe aka siya mata wayar amma tana neman ta kashe mata ita. *Gombe, 11:00am.* a sanda suka gama wayar da Dada, Turaki ya baro office ɗinsa yana jin kansa duk ya cunkushe. Bello dake driving ɗin yace da shi,"karka sakawa kanka damuwa, komai zai warware insha'Allah". Turaki ya kallesa da jajayen idonsa cikin ƙaraji yace,"fisabillahi saboda mace sai in rasa kwanciyar hankalina, ta ko'ina ji nake babu daɗi, haba dan Allah". Bello ya sauke numfashi yace,"ba mace bace rashin kwanciyar hankalinka MT, kai ne ka jawa kanka matsalar duk da kake ciki, yanda kayi gaban kanka a auren nan dole ka fuskanci ƙalubale, in ace da izinin iyayenka kayi komai wallahi wannan matsalar ba zaka shigeta ba". "shiyasa nayi deciding rabuwa da ita ai tunda itama bata sona, but Maama da Mum sun hana, to ni zan haɗa har ita Ilham ɗin na sakesu, ba zan iya da wannan damuwar ba". ya faɗa daidai da sanda suka ƙaraso bakin gate, Bello ya bushe da dariya, kafin yayi magana tuni Turaki ya fice daga motar ya shige gida. yana shiga yayi kiciɓis da Boɗejo a compound tana ta masifa akan bai bi ta kan Ilham da bata da lafiya ba, ta tsayar da shi bai ko bi ta kanta ba yay wucewarsa side ɗin Hajiya Madina, kai tsaye upstais ya haye, yana zuwa yay knocking door, daga ciki Hajiya Madina ta ɗaga ido ta kalla bakin ƙofa kafin tace,"come in". ya murɗa handle ɗin ya shiga gabansa na faɗuwa, yana saka ƙafa suka haɗa ido, ba shiri ta ɗaure fuska kamar bata san shi ba, ta ɗaga masa hannu da cewa,"get back". ya marairaice,"please Maama i want to talk to you, dan Allah kiyi haƙuri akan laifin da ban san nayi miki ba". ta ɗauke idonta daga kansa tace,"nace ka fita ko". ya ƙarasa shigowa yana ƙoƙarin zube gwiwoyinsa a ƙasa, ganin hakan yasa ta miƙe zata bar masa ɗakin ba shiri ya rigata fita, ya fita yana riƙe kansa da yake jin kamar zai bar jikinsa. part ɗin Hajiya Ramla ya wuce, tana ganinsa ta ajiye cup ɗin dake hannunta tana tambayarsa,"Babana lafiya?". ta tambaya duk da tasan yana cikin matsala, amma yau ɗin tana ganin ba irin yanda ta saba ganinsa aciki ba, damuwar ta girmama. ya zauna akan kujera yana daɗa riƙe kansa ba tare da ya ce mata komai ba, ta baro dining area da sauri tazo ta zauna a kusa da shi, ta dafa kafaɗarsa tana cewa,"what is wrong with you Babana?, kai da Boɗejo ne?". ya ɗago ido kamar zai yi kuka yace,"Maama ce". "me ya haɗaka da Maaman?". ya kwantar da kansa a kafaɗarta yace,"almost 1week fa Mum ko gaisuwana bata amsawa, ban san laifin da nayi mata ba wallahi, and taƙi bani damar ma da zan bata haƙuri, na mata sending apology through text message and letter duk tayi ignoring ɗina, kuma ina so nayi magana da ita Mum". Hajiya Ramla na kallonsa da tsananin tausayi tace,"and duk ina ina hakan ta faru?". ya kama hannunta cikin sanyin murya yace,"kinyi busy da yawa a office Mum, kuma kinga Baffa ya hanani zaman gidan nan". ta sauke numfashi tace,"tashi muje". yace,"Mum ko munje fa ba zata saurareni ba, korana take yi". ta kama hannunsa kawai suka fita zuwa side ɗin Hajiya Madina, suna shiga parlo tana saukowa daga upstairs, taiwa Turaki kallo ɗaya ta ɗauke kai ta wuce kan kujera ta zauna, yabi bayan Mum suka ƙarasa ya zauna kusa da ƙafafun Hajiya Madina. Hajiya Ramla tace,"ina bayar da haƙuri a madadinsa Madam". Hajiya Madina ta kalleta tace,"bai faɗa miki laifinsa ba?". yay karaf yace,"ki faɗa min Maama zan gyara". nan da nan ta fara masifa tana cewa da Hajiya Ramla,"yaron nan saboda baida mutunci yana so ya mayar damu ƙanan mutane yaje dubai ince idan sun tashi dawowa ya taho da trollys amma ya kawo min guda goma sha biyu kacal, ba wannan ba ma!, nace ya haɗo lefe but sai ya turawa Zaytuna 1ML wai ta siya abin da taga ya dace, wato gamu faqararru da miliyan ɗaya zamu haɗa lefe ko?, in tambayeka ma! zatonka Fillo ƴar aiki daka sani a baya zaka kaiwa lefe da zaka kashe 1ML kacal?, to in haka ƙwaƙwalwarka ke faɗa maka ta yaudareka, Fillo ƴar aiki daban Fillon da zaka kaiwa lefe daban, in ka manta ka tuna gidan da kaje kayi gaisuwar mahaifinta, ka tuna irin mutanen da ka samu, ka san da cewa kenan tafi ƙarfin naira miliyan ɗayanka, Fillon yanzu ƴar gata ce gaba da baya kuma ƴar gidan manyan mutane, beside wallahi ko da ace Fillo ta nan a yanda ka santa tun farko baka isa ka kawo min lefenta na miliyan ɗaya na karɓa ba, kai ka san da cewa taimakonka da tayi tafi ƙarfin dukka arziƙin ubanka har da naka. to make it short, kaje ka sami ubanka Alƙali Dikko ka tambayesa lefen nawa suka haɗawa ƴarsu daga nan sai kayi abin da ka san zai ɗaga mutuncinmu ba wanda zai ja mutuncinmu ya zube ba, dan mu ba marowata ba ne". kansa a ƙasa yace,"Maama kiyi haƙuri amma wallahi bani na tura kuɗin ba, time ɗin account ɗina ya sami matsala kuma kaina ya ɗau caji da damuwar Boɗejo shine nasa Bello ya tura mata, kuma wallahi sai da nayi masa magana yace ai hakan ya isa wai almubazzaranci babu kyau". Hajiya Madina ta zare ido tana doka masa tsawa tace,"rufe min baki shashasha, shi Bellon da zai haɗa nasa lefen da 1ML ya haɗa da har ya mayar da kai ɗan iska, me yasa baka tuna masa check ɗin da na basa yaje ya haɗa nasa lefen ba?, ko kuma baka faɗa masa gidan da kaje ka sami Fillo a yanzu ba?, to wallahi wallahi ba zan kai iyaka akwatu sha biyu ba, kuma ba zan kai lefen miliyan ɗaya ba, tashi ka bar min parlo". ya ɗago ya kalleta kamar zai yi kuka, ya marairace yana roƙonta akan tayi haƙuri. tace,"fitar min a parlo tun ina ganinka da gashin ido, ai ba iyakarta kenan ba, nace kaje ka gano lafiyar matarka kaƙi zuwa yau kwana hamsin da wani abu, wanne kallo kake so mutanen nan suyi mana?, amma na lura da hakan bai dame ka ba saboda kana tare da zaɓin ubanka acikin gidanka ko?, kai kasan maganganu marasa daɗin da Boɗejo tazo ta yiwa mahaifiyarka yanzu kuwa?, kuma duk akan Ilham, me ta-ke nufi da mu?, auren nan muma da muke iyayenka muka haƙura da yanda kaje kayi gaban kanka balle ita, ta bar yarinya ta tare a ɗakinta amma ta hana kowa kwanciyar hankali, ba'a zama da kishiya ita uwar yarinyar ta zauna da kishiyoyi, haba dan Allah tun yaushe ake abu ɗaya, abu mitsitsi yaƙi ci yaƙi cinyewa, comon tariyar da za'ai lokaci ɗaya a wuce wurin ta hana rawar gaban hantsi, tabi tasa mahaifinka ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243