Chapter 237
Chapter 237
Manzon Allah ya karɓi baƙuncinki, Allah yasa mutuwa ta zamto hutu a gareki, Allah ya lulluɓeki da rahamarsa da gafarsa, haƙiƙa ba ki yi min komai ba, na yafe miki duniya da lahira, abin da kika bari Allah ya kula miki da su, Allah ya basu haƙuri da juriyar rashinki. sai mun taho muma". aka shigo da Turaki, ya zauna shi ma agaban gawar, yana jin sautuka na shiga kunnensa, sai dai a lokacin babu abin da ƙwaƙwalwarsa ke iya ganewa, har yanzu ya kasa karɓar mutuwar matarsa, ganin komai yake yi tamkar shirin wasa, tamkar shirin film aka haɗa don kawai a girgiza shi, don kawai a gwada irin ƙarfin soyayyar da yake yiwa Fulaninsa. "Muhammad ka yi mata adu'a, kuyi sallama Muhammad kaji". tun daren jiya, tun lokacin da labarin mutuwar matarsa ta riske shi, da zaman kwanan da yay agaban gawar, zuwa wayewar garin yau da ya ƙara tabbatar da ya rasata, sai a yanzu da ake cewa yay mata adu'a suyi sallama ya ji idonsa ya cika, saɓanin jiya da yake a bushe, har yana jin kamar ba zai taɓa zubar da ruwa ba, amma a yanzu tarin ruwan da ya cika a idonsa ba ya jin zai iya dakatar da su, saboda haka sai kawai ya kifa kansa akan ƙirjin gawar, hawayen ya ƙwace, kukan ya kubce, ya shiga rero kuka tamkar ƙaramin yaro, yana kukan jikinsa na girgizawa kamar yanda zuciyarsa ke yi. adu'ar da ake ta cewa yayi ya kasa yi, sai da ƙyar aka iya raba shi da jikin gawar, aka miƙar da shi aka riƙe shi, yana kallo aka ɗauki gawar aka fita da ita, da sauri ya bi bayan su, ya tarar da su suna saka gawar a cikin makara. abinda ya saka shi ƙara rikicewa, sai ya tsinci kansa da yiwa Allah godiya da ƴaƴansa ba su tsinci ganin wannan lokacin ba. ƙarfe sha ɗaya dai-dai aka yiwa Fillo sallah, a cikin ƙaton compound ɗin gidan Alƙali Dikko, bayan gama sallar gawar aka ɗauƙi makarar aka fita da ita daga gidan, Turaki na sahun gaba, ƙafafunsa ke jansa ba shi ne yake tafiyar da su ba, yayin da hannunsa guda ɗaya yake cikin na Bello ya riƙe shi da kyau, saboda gudun faɗuwarsa. a lokacin da aka isa maƙabartar, Hamid da su Yusuf da Baffa su ne suka fito da gawar daga cikin makara, Bello ya kama hannun Turaki ya kama kan gawar sannan aka sata a cikin ramin ƙabarinta, yana kallo ana fuskantar da fuskarta zuwa ɓarin gabas, yana kallo aka ɗauko fasassun tukwane aka jejjera a saman gawar, kafin daga bisani yaga ana zuba ƙasa ana toshe ko'ina, yana jin muryoyin da ba zai iya tantacewa ba na faɗin a toshe kowacce ƙofa, yana kallo bayan an gama rufe gawar ruf da ƙasa aka yayyafa ruwa a samanta, sannan aka ɗauko allon shaida aka dasa a wajen kan, allon da yake iya karantawa, komai yana faruwa kamar dai sati biyu da suka wuce. sunan da ke jikin Allon ɓaro ɓaro, sunan matarsa, sunan abar ƙaunarsa, wannan Fulanin tasa, wannan Fulanin da yake jin ba zai iya rayuwa ba a duk san da babu ita a tare da shi, yau shi ne a gaban ƙabarinta, da shi aka kawota, yana kallo aka sakata cikin rami bai iya hanawa ba, bai iya buɗar baki yace a'a ba, bai iya motsawa ba balle ya riƙe gawar. *Marigayiya Halima Muhammad Barkinɗo(Fulani), Allah ya jiƙanki da rahamarsa, 03/10/2022.* kamar hakan allon ke ɗauke da rubutun cikin manyan baƙi, ji yake kamar ya fincike allon ya jefar. a hankali ya dawo da tunaninsa ɓangaren da yaji ana doguwar adu'a, sai ya fara kallon kowa ɗaya bayan ɗaya, kowa a tsugune yake ya ɗaga hannunsa, sannan Dr Yusuf da Hakim da Khaleel idanuwan suna hawaye, sai Baffa da Daddy(Baban su Dr Yusuf) fuskarsu fayau, sai ya mayar da kallonsa kan ƙabarin, shi ma ya ɗaga nasa hannun, ya shigo jero tarin adu'a wa ruhin matarsa, yi yake yi yana maimaitawa, har zuwa lokacin da yaji takun tafiya alamu na ƙafafu sun fara barin wajen. yana ji mutanen da ke kusa da shi suna tashi, kuma kafin kowa ya tafi sai an zo an dafa kafaɗarsa ance masa,"Allah ya jiƙanta, Allah ya bada haƙuri". da haka da haka sai da ya tsinci babu kowa a kusa da shi, sai shi kaɗai da yake zaune yana kallon ƙabarin ya kasa sauke hannunsa, har sai da Bello ya zo ya dafa shi yace,"kayi haƙuri ka tashi mu tafi". sai yaji Khaleel ma na ce masa,"Hammah kayi haƙuri". kawai sai ya saki kuka me ƙarfin sauti, ya kai hannunsa ya ɗora akan ƙabarin, a hankali yace,"insha'Allahu zan yi duk abin da kika ce, zan kula da yaranmu, zan ba su tarbiyya, zan saka su a makarantar da kika faɗa, ba zan bari su yi kuka ba, ba zan sa suyi kuka ba, ba zan bari su shiga cikin ƙunci ba, ba zan bar su suyi maraici ba, zan riƙe amanar da kika bar min, nayi miki alƙawari, zan kuma cika miki shi tabbas. don Allah ki yafe min da duk laifin da nayi miki, don Allah Fulani Nah, ki ce ina gaida Maama". Bello da Khalil suka kama shi ya miƙe. suka riƙe shi suka fara tafiya domin barin cikin maƙabartar, sai da suka zo bakin ƙofar fita ya juyo yana daɗa hango kabarin, yana faɗin,"zan dinga zuwa kullum ina gaishe ki, zan dinga zuwa kullum ina yi miki adu'a, idan Aayan ya girma zan dinƙa kawo miki shi kina saka masa albarka, na gode Fulani Nah, sai anjima kinji ƴar aljannah". komawar su gida suka tarar da ɗumin dandazon jama'a acikin rumfunan tanfol ɗin da aka yi kusan guda biyar, kai tsaye cikin gidan ya wuce bai tsaya a waje ba, yana shiga ya fara karɓar gaisuwar ta'aziyya daga mutane, ba wani ganin su yake yi ba, don ba ya gani da kyau. ya ratsa ta cikin falon Mum ya haye sama, daga ƙofar ɗakin nata ya tsaya yana kallon Nihal da Ilham da ke goye da marayun jariransa, sai ya shiga ciki ya kunto yaran daga bayansu da kansa, ya fito ya bar ɗakin, ya kuma ratsa mutanen dake parlon ƙasa ya fice daga sashin gaba ɗaya. kai tsaye ɓangarensa ya nufa, ya buɗe ɗakinsa ya shiga, ya zauna akan gado tare da jinginar da kansa jikin gadon, ya kwantar da macen a ƙirjinsa, namijin kuma ya ɗora shi a kan ƙafafunsa. "your mum is no longer with us, she is gone and she is never coming back, death have separated us, she wants us to pray often for her, tun kafin ta haife ku tace Allah yaywa rayuwarku albarka, kuma na san ta biku, Allah ya raya min ku. Allah ya bamu haƙurin rashin da muka yi, ina yi mana ta'aziyya". ya faɗa ya ƙara maimaitawa kamar yaran suna fahimtar me yake cewa, kafin a hankali ya rufe idonsa. in da a wannan lokacin Ilham ta shigo hannunta riƙe da tea flask, jikinta duk a sanyaye sai idanuwanta da suka yi jawur. ta ƙarasa ta zauna a bedside drower tana kallonsa, tana kallon yanda hawaye ke fitowa daga idonsa yana bin kumatunsa, yayin da bakinsa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243