Chapter 149
Chapter 149
gaisa, me pineapple ɗin yace da shi,"ta nawa za'a zuba yallaɓai?". Hamid yace,"sako guda goma, kar a yanka kowacce". mutumin ya juya yaje ya zubo pineapple ɗin a cikin leda har guda biyar ya dawo, Hamid ya buɗe masa booth ya saka a ciki, kwata-kwata ba ita yay niyyar siya ba kawai dan mutumin ya rigada ya saka rai ne. mutumin ya dawo yana goge hannunsa da durster yace,"ranka ya daɗe an gama sakawa". Hamid ya juya bayan motar ya kalla mahaifinsa daga kishingiɗe kamar me bacci amma ya san ba bacci yake ba, sannan ya juyo ya ƙara cewa da me pineapple ɗin,"bamu apple". cikin sauri yaje ya dawo. Hamid yace,"nawa ne kuɗin?". yace,"ka bada dubu takwas". Hamid yasa hannu a aljihu ya ɗauko ya basa, yana shirin barin waje ya tsayar da shi da cewan,"yauwa kaga dan Allah tambaya nake dama". mutumin yace,"to Allah yasa na sani". Hamid yace,"gidan Alƙali Dukko nake nema". mutumin yace,"ohh gidan uban marayu zaka ce". sannan ya shiga yiwa Hamid kwatance yanda zai gane, Hamid yay masa godiya sannan yaja motar ya bar wajen bayan ya ɗau apple ɗaya ya miƙawa Mahaifin nasa yana roƙonsa akan ya daure yaci ko ya ne. tafiya kaɗan ta kawo su ƙofar gidan Alƙali Dukko, dai-dai lokacin da motar Maama ta shiga gidan, Hamid ya fito yana ƙarewa girman gidan kallo sannan ya ƙarasa yay knocking gate. me gadi ya buɗe ƙofar ya fito suka shiga gaisawa da Hamid, bayan sun gama gaisawa Hamid ke tambayarsa dan Allah ko akwai Hajiya Rabi anan gidan. Me gadi yace,"a'a wallah babu Rabi, wani yay maka kwatance da nan ɗinne?". Hamid yace,"ehh tou, daga can gidan sarki aka kwatanto mana nan ɗin, da tana aiki acan sai akace ta dawo nan gidan". Me gadi yace,"ohh ai nan ɗin main gate ne na gidan, da yake ɓangaren ma'aikatan gidan daban, daka zagaya ta baya zaka ga gate ɗin irin wannan ne". Hamid yay masa godiya sannan ya koma mota, yana zagawa ɗaya gate ɗin ya faɗawa me gadin sunan Kaka na ainihi shima yace gaskiya bai san wannan sunan ba, sai dai bari ya kira masa shugabar ma'aikatan. ba jimawa Yami tazo wajen, tana kallon Hamid tace,"kar dai jikanmu ne kai". ta faɗa saboda tsananin kama da Fullo da ta gani a fuskarsa kamar an tsaga kara. yace,"ehh to indai wadda nake nema ɗin ita kike nufi to ni jikanta ne". Yami na murmushi tace,"Allah sarki, ai da yake ma ta kwana biyu da tashi daga nan ɗin, amma bari sai muje yanzu na raka ka gidan da suka koma dake ba anan unguwar ba ne". Hamid ya jira Yami ta koma ta sanyo mayafi sannan suka tafi, ita bata ma lura da wanda ke bayan motar ba saboda tana nufar shiga baya Hamid yace da ita ta dawo gaba. sunyi tafiya me nisa kamin su isa gidansu Fullo, motar tasu ta shigo layin a sanda Fullo ke fita daga layin tana sanye da uniform da kuma niƙab zata wuce islamiya. ƙofar gate ɗin a buɗe take dan haka bata tsaya knocking ba, Yami ta shiga dan sanarwa da Kaka, a parlo ta sami Kaka ita ɗaya tana kallo, suna gaisawa tace da ita,"taso ƙawata, taso taso". Kaka na bin ta da kallo tace,"lafiya dai Ƙawata?". Yami tace,"lafiya lau Ƙawata, ke dai fito da sauri kiga abin mamaki abin farin ciki". cikin azama Kaka ta miƙe akan kujerar ta ɗauka hijab ɗin Ummi dake kan kujera tabi bayan Yami da sauri hankalinta duk ba'a kwance ba dan taga Yami a hargitse take. Fitowarsu bakin gate Kaka tayi saurin dafe ƙirji asanda tayi tozali da Hamid jingine a jikin mota. "me idanuna suke gane min?". wani farin ciki da jin daɗi suka mamaye Hamid ya baro jikin motar yana zuwa ya rungume Kaka. ta ɗan ture shi a jikinta tana faɗin,"Hamid kaine ka zama mutum haka?, dama zan ƙara sanyaka a idanuwa na?, Hamid dama kana raye baka taɓa nemana ba?". Hamid ya sauke numfashi yace,"kiyi haƙuri Kaka Allah ne bai nufa ba, amma wallahi kina raina, ta ya zan manta dake bayan kece silar zuwan mahaifiyata duniya". Kaka ta share hawayen farin ciki tana bin motar da kallo kamin tace,"to ya akai kazo nan Hamid?, kar dai wani abu ne ya faru mara daɗi?, wannan motar kuma ta waye?". Hamid yace,"Kaka ai ban manta da kina aiki a gidan sarki ba, na faɗa miki tsawon shekarun nan Allah ne kawai bai nufa ba sai yanzun". tace,"dan dai kaga bana tare da abu me muhimmanci a wurinka ne shisa ka kasa nemana". yaga tana kallonsa tana ƙara bin motar da kallo yace,"mota ta ce, ba zai yiwu mu shiga daga cikin gidan ba ne?". Kaka na kallonsa tace,"zai yiwu mana Hamid, ai shiga cikin gida ma dole, gidanku fa kazo taho muje". ta faɗa tana juyawa ya dakatar da ita,"Kaka mota ba zata shiga ciki ba ne?". tace,"to sai dai ka duba tunda mu ba mota garemu ba, tun zuwanmu dai ta wannan ƴar ƙofa muke shiga". ya ƙarasa ya duba yaga gate din ba me zugewa ba ne, hakan yasa yace mata,"Kaka to bari na fito da shi". tace,"waye?". yay ɗan jimm damuwa na bayyana a fuskarsa sannan yace,"tare da Abba muke, ba zai iya tafiya ba sai na taimaka masa". idanun Kaka a waje tace,"kana nufin Babanka Hayyo?". ya ɗaga mata kai,"ehh Kaka". da mamaki sosai tace,"to me ya sami ƙafar tasa da ba zai iya takawa ba, ko wani mulkakken ya zama?". ya sauke numfashi yace,"jarabawar ubangiji". Kaka ta taɓe baki tace,"Alhaki dai yake bibiyarsa". bai ce komai ba ya ƙarasa mota ya buɗe booth ya ɗauko wheelchair sannan ya buɗe bayan ya taimakawa Hayyo ya fito ya ɗorasa akan kujerar, tun fito da shi Kaka tayi masa kallo ɗaya taji mugun tsoro ya kamata kamin bala'in tausayinsa ya biyo baya, indai gani take yi da kyau ya rame kamar me cutar ƙanjamau, mutumin da yake jayent son kowa ƙin wanda ya rasa, mutumin da bama a gane girmansa ko ada amma yanzu girma ya bayyana ajikinsa sosai kace me shekaru ɗari. Hamid ya turo shi suka ƙaraso inda Kaka ke tsaye cike da tsoron duniya, hoton abubuwan da suka faru a baya suna ta haska mata a ido, ita dai banda Hamid ya faɗa mata yace Abbansa sai ta rantse tace ƙarya ne ba shi bane, dan gaba ɗaya ya fita daga kamanninsa tsabar wahala, kamar ba wannan ƙaƙƙarfan namijin da ke zage dukkan ƙarfinsa ya zane mata ƴarta ba. ta girgiza kai tana ƙara jin tsoro na al'amarin sakayyar wanda aka zalunta, a hankali tace da shi,"Hayyo". ya ɗago da wuyansa da ƙyar wanda ya laƙwashe. ya kalleta ya buɗe baki yace,"nannnnaaammm Daddddda". ya faɗa cikin ƙinƙinar da sai kayi da gaske zaka gane, kuma cikin murya kamar ta masu koyon magana. kawai sai Kaka ta fashe da kuka sosai tana ambaton,"innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". ta ƙara kallonsa tace,"Hayyo kai ne ka koma haka?". ta tambayesa tana tuna zaƙin maganarsa ada, wanda daɗin amon muryarsa na ɗaya daga cikin abin da yake jan hankalin mata garesa, dan ƙarya ne Hayyo yayi magana kana wajen baka ce kaji daɗin muryarsa ba. hawaye ya sakko a idonsa yace,"Kakkkkaaa dddddaaa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243