Chapter 235
Chapter 235
za su ta so ba tare da sun san wannan ɗumin jikin na uwa ba, za su taso babu wannan kulawa da soyayyar da yake a wurin uwa ba kaɗai. "bismillahir-Rahmanirrahim, bring the knife". haka taji likitan da ke tsaye akanta ya faɗa, kuma bayan wannan zata iya cewa jinta ya ɗauke na ɗan wani lokaci kafin ya dawo. a san da aka fara aikin, idanun Fillo a jiƙe suke sharkaf da hawaye, hawayen da ya hanata ganin komai sosai. a wannan lokacin dukkan tunaninta ya gama hargitsiwa da kowanne motsin dake faruwa a cikin ɗakin tiyatar, tana jin yacca sautin zuciyarta ke bugawa da ƙarfi acikin kunnenta. lokaci ɗaya taji sautin wata ƙara ta fita a jikinta, sautin da ta tabbatar na yanka ne, cikinta ake yankawa!, sai taji zafin ciwon da take ta daurewa ya ƙaru, zafinsa na ƙaruwa sosai da sosai, zafin da har ta kai ga kasa tantance cikinta ake yankawa ko kuma ruhinta ake zarewa. hawaye ya bi ta gefen fuskarta, ta ji kamar ta ɗago tasa hannu ta danne wajen da aka yanka ko zata sami sassauci, sai dai babu abin da zata iya, bata da ƙarfin motsi ko kaɗan, tamkar matacciya take. tsawon lokaci babu wani abu dake wanzuwa a cikin ɗakin tiyatar sai fafutukar da likitoci ke yi wajen ciro yaran daga cikin mahaifiyar su. kunnuwan Fillo sun ji lokacin da aka ciro Baby na farko, Babyn da taji Dr na cewa da nurses su yi ƙoƙarin su wajen ganin yayi kuka, sai taji wani farin ciki ya ratsata, farin cikin da taji tamkar an yi mata bushara da gidan aljannah. so take taga yaron da aka ciro, don haka cikin ƙarfin hali da dauriya ta karkata kanta gefe domin kallon jaririn da cibiyarsa kaɗai take iya hangowa, kuma a san da nurse ɗin ke juyowa zuwa sashinta, lokacin sabuwar azaba ta ƙara ratsata, tayi saurin rumtse ido tana ambaton innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. ambaton nata ya haɗe tare da kukan Baby na biyu da aka ciro, kukan da ya cika ɗakin gaba ɗaya, kukan da zata ce kamar ta tsinci sunan da take ta muradin ta haife su taji sun kirata da shi, Ummina!. a san da Babyn yay shiru sai taji jikinta ya tsaya a lokaci ɗaya, yay sanyi ƙalau, numfashinta mai nauyi na cigaba da fita, yayin da zuciyarta ke bugawa a hankali, hakan yasa ta fahimci cewa hargitsin azabar ciwon da take sha yazo ƙarshe, ƴaƴa biyun da ke cikinta an fito da su duniya, ta zama uwa, dukkan fatanta da burinta ya gama cika, atleast ta samu masu yi mata adu'a a kowacce daƙiƙa a yayin da komai ya riga ya kai ƙarshe. ta riga ta san abin da yake cikinta tuntuni, macece da na namiji ne ba sai an faɗa mata ba a yanzu. tana jin yacca motsin yaran da ake ta aikin gyarawa ke mutsutsu acikin kunnenta, tana jin yanda zuciyarta ke bugawa da son su da ƙaunar su, sannan a hankali ta fara jin komai na zamewa daga cikin kanta yana barin ƙwaƙwalwarta, cikin ranta tana adu'ar,_"Ya Rahman if you decide to take my soul at this time, i beg you Allah to give my husband and my childrens the strength to bear it, Allah kaji tausayin ƴaƴana, ka tausayawa maraicin su ka basu tamkar Hajiya Madina a matsayin wacca zata kula da su"._ da ga wannan furucin dake cikin ranta, sai kuma bakinta ya shiga maimaito kalmar shahadar da taji tana wanzuwa acikin kanta, hakan yasa idanuwan likitocin da ke ɗakin ya manne akanta, akan murfin idonta da ke barin kan twins ɗin da ake nuna mata amma ta kasa kallon su. kuma wucewar sakanni biyar komai ya zama ya ƙare, komai ɗin dake rayuwar Fillo, shikenan wa'adin da ubangiji ya ɗiba mata ya cika, alƙalaminta ya riga ya bushe, ubangiji yayi hukuncinsa. bayan wasu mintuna Turaki da ke tsugune a ƙofar ɗakin tiyatar yaji an buɗe ƙofar, bai motsa ba dan bai san ta yanda zai motsa ba, yana so dai ya buɗe idonsa yaga abin da ke wanzuwa, so yake ya buɗe ido ko ya samu zuciyarsa ta daina bugawar da take yi. acikin wata fargaba da ke tare da shi yaji an ɗora hannu akan kafaɗar sa, sai ya ɗan buɗe ido kaɗan yana kallon nurses guda biyun da ke tsaye akansa tare da likita, ba zai ce ga lokacin da ya miƙe ba, ya dai tsince shi ne tsaye akan ƙafafunsa yana kallon jariran dake hannun nurses ɗin, bai san me yake ji a zuciyarsa ba, amma dai ya san bakinsa ya kasa rufuwa, ya miƙa hannu ya fara karɓar namijin, sakanni uku yana kallon yaron me kama da shi sak kafin ya miƙa shi ga Dr Yusuf da ke tsaye a kusa da shi, sannan ya daɗa karɓar macen da ita ce ƙarama, kuma a lokacin da ya ɗora idonsa akanta a lokacin Doctor ɗin yace da shi,"I am very sorry to tell you that your wife is no more, Allah yayi mata cikawa, ina yi maka ta'aziyya Allah yaji ƙanta da rahamarsa". a maimakon rufewar da idanun Turaki ke shirin yi sai yaji sun maƙale akan jaririyar da ke kuka a hankali, jaririyar da yake hasko fuskar mahaifiyarta a fuskarta. sai kawai yaji furucin likitan na maimaituwa acikin kansa,_"your wife is no more"._ sai yaji kalaman likitan suna ƙara tafiya a hankali, yayin da yake ji suna barin cikin kunnensa har zuwa cikin kansa da zuciyarsa in da suka samu masauki, don ya kasa gane ta yadda zai karɓe su balle har su yi ma'ana a cikin ƙwaƙwalwarsa. Fulani ta mutu?, yana nufin Fulaninsa ta mutu, Fulani ta mutu!, Fulanin da suka yini tare yau, to ta ya zai yarda da hakan?. sai kawai ya kutsa ta tsakiyar mutanen da ke gabansa ya faɗa cikin tiyata room ɗin still yana riƙe da jaririyar, yana shiga ya hangota an rufeta, rufewa tana nufin lulluɓewa har fuska, irin lulluɓewar da ya gani akan Maamansa sati biyu da suka wuce, irin lulluɓewar da yasan mamaci kawai ake yiwa, irin lulluɓin nan da ake yiwa gawa kaɗai. Turaki ya tsaya cak tamkar mutum mutumi, idonsa na kallon gawar, yaji guiwoyinsa sun yi sanyi ƙalau, irin sanyin da suka kasa cigaba da ɗaukarsa, don haka sai ya nemi bango ya dafe gudun kar ya faɗi jaririyar da ke hannunsa ta cutu, haka ya dinƙa jan ƙafa yana dafe da bangon har ya ƙarasa gaban gawar, a lokacin ƙafafunsa suka kasa ci gaba da ɗaukarsa ya zube a wajen, ya damƙi mayafin da aka lulluɓeta da shi, a hankali ya shiga adu'ar. "Allah ba yanzu ba, Allah ko don waɗannan jariran, zuwansu duniyar kenan Allah, Allah ka sauya musu wannan ƙaddara ya zama ka ɗauke ni ba mahaifiyar su ba, sun yi kaɗan da irin wannan jarabawar, Allah don Allah ka dawo da Fulani ka ɗauke ni, Allah kar kasa Fulani ta tafi ta barmu, Allah ka tausaya mana ba zamu iya ɗauka ba,Allah ka tausaya mana don masoyinka fiyayyan halitta, Allah don son da kake yiwa Annabi Muhammadu SAW". sai ya kalli jaririyar da kukanta ya fara yawa yace,"Allah'n mu ka tausaya mana, don Allah Allah ka juya wannan ƙaddarar, ka ganta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243