Chapter 198
Chapter 198
zo ya tare masa, da ma akwai shi da siyan faɗan da ba nasa ba, har kuɗi yake bayarwa ya siya faɗa, akan siyan faɗa har abincinsa break ɗinsa yana bayarwa. shikenan daga ranar su ka ƙulla abota da Bello, kuma daga ranar shi ma ya zama me ƙarfi ya ko yi faɗa da ƙiriniya, sai da ta kai ta kawo ya koma kamar wanda ke aiki da battery, kuma duk saboda zama da Bello, Maama tayi ta tofa masa lahaula. duk friday Bello a gidansu yake yini, kuma shi Bello babu abinda ya iya sai shegiyar fitina da dambe, sai suje can field Bello yay ta koya masa yanda zai ƙwaci kansa in wani yafi ƙarfinsa, har ranar ya gwada masa yanda zai shaƙe wuyan mutum, Bello ya shaƙe masa wuya har sai da numfashinsa ya kusa ɗaukewa, kuma kamar wani Malaminsa ko Babansa Bello yace yaje yay ta practical, tun da yana da ƙanne yay ta gwadawa akansu, ai kuwa da daddare ya shaƙi wuyan Khalil zai yi assignment ɗin da Bello ya ba shi, Baffa kuwa ya tarfa shi yay masa ɗan banzan duka ya kulle shi a store, aciki ma ya kwana dan sai da safe Maama ta sato key ta buɗe shi, kuma a washe garin da suka haɗu a islamiyya ya faɗawa Bello, sai yace zai koya masa yanda ake ɓalle ƙofa in an kulle mutum, ko kuma da an kaishi ɗaki za'a kulle ya fice a sukwance tun kafin a rufe, har haura katanga duk tsayinta sai da Bello ya koya masa, da yacca zai ɗauko key ɗin mota ya fice daga gidan, har yana ba shi labarin wai shi a gidansu sai da ya fasa glass ɗin mota har biyu, Abbansa yazo dukansa ya ɗafe wuyansa yaƙi sakinsa. watarana sun tashi a school yasa driver ya wuce da shi gidan su Bello, ya koya masa duk kalar yanda zai tseratar da kansa, wata rana kuwa yaywa Granny laifi zata kullesa a ɗakinta yay sufa yabi ta ƙarƙashinta, garin kamo shi ta zame ta faɗi, Anty Sa'adah ta kama shi ta murɗe masa kunne har sai da ya saki fitsari a wando. yay shiru yace,"kin san Bello har cewa yay inyi kashi a fo sai in dangwala in rubuta sunana ajikin bangon ɗakin Baffa, in dai yake ni to baya so na...ai ko in faɗa miki ina yin haka washegari Baffa ya kaini Europe wurin Granny". Fillo ta dinƙa dariya har da riƙe ciki, shi ma ya shiga tayata dariyar kamar yanda take yi. ta kama hannunsa ta ɗora a saman ƙirjinta tana rufe ido, yayinda dariyarta ke juyewa zuwa sanyayyan murmushi, a yanzu ta ƙara yarda cewa Turaki yana sonta har cikin zuciyarsa, kuma ba ta tunanin akwai abinda zai canja hakan, tana ganin zallar soyayyarta fal a cikin idanunsa a duk sanda ya kalleta, duk da har yanzu da bakinsa zuwa kunnenta dai bai furta ma ta kalmar i love you ba tun bacin wadda ta gani a takarda. acikin kwanaki ukun nan kacal tana cikin wata duniya ne ta daban me cike tarin kulawarsa da tarairayarsa, ta daina jin tsoronsa dan ya bi ya kulle duk wata hanyar tsoronsa a gareta, ta saba da shi yanzu fiye da tunanin kanta ma, ta saba da hirarsa da yake cikin yi ma ta ko da yana cikin aiki ne, kamar yanda ta saba da jikinsa, dan duk wani motsi nasa cikin taɓata yake yi, ko akan laptop yake to hannunsa ɗaya na cikin nata, ko kuma ya ɗorata ajikinsa yay aikin a haka, haka in bacci ne tana manne a jikinsa. kuma yanzu duk ta san abubuwan da yake so da wanda baya so, dan a kwanaki ukun nan duk ya lissafa ma ta halinsa, ya faɗa ko mai da yake so ta dinƙa yi masa, kuma sai a yanzu ta fahimci ashe shi mutum ne me sauƙin kai in har ka fahimce shi. bayan sallar la'asar Fillo na zaune ita ɗaya a ɗaƙin Turaki, wayarsa ce riƙe a hannunta tana game, ta ajiye wayar tana ɓata fuska, Tunda Turaki ya fita masallaci bai dawo ba, wai Baffa yayi baƙi daga ƙauye sun zo ba su sameshi ba, shi ne yace yaje ya kula da su, gaba ɗaya bai fi minti goma sha biyar da fitar ba, amma duk sai take jin babu daɗi, ta san dai akwai ƴan aiki amma gidan duk sai taji yay ma ta girma, ba ta san ta saba da shi ba har haka ba, ji tai tana kewarsa sosai kamar tun safe ya fita ya barta, abu ɗaya kawai ta sani ba zata ji daidai ba har sai ya dawo. tun ɗazu tayi wanka but ta kasa shiryawa, so take sai yazo yayi mata choosing kayan da zata saka, cikin kwana ukun nan duk shi ke zaɓa ma ta kayan da take sawa, and ta lura ya fi son ƙanan kaya, amma yanzu fita za su yi, ba ta san waɗanda zai so ta saka ba a yayin da fitarsu za ta zama karo na farko. ta ɗau wayar tana jin kamar ta kira shi, sai dai bata so ta dame shi, duk da bai faɗa mata ba tasan shi ma hankalinsa na kanta. miƙewa tayi ta koma ɗakinta, ta buɗe wadrobe ta watso da duka kayan ciki, ta kama ƙugu ta tsaya tana ƙare musu kallo. ta ɗauki wata blue ɗin atamfa, tsaye tayi a gaban full body mirrow tana kara atamfar a jikinta tana kallon kanta, ta ƙara haske sosai alamun jin daɗi na ratsata, kuma idan tasa atamfar ma zata yi ma ta kyau sosai, sai tasa hannunta a kumatunta tana taɓawa, sai taga kamar ƙashin wajen ya fara komawa nama yana son cika wajen. a lokacin taji ƙarar buɗe ƙofa, tana juyawa idanuwanta suka sauka akan Turaki da ke gyara zaman hula a saman lallausan gashin kansa, fuskarsa ɗauke da wannan murmushin da yake tafiyar da tunaninta, baƙin boyel ne acikinsa ɗinki boda, yayi kyau sosai, sai taji kamar ta ɗauke shi ta kaishi can ƙuryar zuciyarta ta adana, ta yanda babu wani da zai dinƙa ganinsa, sai ita ɗaya tallin tal. Turaki ya gama gyara zaman hular tasa, ya ɗago ya kalleta, ya furta ya Ilahi a sanda ya lura da ƙwayar idonta. ya ƙaraso ciki da sauri, ya tsaya a dab da ita yana kamo fuskarta cikin tafukan hannunsa biyu. "Fulani nah me ya faru?, me ya same ki?, me ya taɓa ki?". yayi tambayar duk a lokaci ɗaya, me shirin kaɗan kawai sai ta sa masa kukan shagwaɓa, cikin sheshsheƙar kuka tace,"ba kai ba ne ka tafi ka barni ni ɗaya, gidan duk babu daɗi yay min girma". "shhh...". yasa hannu yana goge ma ta hawayen a hankali, ita kuma tana ƙara narkewa da shagwaɓe masa. duk sai yaji zuciyarsa ta matse da tausayinta, ya san tunda ya sabar ma ta da zama tare da shi yanzu dole ba zata ji daɗin zama ba idan ba ya nan. "i'm sorry Fulani Nah, ban san zan jima har haka ba da ban fita ba sai in aika Sameer kawai, sai da naje naga ashe wai wata gona za'a ba su, kuma ba su faɗa min ba har sai da na
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243