Chapter 42
Chapter 42
hakan akayi, cikin police mutum ɗaya yay driving motar Turaki. sai da suka yi nisa a tafiya sannan Khalil yace,"Hammah kasan wa ka kaɗe?". Turaki bai ce komai ba, kuma sai a wannan furucin nasa Hajiya Madina tama tuna da wata halitta da aka buge, ta manta da wannan batun ta ɗanta kawai take, kuma tana ganinsa lafiya shikenan ta ƙara mancewa da batun gaya mata da yayi ya buge wani. tace da Khalil,"koma wacece fatanmu ta rayu, idan ta dawo hayyacinta sai ta faɗi inda take ko kuma akai sanarwa gidan radio". Khalil yace,"Maama ai wadda muke tare ce, Fillo ce". da maɗaukakin al'ajabi Turaki da Hajiya Madina suka waro ido a tare. tace,"wace kuma Fillo?". Khalil yace,"me aikinmu dai". Turaki dai bai ce komai ba, bai san ya zai kimanta yanda yaji maganar acikin kansa ba. Hajiya Madina tace,"me yasa kace itace Khalil?". ya sauke numfashi yace,"idan munje asibiti za ki gani Maama". *Taraba.* ɗan ƙaramin tsakar gidan share yake tass, sai simintin yay haske kamar sabo. daga ɓangaren yamma wata ƙaramar ƙofa ce ta langa-langa, inda yake nan ne kitchen. wata dattijuwar mata ta fito daga ɗaki wanda yake daga ɓarin yamma ta buɗe ƙofar kitchen ɗin ta shiga. ta sunkuya ta sauke tunkuyar daga kan gawayin da take girki da shi. tana saukewa sai ga ƙaramin yaro da bai wuce shekara bakwai ba yazo wajenta yana faɗin,"Yaya ki zuba min abincin kar mu makara". sunan da suke kiran mahaifiyar tasu da shi kenan Yaya. ta kalli yaron sannan tace,"to Yasir yanzu zan zuba maka, ai kaga sai yanzu na sauke". ta faɗa a sanda ta ke ƙoƙarin ciro farantan roba daga cikin kwandon wanke-wanke. ta shiga zuba farar shinkafa da mai da yajin a faranti daban-daban, tana ta jin labarin da Yasir ke bata na yacca ake duka a islamiyar tasu. bayan ta gama rabon abincin tace da shi,"kira su Maimuna su zo su ɗauka, wannan kuma riƙe namu ne ni da kai, ka riƙe da kyau". ya karɓi filas ɗin abincin ya wuce yana ƙwala kiran Maimuna da Hindu kuzo ku ɗau abinci inji Yaya. yana shiga ɗaki Yaran suma suka fito suka ɗauki nasu, anan tsakargidan suka shimfiɗa tabarma suka zauna suna ci, Yaya na faɗa musu idan suka ɓata wurin sai sun share. hakan yasa Hindu tace da Yayarta Maimuna,"ni dai kinga ban ɓata wurina ba ko". wani saurayi da bai fi 26 years ba yayi sallama gidan, dogo ne sosai kuma ɗan siriri kamar sandar kara, fuskarsa kewaye da saje wanda ya haɗe da gemunsa, ga kuma gashin bakinsa shima da yaywa fuskarsa kyau. yaran suka amsa sallamar tasa suna yi masa sunnu da zuwa, ya amsa musu sannan ya shiga ɗakin kishiyar mahaifiyarsa da sallama a bakinsa. ta gama cin abinci tana siɗe yatsu lokacin, ya zauna kan kujerar parlon da duk taji jiki. ta kalle shi da tausayi tace,"an dawo?". sai dai ya sauke ajiyar zuciya sannan yace,"ehh Yaya sannu da gida". tace,"yauwa, ya wurin ɗinkin naku?". yace,"ɗinki babu daɗi Yaya, yanzu ma gudowa nayi saboda kaina da nake jin kamar zai fashe, jiya kwana nayi ban runtsa ba ina kan ɗinkin ƴan bikin nan". tayi murmushi tace,"to ya za'ai, neman halal da wuya, wataran kuma za'aji daɗi da izinin Allah...amma dai ka kammala musu ɗinkin nasu ko?". Hamid yayi gajeriyar dariya yace,"yanzu ma da su muka gama rigima ai, Suhaila na cewa ba zata ƙara kawo min ɗinki ba balle ranta ya ɓaci, kuma dan nace idan tayi haka ta burgeni shine tayi fushi ta tafi, inaga da kuka ma ta wuce". Yaya ta miƙe tana cewa,"an dai ji kunya wallahi, budurwar taka ma sai kayi mata halinku na teloli". gajeriyar dariya kawai yayi baice komai ba, Yaya ta miƙe tace da shi,"ka ɗauko abincinka kaci ka koma ka ƙarasa aikin mutane, bana son saɓa alƙawari Abdulhamid". ta shiga ɗaki don shirya Yasir, shi kuma ya wuce kitchen ya ɗauko abincinsa. yana cin abincin ne ƙannensa da suka shirya zasu wuce makaranta suka zo suka ce da shi kuɗin makaranta. yana kallon Maimuna yace,"har lokacin biya ya yi?". ta ɗaga kai alamar eh tare da cewar,"shekaranjiya da jiya ma duk sai da aka fito da mu, bamu shiga aji ba". yace,"kuma dan shirme shine baku faɗa ba". tace,"Kawu ai ban sani ba ko baka da kuɗi". yayi mata wani kallo yace,"ina ruwanki da rashin kuɗina, karki ƙara yin irin haka". tace,"to Kawu". Yaya ta fito daga ɗaki tana cewa,"ba laifinta ba ne ni nace su bari ba yanzu ba". yasa hannu a aljihunsa yace,"a'a Yaya to ai zuwan nasu baida amfani kenan tunda ko sunje ba barinsu ake suyi karatun ba, kuma ni ai na sami kuɗi kwana biyun nan". tace,"to Allah ya ƙara horewa dai". ya ɗauki dubu uku ya bawa Maimuna ƴar shekara goma yace,"ungo ki bawa Malam Ado, kice na Yasir da Hindu ne, dan Allah suyi haƙuri su ɗaga ƙafa jibi insha'Allahu za'a bayar da naki". ta duƙa ta karɓa suna yi masa adu'a, sannan Yaya tayi musu adua suka tafi. fitarsu babu jimawa mai gidan Yayi sallama, sallamar da ta hassada faɗuwar gaba a zuciyarsu Hamid. "Shema'u! Shema'u". kiran da me gidan keta ƙwalawa kenan, Yaya ta miƙe jiki a sanyaye ta fita tana cewa,"sannu da zuwa". yay mata wani banzan kallo yana zuƙar tabar dake hannunsa sannan yace,"sai yanzu kika ji kiran nawa ko amsawar ce ba ki ga damar yi ba?". bai jira cewarta ba ya ɗora da faɗin,"mutuniyar banza da wofi kawai, to ki gama rashin mutuncinki wallah idan banga dama ba aljannah dai ba za ki shigeta ba, tunda a ƙasan ƙafata aljannar taki take, kuma har saina ɗaga miki za ki shiga...kuma indai don ta ni ne na rantse sai da ki zama ƴar kallo, kina ganin mata na tururuwar shiga ke kina daga gefe can". *Pls Vote, Comment and Share.* [8/27, 20:15] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halimahz* *Anyway@arewabooks* *HalimaAnyway@Wattpad* *Halimahz@Bakandamiyahikaya* *17* Yaya dai tayi shiru bata tankawa maganarsa ba, idan ma tace zata basa haƙuri wani sabon cin mutuncinne zai biyo ba, to shirun shi yafi alkhairi, but down deep in to her heart zafi ta ke ji, wannan halin na mijinta bata so, ƙaddara dai ta riga fata, ta ɗauki aurenta da Hayyo matsayin wata jarabawa daga ubangiji, kuma tana roƙon Allah ya bata ikon cinyewa. ta mayar da tarin ƙwallar da ta cika idanunta. ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ɗago ta kallesa tace,"a ɗauko maka abinci?". Hayyo yayi mata wani kallon banza yace,"mayya kawai wadda kare ya cinye zuciyarta, indai haƙuri ne naga Halima ma, dan haka kema muna nan wannan kafirin haƙurin naki zai kaiki maƙurar da za ki bar gidan nan da ƙafafunki. yo guda nawa kuma akayi?, saki dai kike so saboda ki tafi da hujja to ni ba zan sakeki ba dan bana yinsa, musulmin ƙwarai ne ni sam bana son al'arashin ubangiji ya girgiza". Yaya ta girgiza kai kawai tana me cike da takaici, ita kanta ta sa ni haƙuri yayi kaɗan ya barka ka zauna da Hayyo, sai dai darajar ƴaƴa, tun bayan aurenta da shi daya sami biyan buƙatar kansa ya fito mata da asalin halinsa wanda yake ɓoyewa a lokacin aure, ta kuma san asalin waye shi wanda
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243