Chapter 134
Chapter 134
tausayin Fulani Azima domin ita ɗin mutum ce a garesu, duk wanda zai buɗi baki ya faɗi aibutunta to sai dai idan maƙiyinta ko kuma wanda basa shiri. duk cikin su huɗun ita ɗaya ce babu ruwanta a yanda take nuna musu, ko irin kishin nan ma na rashin haihuwar ɗa namiji ita bata yi sam bata ɗaga hankalinta ba, hasalima kama nasu ƴaƴan take kamar nata, nan kuwa duk basu san tana bi musu ta ƙarƙashin ƙasa ba ne, fir'auna ce a zuciya Allah a fili. suka miƙe gaba ɗayansu suka wuce zuwa room ɗin da take, duk me cikakken imani kallo ɗaya zai yiwa Fulani Azima yaji saukar hawaye a fuskarsa, kwance take kan gadon kana kallon idonta na dama zaka san bata gani da shi kwatakwata, sai kallon kowa take yi da ɗayan shima kuma dusudusu take gani, ga karaya a hannayenta duka biyun banda ta ƙafarta guda ɗaya, kallon kowa kawai take tana hawaye masu zafi. ita so take ma tayi magana amma ta kasa, tun washegarin ranar da abun ya faru taso ta buɗi baki ta nemi yafiyar Hajiya Ramla a sanda suka je dubata, amma tayi tayi tai magana sam ta kasa, ga shi duk ta yanda taso tayi wata alama da zaisa a fahimci tana so tayi magana da Hajiya Ramla ta kasa, kuma daga yanda taga fuskokin familyn Dikko tasan ko kusa Hajiya Ramla bata tona mata asiri ba, akwai tabbas ɗin bata faɗawa kowa komai ba, wanda hakan ya ƙara haifar da danasani da kuma dama nadama a tare da ita, tana ji tana gani ko da bata mutu ba tata rayuwar dai ta ƙare, ita da matacce marabarsu numfashi kawai, babu abinda take biɗa a yanzu sama da ta kalli Hajiya Ramla a gabanta ta nemi yafiyarta, sannan taga Jakadiyya da Drivern da ta kashe suma tace su yafe mata, to amma ba zata samu duka wannan damar ba, haka zata tafi lahira da tarin zunubi da kuma hakkin waɗanda ta zalunta, shikenan ita kuma tayi biyu babu, babu nan duniyar babu can lahirar, innalillahi wa'inna ilaihi raji'un. sosai take kuka idonta guda ɗaya na hawaye, inama ace a dawo da baya, da tayi amfani da damarmakin da take da su ta gyara lahirarta, to sai dai hakan ba zai kasance ba, lokaci ya riga ya ƙure mata, yanda kowa ke ganin saukar hawayen nata babu wanda ya fahimci me take buƙata, sai tausayinta da kowa yaji yana roƙo mata lafiya a wurin Allah. Ilham ta ƙwace daga hannun Sauraniya Mabruka ta isa gadon ta faɗa jikinta ta fashewa da wani irin kuka, kukan da duk sai da ya saka kowa dake ɗakin hawaye babu shiri. *Dubai Quarters, Gombe State, Nigeria.* daga ɓangaren kudu, gida na tsakiya me lamba 20, flat house ne ɗan tsakiya me ɗauke da milk gate da abuja brown paint, sai flowers dake zagaye da ƙofar gidan, daga yanda wajensa yake da kyau zaka shaida cikinsa ma me kyau ne. daga cikin gidan Fillo ce a ɗakinta kwance akan madaidaicin gadonta, ba bacci takeyi ba idanuwanta a rufe suka kawai hawaye na bin gefen fuskarta. ta tashi zaune tana saukowa akan gadon ta shiga toilet tayi alwala tazo ta tayar da sallah, tana cikin sallar Ummi ta shigo, ganin tana sallar yasa ta ce mata,"idan kin idar ki fito muci abinci". bayan Fillo ta idar ta kalli agogo taga har biyu saura, dan haka bata fita ba sai da ta saka uniform na islamiyarta tukunna, ta ajiye hijab ɗin da jakar akan gadonta ta fito cikin sauri. Kaka da Ummi na zaune a ƙasa kan carpet suna kallon tashar arewa 24 ana maimaicin kwana casa'in, ta zauna gefen Ummi sannan su kai bismillah suka fara cin abincin, bai fi spoon biyar Fillo tayi ba ta miƙe, Kaka da Ummi suka bita da ido har ta shiga ɗakinta. wucewar minti biyu sai gata ta dawo riƙe da jaka da hijab a hannu, ta zauna kan kujera tana kallo tv tana ji tana neman kasa riƙe hawayen dake yunƙurin zubo mata. sai bayan da su Ummi suka kammala cin abincin sannan Kaka na dubanta tace,"kinga, kinga Fillo ki kiyaye ni, na faɗa miki ki cire batun cutarwar da Amir yay miki a ranki amma kinƙi ji ko, haka kawai kina ƴar ƙarama dake kisawa kanki damuwa salon kija mana masifa, ke bama abin farin cikinki bane tunda har aka sami bayin Allahn da suka tsaya miki hukuma tabi miki hakkinki". take kuwa hawayen da take ta riƙewa suka zubo, ta kifa kai da gwiwa tana fashewa da kuka, Ummi na kallon ƴartata da tausayawa tace,"Auta zo nan". ta taso ta dawo kan kujerar da Ummi take ta kwanta a jikinta. Ummi na shafa kanta tace,"kina so na koma inda ba xaki ƙara ganina ba?". da sauri ta girgiza kanta da cewar,"a'a Ummina". tace,"to ki daina kuka haka nan ya isa bana so, ki manta da duk abinda ya zama past ki focusing akan rayuwar gabanki, babu abinda zai fishsheki yanzu sama da ki mayar da hankali akan karatunki shine kawai gatanki har zuwa ranar da Allah zai kawo miki miji na gari kiyi aurenki". bata daina kukan ba tace,"Ummi har yanzu abin yana yi min ciwo sosai". Ummi tace,"sai ki godewa Allah da ya tona asirinsa tun bai aureki ya miki cuta me gaba ɗaya ba, ki kuma gode masa da ya kareki daga sharrinsa a iya zaman da ku kai da shi". tayi shiru bata ce komai ba, idonta na haska mata hoton jiya sanda suka je kotu ita da su Maama akan case ɗin Amir da aka ƙarke a jiyan, tana tsaye a bayan Mum taji Turaki ya kama hannunta ba tare da sanin kowa ba suka bar wajen, kuma duk ta yanda taso ta raba hannunsa da nata ta kasa har suka shiga wani ɗaki inda aka kai Amir shi da tawagarsa, kallo ɗaya tayi masa ta saurin ɗauke kanta gefe dan a duniya idan da mutumin da bata ƙaunar gani bai wuce shi ba. kuma tsabar rashin kunya irin da azzalumin bawa wai har yake zubewa a gaban ƙafafunta yana roƙonta Allah da Annabi akan ta yafe masa abinda yay mata, sannan ta roƙar masa alƙali ya sassauta masa hukuncin da aka yanke masa na zaman prison tsawon shekara goma sha biyar, har da wai in ya fito yayi mata alƙawari zai tuba ya koma mutumin arziƙi ya aureta. wannan maganar kuma ita tayi mata zafi bata san lokacin da ta ɗaga hannu ta wanke shi da maruka har biyu ba, Turaki kuma ya karɓi kulki a hannun police ya bata, ta dinga buga masa a fuska har sai da taga jini yana zuba ta hancinsa tukunna ta ƙyale shi tayi saurin fita daga ɗakin, in ba haka ba tsab zuciya zata iya sata ta rarumi duk abinda zai kai Amir Lahira ta buga masa. Kaka na kallon Ummi tace,"Halimatu kinga duk inda Hamid yake yana nan hankalinsa na kanki da tunanin halin da kike ciki, fushin fa da kike da mahaifinsa ba zai fa shafe shi ba tunda ba shi yay miki laifi ba". fuskar Ummi ta juye zuwa ɓacin rai tace,"Dada zan nemi Hamid amma ba yanzu ba, akwai lokacin da nake
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243