Chapter 128
Chapter 128
da Mum". ai kan kace me wannan asibiti ya karaɗe da ihun murna, duk suka tafi da gudu suka faɗa kan Hajiya Ramla suna ta ihu, wanda in ace a tsaye ta-ke sai sun kaita ƙasa. Zaytuna ce kawai ta tsaya taƙi zuwa wajen tana kaudar da fuskarta da gefe, dan ita bata ganin zata yi farinciki kamar yanda bata tunanin zata yafewa Mum. Ilham kuwa na tsaye daga gefen su tana ta kallon su cike da burgewa, musamman Turaki da ta kasa ɗauke idonta a kansa saboda yacca ta-ke ganin haƙoransa gaba ɗaya a waje, da irin tarin farin ciki da annurin da bata taɓa ganinsa ba aciki. a ɗazu hankalinta duk a tashe yake da bai dawo gida ba, haka da taji wurin kidnappers ya tafi hankalinta ya ƙara kaiwa ƙololuwar tashi, but a yanzu zata iya cewa kamar tana jin kanta ne a saman gajimare tana tafiya, ko ba komai tasan lokaci yayi da zata samu wannan gurbin da Turaki ke cewa ba zata same shi ba a zuciyarta, ta sani wuyarta mahaifiyarsa ta san ita matarsa ce, ita kanta bata san Mum ba dan ba'a haifeta ba lokacin, amma kallo ɗaya ta yiwa Mum ɗin tasan itace mahaifiyarsu da kowa ya taso a family yake jin labarin ɓatanta. a taƙaice dai Maama da iyalanta duk sai suka manta da batun wata Fillo saboda tsabagen farin cikin da suke a ciki. kuma haka suka zama ababen kallo a wajen dan tuni akai caa akansu ana kallon ikon Allah. gaba ɗaya sun cikwikwiye Hajiya Ramla sun kasa jin ma abinda ta-ke cewa na,"ina da patient kuyi a hankali". but inaa duk wannan batu da take yi babu wanda ya jita hatta Turaki dake manne a jikinta. kuma a lokacinne Kaka suka shigo ita da su Yami da Khalil waɗanda yaje ya ɗauko daga asibiti, sai dai me?, zuwan su wajen kawai suka ga Fillo a guje ta fito tana ƙwala kiran,"Kaka ga Ummina, Kaka Ummina ta dawo". *Vote, Comment, and Share.* [8/31, 01:15] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* _😂😂yau dai ina typing ina gyangyaɗi, so duk baragadar da ku ka ci karo da ita ku gyara da kanku kawai🤣🤣._ *37* gaba ɗaya Fillo sai ta rikice ta firgice ta nemi fita a hayyacinta, ba don komai ba sai dan tsananin murna da kuma mamakin ganin mahaifiyarta a lokacin da bata tsammata ba, tsabar farin ciki ji take kamar ta zuba ruwa a ƙasa ta sha. ganin komai ta ke yi tamkar mafarki ko kuma ba daidai take gani ba, lokacin da ta farka da matsanancin ciwon kai ta tashi, amma buɗe idon da zata yi ƙwayar idanunta suka sauka akan Ummi dake zaune a gefenta ta kama hannunta ta riƙe tana hawaye. da farko tai zaton gizau idonta yay mata, dan haka tai saurin maida murfin idonta ta rufe sannan ta ƙara buɗewa, kuma a wannan buɗewar ne ta tabbatar da abinda ta gani ɗin gaskiya ne, Umminta ce a gabanta, wannan macen da tafi gwal, tafi zinare, tafi lu'u lu'u girma da daraja, wannan macen ce da bata da tamkarta a duniyarta, tauraruwar da ke haska duniyarta, mahaifiyarta ce mafi soyuwa a ranta, jarumar da tai fama da rainon cikinta tsawon watanni tara, jarumar macen da ta tsaya tsayin daka akan ibadarta da iliminta da kuma tarbiyarta, jarumar macen da ke sadaukar da farincikinta domin ƴaƴanta, jarumar dake ɓoye zafin ciwon rashin lafiyarta gudun tashin hankalin ƴaƴanta, jarumar uwar da ta kan iya haƙura da loma ɗaya na abinci da zata sa a bakinta ta rabarwa ƴaƴanta, tabbas itace, ba zata mantata ba ko da ace tana cikin ciwon hauka ne, har a naɗe duniya ba zata kasa gane ɗumin jikinta ba, ba zata manta wannan farar fuskar da bata iya bacci ba har sai ita tayi, abu ɗaya da ta san yake dahir shine uwa dabance, daban take da kowacce irin halitta a duniya, soyayyarta dabance da ta kowa, ƙaunarta ma haka, mahaifiyarta itace ranta itace jininta itace duniyarta. hawaye ta dinƙa ji yana bi ta gefen fuskarta, dama tasha faɗawa Kaka cewar Ummi bata mutu ba tana raye, kuma da izinin Allah zamu gana da ita, sai ga shi yau ta ganta, sai ga shi ta ganta a ranar da wani macuci, azzalumi ya dasa baƙin ciki a zuciyarta wanda ba zai taɓa gogewa ba, to mai ma zai ci gaba da zamar da wannan baƙin cikin alhalin ga mahaifiyarta ta dawo a sanda take tunanin babu me iya share mata hawayen baƙin cikin da Amir ya haifar mata?, ai babu wani sauran baƙin cikinsa kuma, ta san in ace bata sami ganin mahaifiyarta ayau ba, to tabbas baƙin cikin abinda Amir yayi mata shi zai zama ajalinta. zata iya cewa bata san lokacin da ta yunƙura ta miƙe zaune ba daga kwancen da take, jinta tayi kawai ajikin Ummi tayi mata wata tsatstsaurar runguma, Ummin ma ta kewayeta da dukkan hannayenta tana daɗa matseta a jikinta, Fillo taji saukar wannan ɗumin na daban wanda ajikin uwa kawai aka halicci yana ɗumama jikinta, tana jin wannan soyayyar mahaifiya ta daban tana ratsa jini da sassan jikinta, sai kawai suka fashe da kukan farin ciki a tare, babu wanda ya lallashi wani acikinsu har sai da suka yi me isar su tukunna. cikin muryar kuka tace,"Ummina ina sonki sosai". kuma abinda taji Ummin ta fara ce mata shine,"Auta wa ya kawoki nan garin?, me ya sa me ki haka?". ta tambayeta ɗin tana janyeta daga jikinta tana dubanta, tana yi mata kallo me cike da tausayi da kuma fargabar abinda bata fatan ya kasance a rayuwar ƴarta, domin tasan rashin uwa a tare da ƴaƴanta babu halin da baya jefa su, balle kuma su da basu yi sa'ar uba ba, wanda ko kallonsu ba yayi balle ya kula da rayuwarsu. a lokacin sai kawai ta faɗa ƙirjin Ummi tace,"Ummi kullum sai nayi kukan rashinki, Ummi ko me nake yi tare dake nake yinsa a zuciyata, Ummi duk sanda naga ƴa da mahaifiyarta sai nayi ta kuka in kasa ko da cin abinci. Ummina me yasa kika tafi inda ba zamu ganki ba?, me yasa baki ci gaba da wannan haƙurin naki ba?, me yasa kika bari takaicin ɗa namiji da baƙin cikinsa yasa kika nesanta kanki da ƴaƴanki da kowa naki?, Ummi kin san kuwa tsananin son da nake miki?, muna fa yi miki so me zafi, Ummi kin san buƙatar rayuwar ƴaƴa shine mahaifiyarsu, amma mu sai kika ƙaurace mana na tsawon shekaru da yawa, Ummi ba kiyi tunanin in ta gayyara ba?, ba ki yi tunanin...". bata ƙarasa ba Ummi tasa hannu ta rufe mata baki, hawaye na zubar mata tace,"tambayar da nayi miki daban, zancen da kike min daban". Fillo ta ƙara matseta tace,"kiyi haƙuri Ummina". tace,"ban san amsar tambayata". Fillo ta rumtse ido tace,"ai tun sanda kika tafi na dawo wurin Kaka. wannan halin da kika ganni a ciki kuma wanda zan aura ne sila". lokaci ɗaya jikin Ummin ya hau kyarma ta ɗago Fillo ajikinta tana bin ta da kallo tace,"ya zamo silar me?, me yay miki?, ina Kakan?". tace,"garkuwa yayi dani Ummi after all na basa dukkan yarda". ta faɗa tana fashewa da kuka sosai, muryar Ummin ta fita a hankali da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243