Chapter 188
Chapter 188
ba ta dawo ba ga ƴan aiki nan an ajiye miki cikakkakun ƴan mata masu buɗaɗɗan ido, inda rabon sun ƙwace miki miji sun barki da sakakken baki ne ke kika jiyo, dan wallahi ni ban wani yarda da ƴan aikin nan ba, son samu ma duk ki saita musu hanya kiyi aikinki ke ɗaya, mene abin wahala anan, haka kawai ƴan aikin yanzu da suke ƙwace maka miji". ita dai Fillo jinta kawai take bata ce mta komai ba, tun sakkowarsu Yami ke bin su da kallo har suka ƙaraso suka zauna kan kujera, Fillo ta sauko ta gaishe da Yami, ita dai Yami sai kallonta take yi cike da nazari da son gano wani abu, kuma cikin hikima ta iyaye manya ta fahimci abin da yake faruwa ba tare da ko ta tambayi Fillo ɗin ba, ai kuwa nan da nan Yami ta shiga yi ma ta nasiha sosai, da ƙara koya ma ta dabarun riƙe miji gam a tafin hannu, ita dai Fillo ji kawai take yi, don ba ta tunanin zata aiki ko da abu guda indai akan Turaki ne. lokaci ɗaya Fillo ta sake, su Yami su ka ɗebe ma ta kewar da take ciki, hira sosai kamar sun shekara ba su haɗu ba, tana ta zumuɗin za ta ji muryar Ummi ta tambayi Yami wayarta tace ai ta lalace, ɗoki da murnar da take ciki duk sai taji sun gushe, har la'asar su Yami su na nan ba su tafi ba. su na cikin kallo Turaki ya shigo, ita ta fara kai kallonta kansa, haka kawai sai taji gabanta ya faɗi, tayi saurin ɗauke idonta a kansa ganin wani kallo da ya yi ma ta fuskarsa a tamke. ya shigo ya zo ya gaida Yami, suka gaisa sosai tana sanya masa albarka tare da yi musu adu'a sannan ya wuce sama. bayan tafiyarsa Yami ta kalli Fillo ta ce da ita,"ban ji kin yi masa sannu da zuwa ba, ba ki tashi kin karɓi jakar hannunsa ba, duk lafiya?". ta turo baki gaba tana faman ɓata fuska, ai kuwa Yami ta shiga yi ma ta faɗa sosai kamar zata duketa. "ta shi ki bi bayan mijinki". murya a kumbure ta ce,"ai sai kun tafi zanje Yami". tai maganar alamarta na shaida ko sun tafi ɗin ba zuwa zata yi ba. Yami ta taso mata da faɗan da yafi na ɗazu, ba shiri ta miƙe kamar zata yi kuka ta wuce sama fuuu, tana hawa ta shige ɗakinta, sai kuma taji kamar Yami zata hawo saman, hakan yasa tai saurin fitowa ta wuce ɗakinsa. ta buɗe ƙofar ta shiga babu ko sallama, ta nemi bakin ƙofa ta maƙale tana jan yatsu sai kace munafuka, Turaki ya buɗe idanuwansa da ke rufe ya bi ta da kallo, ƙwayar idonsa kawai za ka kalla kasan akwai abin da ke damunsa, akwai abin da yake buƙata sosai, ta ɗago ido karaf suka haɗa ido da shi, sai ta saurin juya masa baya, ya miƙe zaune da ga kishingiɗen da yake ya ce,"is there anything?". ta juyo tana turo ba ki gaba cike da zallar yarinta tace masa,"Yami ce ta ce na biyo bayan ka". babu shiri murmushi me kama da dariya ya suɓuce a leɓensa, sai ya tallafi haɓa yana kallonta kawai, ganin hakan yasa ta ɗan duki ƙafafu a ƙasa ta ce,"ce tayi ka kira min Ummi a waya". sai ya ɓata fuska ya mayar da kansa jikin pillow yace,"ba ki faɗa mata kin tarwatsa wayar ba?". kamar zata yi kuka ta ce,"ai na faɗa maka bana sa ne". "to sai ki jira sai kin gyaro sai kiyi kiran". kawai sai ta saka kuka tana faɗin,"to wayan naka ai ba guda ɗaya ba ne, dan Allah ka bani in kira Ummina, yau kwanana 9 banji muryarta ba fa". ya galla mata harara, banda tana kuka tsab sai tayi dariya saboda yacca idanunsa suka yi a hararar, ta ƙara dukan ƙafafu a ƙasa da shagwaɓa sosai tace,"don Allah ka ba ni kaji, to ni ka bani lambar sai inje wajen Baba me gadi ya ara min tasa". ya kasa ɗauke ido akanta, sai yaji tana cewa,"kuma kai fa kace za ka zame min kamar Abba nah". sai ya sauke numfashi ya ce,"zo ki ɗauka". ta taho kamar wadda ta yiwa ƙasa laifi, tana zuwa bakin gadon taga duka wayoyi biyun akan bedside locker har ma da keypad, tana kallon wacca ta fasa ta gane ta, kenan an gyara ma shi ne yake ta yi mata ciwon baki, ta ɗan waigo kaɗan ta kalle shi taga hankalinsa bai kanta, sai ta kai hannu zata ɗauki wayar, caraf taji ya riƙo hannunta ya janyota jikinsa ya zaunar da ita kan ƙafafunsa da ke tankwashe. "da kika fasa ai ba ki iya ba da haƙuri ba, shi ne saboda rashin kunya yanzu an gyara za ki zo ki ɗauka, to ba ni sai kije can wajen me gadi ya ara miki". ta shiga kokawar ƙwace hannunta tana faɗin,"to ai kaine kace in zo in ɗauka". "ehh ai ƙarshen rashin kunyarki zan gani kuma na gani, ba ni wayata ba zan bayar ba, kije shi me gadin ya ara miki tunda dama wajensa kike zuwa aron abu". ta ce,"to ka ban lambar". kawai ya fizge wayarsa sannan ya ɗauketa daga kan ƙafar tasa ya dire a ƙasa, yasa wayoyinsa a aljihu yay shigewarsa toilet, after 3 minutes ya fito yana goge hannu da ƙaramin towel, mamaki yasa shi tsayawa yana kallon Fillo da ke durƙushe ta kifa kai akan gadon tana kuka bilhaƙƙi, yau rana ɗaya da ya tambayi kansa shin hawaye basa ƙarewa ne?, ko da yake in su na ƙarewa ai da tuni ya sami salama da wannan kukan, ya girgiza kai ya koma toilet ya mayar da towel ɗin sannan ya fito. ya dawo ya koma kan gadon yay kwanciyarsa ya juya ma ta baya, taji yana waya yana cewa,"oak gani nan, ki ajiye ki wuce, na bawa Samha saƙonki". ta ɗago kanta lokacin da yake sakkowa akan gadon yana barin ɗakin, ta bi bayansa da kallo, after few minutes sai ga shi ya dawo ɗauke da basket ɗin abinci, ya wuce ya ɗora akan table, sannan ya zauna akan kujera ya shiga zuba abincin da ke cikin flask, duk tana kallonsa yadda yake yi tamkar bai san da halittarta a ɗakin ba, ita kuma tana yi ana yana shareta shi yake daɗa tunzurata, hakan na ɓata ranta, har ya kammala cin abincin bayan ya tsarga masa ya taso ya dawo kan gadon, yay kwanciyarsa kamar mai bacci. can yaji ta riƙo hannunsa, ya juyo yana kallonta, ta kifa goshinta akan hannun nasa, hawayen idonta ya sauka akan fatarsa, ɗumin hawayen ya wuce ta cikin jijiyoyinsa har zuwa ƙirjinsa, tausayinta ya wanzu a zuciyarsa, gaba ɗaya jikinsa sai yay sanyi, Allah ma ya sa ni yana tsananin tausayinta, basarwa kawai yake yi, ko shi da yake namiji ba ya jin zai iya ɗaukar 2days bai ji muryar Mum da Maama ba, balle har akai ga kwanaki tara, ai sai rashin lafiya ta kama shi. but sai ya ƙara ɗauke kansa akanta, ya tamke murya ya doka mata tsawa yace ta fitar masa a ɗaki, ta miƙe jiki a sanyaye
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243