Skip to content
NovelPress

Hausa Novels

Chapter 227

Chapter 227

Lullubin Biri Book 1 Complete Hausa Novel 1,210 words 0 views Progress saved
Download Book

kuma ya jin zai iya. don haka sai ƙafafunsa duka biyun suka tankwashe, yayinda da dukkan hannayensa ke riƙe da nata, a sanda kuma ƙwayar idonsa ta kasa ƙiftawa akan fuskarta. "ba ki taɓa yin bacci me nauyi ba irin na yau Maama, ba ki taɓa ba. tun ina ƙarami ba kya iya baccin rana kawai saboda mu, balle ma har ki sami damar yin me nauyi, amma yau zan bar ki ki huta, ki yi baccinki yanda ya kamata, na san kin gaji ne, zan zauna tare da ke har sai kin farka". a lokacin da yay shiru da maganar, a lokacin yaji tarin ruwan hawaye sun cika ƙwayar idonsa, zubowa suke so suyi ya sani, amma ba zai ba su damar hakan ba har sai abun da yake gudu akan farin cikinsa ya tabbata. shigowar Hajiya Ramla ɗakin yasa shi juyawa ya dubeta, sai ya ganta gaba ɗaya a rikice, cikin irin rikicewar nan da bai taɓa ganinta aciki ba. "Madam, Maaman yara, kar muyi haka da ke, kar kiyi mana irin wannan baccin, tashi haka don haka don Allah Madam". zantukan da Hajiya Ramla ke yi kenan a sanda ta sami zama a gefen Hajiya Madina, sai ta ɗagota zuwa jikinta, sai taji gaba ɗaya jikinta ya saki, jikin Hajiya Madina ya zame daga nata ya koma makwancinsa. ƙafafun Fillo suka tsuguna a kusa da Turaki, ta dafa kafaɗunsa hannuwanta na rawa, sai taji ɗan cikinta ya motsa a lokacin da ya riƙo nata hannun, ya juyo ya kalleta, suka haɗa ido tana ganin abun da bata taɓa gani ba acikin idonsa, ruwan hawaye!, ruwan hawayen da su ka sanya zuciyarta bugawa. lokacin da Hajiya Ramla ta tabbatar da baccin Hajiya Madina ba na farkawa ba ne, lokacin tayi ƙarfin hali da dakiyar kallon Nihal, wacce ke tsaye ta kasa ƙwaƙwƙwaran motsi, idanuwanta duk biyu a waje. "Mum Maama bacci take yi ko me?, suma tayi?, zata farka?, ana ta tashinta taƙi ta tashi". "idan baka saba aiki ba kayi to duk jikinka sai ya mutu, ina tunanin gajiya ce tasata wannan baccin me nauyi, ba sai mun tasheta bamu barta ta huta sosai". sai ta juya ta kalli Turaki, ta ƙara juyowa ta kalli Nihal ta ce,"ina wayata?". "Mum gata nan a hannun ki ai". tsabar ruɗewa ta manta ma da wayar na hannunta, ta shiga contact ta danna kiran lambar Family Doctor ɗin su. yana ɗaga tace da shi,"don Allah ka iso gida yanzu". bayan ta ajiye wayar Nihal ta ce da ita,"Mum wa kika kira?". "Dr Ibrahim ne". sai a sannan Turaki ya ɗago ya kalli Mum, mene na buƙatar likita kuma a wannan lokacin?, idan ya zo me zai yi?. su ka haɗa ido da Mum ɗin, tace da shi,"da yake tace min tana ciwon kai ɗazu, gwara ya zo ya dubata wataƙila BP ɗin ne ya hau ba mu sani ba". ta fita a riki ce, tana sauka ƙasa taci karo da Sameer da Khaleel, sai suka tsaya kallon juna. "da ma ba ku fita ba?". Khaleel yace,"dawowa muka yi, lafiya Mum muka ganki a haka?". "a'a babu komai, ko zaku koma kuga idan Baffa ya dawo?". Sameer ya ce,"yanzu ya kira mu, yace ya kira wayoyin kowa bai samu ba". "to ku tsaya anan ku kira min shi a waya". ta faɗa tana juyawa ta koma saman, Khaleel ya bi bayanta da kallo zuciyarsa cike da nazari da zurfin tunani. a san da Dr Khamis ya ƙaraso, idanuwan kowa na kansa a lokacin da yake wasu dube-dube a fuskar Hajiya Madina, da kuma gwaje-gwajen da yake yi. ban da Turaki da idonsa ke kan Maama kawai, yana jin wani bala'in ruɗani na shigarsa. cikin ƴan mintuna kaɗan Dr Khamis ya gama bincikensa, a sannan ne kuma idanuwan Turaki su ka koma kan likitan, yana kallonsa ya matsa kusa da Mum da Khaleel, wanda yake tsaye cikin ƙarfin hali. ya san dai likitan bayani yake yiwa su Mum, domin yaga bakinsa na motsawa, laɓɓansa na motsawa da harufan da riga ya san ma'anar su. kuma cikin sakanni uku sai ga Hajiya Ramla ta dawo kusa da Hajiya Madina, ta kamo hannayenta ta riƙe acikin nata, kafin a hankali laɓɓanta su tale da furta kalmar,"innalillahi ra'inna ilaihi raji'un, gare shi mu ke kuma gare shi zamu koma". furucin da ya haddasa motsawar zuciyar Turaki sannan ƙarfin bugunta ya ƙaru a lokaci ɗaya. idanuwansa suna kallo Mum ta ɗauki zani ta rufe Hajiya Madina da shi, ta rufeta har fuskarta, ta lulluɓeta da wannan zanin da ta ɗauko a jiya tace musu ta siyo shi ne saboda goyon jikanta. ba zai manta da wannan lulluɓin ba, ba zai manta da shi ba har a bada. sai kawai ya kifa fuskarsa akan ƙirjin gawar, hannunsa na dama kuma ya shige cikin sanyayyan nata hannun na dama. "Maama, Maama, don Allah ba yanzu ba Maama". yay maganar da wata karyayyar murya, a san da yay wannan furucin, a sannan ne hawayen da suka taru acikin idonsa suka sami nasarar gangarowa saman kumatunsa. idanuwansa suka runtse, hoton rayuwarsu na tsawon shekaru 27 na haska masa daki-daki, a lokaci ɗaya kuma duk wani sauti na muryarta na amsakuwa acikin kunnensa da cikin kansa, sautin muryar da ya tabbatar ba zai ƙara jinsa ba. ya riga ya sani, faɗar ubangiji ce kullu nafsin zaa’iƙatul maut, Allah ya faɗi hakan har sau biyu a littafinsa me girma, duk wani bawa mutuwa tana kansa, duk wani me rai sai ya ɗanɗani zafin mutuwa, yaro ko yarinya, babba ko ƙarami, sabo ko tsoho. ya sani Mutuwa dole ce, ya san mutuwa akan kowa ta ke, ka aikata sharri ko akasin haka zaka mutu, kana kan aikata daidai ne ko akasin haka, baka san a wani hali za'a ɗauki ranka ba, za mu mutu a yau, ko gobe ko jibi, ko anjima ko yanzu, sai dai dukkanin mu babu wanda yasan a wanne hali zata riske shi, kai dai bawa baka sani ba! baki sani ba! ya sani yin mutuwa ko ambatonta bai da daɗi, amma dole ne sai mun mutu, dole za mu koma ga wanda ya halicce mu, wajibi ne mu amsa kiran ubangijin mu mai son mu, mai ƙaunar mu, mai jiran tuban mu a ko yaushe, dole ne zamu bar duniyar da aka ara mana, haka dole zamu tafi mu bar duk abin da muke so, haka dole zamu kwanta a ƙabari. kana tsaka da jin daɗin rayuwa mutuwa na iya zuwar maka, wani tazo mishi fuj’an, wani ta zo mishi idan yay fama da rashin lafiya, wani tari kawai zai yi, wani atishawa kawai zai yi, kuma da zarar ya furta Alhmadulillah sai Kaga a wannan lokacin an ɗauki ransa, wani yana sallah za'a zare masa rai, wani daga bacci shikenan za'a zare ran, sai dai ya farka ya gansa a ƙabari, gidan da yake na gaskiya, gidan kowa. duk irin son mu da duniya wallahil azim sai mun barta, duk irin so da ƙaunar da muke yiwa juna wallahil azim mutuwa sai ta raba mu, Ya Qadeer kai mana kyakkyawan ƙarshe, Ya Rabbi kasa mu dace duniya da lahira Ya'ilahi! Ya Hayyu Ya ƙayyum, kasa mu mutu muna matsayin mutanen kirki, ba waɗanda zamu mutu duniya da

Table of Contents

Chapters

243 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243