Chapter 151
Chapter 151
ya sauka akan mahaifinta dake kallonta yana murmushi da hawaye, alamun na yaji daɗin ganinta, lokaci ɗaya ta haɗe rai ta ɗauke idonta daga kansa. ta kalla Ummi dake ƙoƙarin raɓata ta wuce, ta kama hannunta zasu fita maganar Hamid ta tsayar da ita. ta juyo tana kallonsa tace,"Hamma dana ganka sai naji farinciki ya kamani, amma da naga wannan masifar a tare da kai sai naji kamar in haɗiyi zuciya in mutu, saboda na san ba komai ya samin Ummina kukan da ta jima bata yi ba, dan haka gwara mu bar muku nan ɗin dan ba zamu ƙara zama da masifar da zata hanamu farinciki da jin daɗin rayuwa ba". tana rufe bakinta Hamid ya ɗauketa da mari, kuma bai sauke hannunsa ba Ummi ta zabga masa marin shima. "ƙarya tayi ba masifar bane shi da har zaka ɗaga hannu ka marar min yarinya, to wallahi ka kiyayeni kar kaja ɓacin rai yasa bakina ya zama silar lalacewarka a duniya, kuma na fasa tafiyar kaje ka gangaro shi kuzo ku fita a gidan nan tunda ba uban wani ya gina mana ba". maganar Hayyo ta shiga kunnen Fillo a sanda yake cewa,"dan Allah dan Annabi ƴata ki yafe min, ki tausayawa halin da nake ciki, wallahi na san alhakinku ke bibiyata shisa na faɗa cikin wannan mawuyacin halin". Ummi tace,"ai baka ga komai ba, kaɗan ma ka gani, kuma insha'Allahu nan gaba maganar ma sai ta gagareka, da izinin Allah sai kowa ya gujeka ya barka kai ɗaya a halin da yafi wannan muni". Hayyo ya kulle idonsa yana ƙara roƙon su Ummi su yafe masa, tasa tazo ƙarshe su taimaka masa kar ya tafi lahira da alhakinsu, Fillo na kallonsa cikin ƙunci tana tuna voice ɗinsa da taji a wayar Turaki tace,"mu yafe maka kake cewa?, ka manta san da kake saka Ummina a ɗaki ka kulle kayi ta dukanta?, ko kuma ka manta san da kake bin ta har waje ka duketa a gaban mutane kana zaginta?, ko manta yacca ka azabtar damu da yunwa kayi?, ko kuma ka manta sheganta ni da kayi da har kake kirana da ƴarka?, to idan ka manta duk waɗannan abubuwan mu ba zamu manta ba, kuma tsakaninmu da sai Allah, da yardar Allah ba zaka mutu ba sai kaga shiga matsanancin halin da yafi wannan". a tsawace Kaka tace da ita,"kul ɗinki Fillo, kar ki ƙara wani furuci anan, wannan lamarin tsakanin iyayenki ne, duk lalacewar uba uba ne shi, uba ba abin wasa bane ki san da wannan, kamar yanda kike ganin mahaifiyarki da mutunci ya zama dole shima ki gansa a mutunci muddin kina son gamawa da duniya lafiya, ke ba dan shi ba ai da baki zo wannan duniyar ba, ki iya bakinki akansa kafin duniya tayi watangaririya da ke". Fillo tasa kuka tana faɗawa jikin Ummi tace,"ni wannan ba Babana bane, shi da ya sheganta ni a duniya ta ya za'ai ya zama ubana, mutumin da ya kasa bani ilimi da tarbiyya shi ne zai zama mahaifina?, ni dai ba Babana ba ne kuma ba zan taɓa yafe masa abunda yay mana ba". tarin da Hayyo ya fara babu qaqaautawa yasa Fillo haɗiye sauran maganganunta tayi kansa da sauri, Kaka tace da Hamid ya tura shi su shiga daga ciki, Ummi na tsaye tana jin zuciyarta nayi mata wani iri tabi bayansu da kallo. cikin ƙanƙanan lokaci dai Hayyo ya fita a hayyacinsa, tari kawai yake yana a basa ruwa ya sha, Fillo ta ɓare jarkan faro jikinta sai rawa yake yi ta zuba a kofi ta tallafi kansa ta basa ya sha, Kaka ta ɗauka lambar Dr Yusuf ta kirasa a waya yace gashi nan zuwa nan bada jimawa ba. cikin mintunan da basu wuce biyar ba Hayyo yasha ruwa yafi roba huɗu, da yasha zai kuma cewa a ƙara masa, kuma duk Fillo ce take basa, idan ta kai kofin bakinsa sai ya haɗa harda hannunta ya kama tukunna yake shan ruwan, hawayenta kuwa dake zuba ajikinsa jinsu yake kamar wuta, in ace ya san haka Ƴaƴa suke da tausayi da jin ƙai da bai wulaƙanta ƴaƴan da Allah yabasa ba balle ya wofuntar da su, bai san Ƴaƴa rahama bane sai da ya shiga wannan halin, lokacin da babu macen da zata kula da shi, haka kuma babu ƴaƴan da zasu zauna su basa kulawa, in ace babu Hamid bai san kuma ya zai yi ba, wataƙila da tuni ya mutu ya ruɓe ba tare da kowa ya sani ba. sai a yanzu da tasa tazo ƙarshe yaji sonsu da ƙaunarsu matuƙa na bin jinin jikinsa, sai yanzu yake jin ina ma ace ba ya zata dawo da ya kyautatawa iyalinsa, babu abinda yake buƙata a yanzu irin ubangiji ya basa aron lokaci, sannan ya ara masa lafiya ko ta ɗan kaɗan ɗin lokaci ne dan ya faranta ran iyalinsa, ya gyara halinsa, ya gyara lahirarsa, to amma ya san ƙarshensa yazo, ba zai ƙara samun wata dama ba a wannan duniyar balle kuma lokaci. yana ta kallon Fillo yana kuka sosai yace,"na karɓi sadakin aurenki tuntuni, na san da cewa hakkinki ne, dole na baki hakkinki, amma saboda son zuciya nawa ban nemeki ba balle na baki, sai na gina kaina da kuɗin motar da na siyar, ban ko fara morarsu ba Allah ya jarabceni da shiga wannan mawuyacin halin, dan Allah ki yafe min kar in mutu da hakkinki akaina". ya faɗa yana kuka sosai. "na san ƙwarai na zalunceku, ba'a taɓa mugun mutum irina ba da ya ƙuntata rayuwar iyalinsa, ban baku ilimi ba balle na baku tarbiya, hasalima duk naƙi karɓarku a matsayin ƴaƴan da na haifa, alhakinku kaɗai ba zai barni in ƙare da duniya lafiya ba, dan Allah ku yafe min ko na sami sassuaci a ƙabarina, kuce kun yafe min ko naga da kyau a ranar gobe". ya kamo hannun Hamid yace,"haƙiƙa banda tamkarka ɗana, Allah ubangiji yay maka albarka, Allah ya saka maka da mafificin alkhairin, ya baka masu kayatata maka fiye da yanda ka kyatata min, fiye da yanda ka dinga kare martabata da mutuncina, na san ba zan ƙara wani lokaci me tsayi ba, idan na mutu ka ɗauk Atm ɗin da na baka ajiya kaje ka ciro miliyan hamsin ka bawa ƴata, hakkinta ne". ya faɗa yana shafa fuskar Fillo, sannan yace,"ka nemi adalin alƙalin da zai raba maku gadonku babu zalunci, duk wata kadara da na mallaka taka ce Hamid na bar maka, na rubuta hakan a takarda ta nan cikin kayana, abinda kayi min ba zan taɓa iya biyanka ba Hamid, na gode, na gode, na gode Hamid, baka taɓa fushi da ni ba, baka taɓa guduna ba saboda mugun halina, matana da ƴaƴana sun guje ni amma kai ɗaya namiji da Allah ya bani kana liƙe da ni, kana faɗa min gaskiya a lokacin da nake da dama amma naƙi saurarenka, Allah yasa ka gama da duniya lafiya, dan Allah yayin da babu ni ka zama uba a wurin ƴan'uwanka, kar ka bari zumuncinku ya yanke, kayi musu gatan da ni banyi musu ba, ka zama na gari Hamid, ka zama na gari, mutum ba ya danasanin zama mutumin ƙwarai har mutuwarsa, amma idan ka zama mutumin da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243