Skip to content
NovelPress

Hausa Novels

Chapter 75

Chapter 75

Lullubin Biri Book 1 Complete Hausa Novel 1,221 words 0 views Progress saved
Download Book

bata daina yinsa ba. ƙafarta kawai take kallo wadda tasha adon sarƙa na gwalagwalai da azurfa, kallon ƙafar tata take yi a zahirance, amma a baɗini ƙafar Alƙali Dikko take kallo, ƙafarsa take kallo tana tuno yanda ta riƙe ƙafafunsa a wancan lokacin tana roƙonsa akan kar ya rabu da ita ya aureta ko da bayan auren zaisa wuƙa ya kasheta, da kuma yadda ya fizge ƙafafunsa ya fita daga ɗakin ya barta ba tare da ya waigo ya kalleta ba, waigen kallon da bai ƙara yi mata ba har yau tsawon shekaru 37, duk da kasancewarta matar Yayansa Mai Martaba Hashim. ta rumtse idonta sosai tana jin zafi a zuciyarta, ganewa ne kawai mutane ba su yi ba, amma zafin so yafi ƙarfin kwatance, ita zata iya cewa zafin so yafi zafin wuta zafi da raɗaɗi, muddin wanda kake so bai bar tasirantuwa a zuciyarka ba. Allah ya sani har duniya ba zata taɓa daina son Alƙali Dikko ba duk da cewar akwai igiyar auren wani akanta, auren ma da har suke da rabon ƴa a tsakani, ƴa me shakaru 21 a duniya, son Alƙali Dikko ba daga gareta bane, so ne daga Allah. taja wani dogon numfashi ta sauke, a sannan ta buɗe ido ta sauke akan ƙaton tray ɗin dake gabanta. Jakadiya Haulat tace,"ranki ya daɗe ki ƙara haƙuri akan wanda kike yi, Allah ya huci zuciyarki uwar gijiyata...yanzu kamata yayi kisha furar nan domin ki samu kiji sanyi a ranki, tun safe babu abinda kika sa a bakinki...batun Hajiya Madina da Ɗan Ramla tamkar tsoma allura ne acikin ruwa, kisa a ranki lokacin kawar da su daga rayuwar Alƙali Dikko yazo ƙarshe, zasu barshi kamar yanda Ramla ta barsa". Fulani tayi murmushin takaici me ciwo, sannan ta ɗago ido ta yiwa Jakadiya kallon tsab kafin nan tace,"ban taɓa yin wani shiri akan Madina ba, kasantuwar nasan Dikko ba sonta yake ba, zatona a lokacin Mai Martaba zai sawwaƙe min daga nan sai na maye gurbin Ramla, ashe duk lissafin da nayi akan hakan da ƙazamin tunani nayi shi...dukkan wani shirina ina yinsa ne akan ɗan Ramla, shirye-shiryen da nayi akan na tarwatsa yaron nan yafi ƙirgen yatsu, sai dai har yanzu na kasa ganewa Jakadiya, na kasa fahimta, na rasa dalilin da yasa cikin tarin ƙullin da nayi akan Turaki babu wanda yay tasiri, amsa ɗaya nake so daga bakinki ba daga bakin boka ba, haka kuma abu ɗaya nake so na sani daga wajenki ba daga wajen boka ba, meke warware aikin Malam?, menene ke warware duk wani ƙulli da nayi?, waye yake lalata min dukkan shirin da nayi?". sai kuma ta miƙe tsaye a fusace, ta ɗaga murya cikin tsawa tana nuna Jakadiya tace mata,"faɗa min gaskiya, kina aiwatar da aikin da na saka ki ko kuma cin amanata kike yi?". cike da tsoro da rawa jiki Jakadiya tace,"wallahi, wallahi Ranki ya daɗe ina sawa a aiwatar da duk abinda kika ce, wallahi kuma ko kaffara ba zanyi ba waɗanda na saka suyi ba zasu ci amanarmu ba, ni kaina ina matuƙar mamakin yanda komai ke warwarewa acikin sauƙi, sai dai ina tunanin ƙarfin adu...". ai tun Jakadiya bata ƙarasa ba Fulani ta ƙara ɗaga murya wajen dakatar da ita acikin tsananin fushi da ɓacin rai,"dakata munafuka, tabbas sai naga bayanki Jakadiya domin babu wanda yake cin amanata na ƙyale shi...karki ƙara buɗe baki kice zaki faɗa min zancen banzan da ba yarda zanyi da shi ba, ƙarya kike yi kice tasirin adu'a zai karya aikin asirin da nake ɓarnatar da kuɗi akai, aikin boka tumbutsu ne ba aikin wani galhonaho ba, bokan da yake aiki tamkar yankan wuƙa, kuma tunda har aikinsa yayi tasiri akan Ramla ƴar Turakin Taraba, bana tunanin aikinsa zai ƙi cin wani tsiyatattan halitta Turaki, don haka kamar yanda na ɗauki alwashin ganin bayan Madina da Turaki a wannan ƙarnin, haka kema sai naga bayanki Jakadiya tunda har kika ci amanta". Jakadiya ta zube gwiyoyinta a ƙasa ta shiga roƙon Fulani cikin tsananin ruɗewa, ana cikin haka Ilham ta turo ƙofar ɗakin ta shigo. cike da shagwaɓa ta faɗa jikin Fulani ta sakin kuka da cewar,"dan Allah Mami ki barni naje, Allah ba zan jima ba zan dawo...sau biyu kenan Hammah Turaki na ciwo bana zuwa na duba shi, kuma yana ta min complain ɗin hakan". Fulani ta tureta daga jikinta, ta fita rai a ɓace daga turakar tata. Ilham ta buta da kallo kafin daga bisani ta zube akan gado tana sakin kuka. tana cikin kukan wayarta ta shiga ringing, ta ɗau wayar tana kallon screen ɗin, ganin sunan Turaki na yawo a jiki yasa ta sakin wani kyakykyawan murmushi sannan ta ɗaga tana cewa hello cike da shagwaɓa. daga ɓangaren Turaki ya sauke ajiyar zuciya sannan yace,"ba ki damu da lafiya ba right?". Ilham ta ƙara narkewa da muryar shagwaɓa tace,"Hammah yau zan zo insha'Allah". Turaki yace,"ba sai kin zo ba, ni gani na zo. ina ɓangaren Abbas...but ba zan jima ki hanzarta". *Comment, Share and Vote.* [8/27, 20:15] Halimahz: *LULLUƁIN BIRI* *©️Halima h.z* _not edited._ *27* Fillo ce zaune akan dakalin bayan ɗakinsu, daga yanda ta zabga tagumi kasan tunanin wani abu takeyi wanda ke damun ranta. ƙwayar idonta ta kaɗa tayi jajir, idon kuma ya ƙara girma. Maijidda ta ƙaraso wajen tana faɗin,"na tsani wannan tagumin naki wallahi". Fillo ta ɗago ido tana kallonta, bata iya cewa komai ba saboda zafin da zuciyarta ke yi mata, tun ɗazu take so tayi kuka ko ta sami relief amma kukan yaƙi zuwa. "kwana nawa kina kuka?, zatonki kuka na maganin damuwa?, to idan baki sani ba kuka baida amfanin komai, damuwarki ya wuci ki kaita gaban Allah, akwai me yaye miki sama da shi ne?, amma sai kiyi ta faman kuka kuma ayi tambayar duniya kiƙi magana, da me kike so Kaka taji?, bafa isassan lafiya ke gareta ba. kuma ke har me kika nema kika rasa a duniyar nan da zaki ɗau damuwa kisawa ranki kina ƴar ƙaramarki, salon dai jawa kai matsala". Maijidda tayi shiru a sanda taji Fillo ta riƙe hannunta gam, tasan ba komai bane illa kukan da take so tayi, ta janyo Fillon jikinta ta kwanta a kafaɗarta, tuni kukan da Fillo ke jira tun ɗazu yazo mata, saida tayi me isarta tukunna ta yakice daga jikin Maijidda tana goge hawayenta. cikin muryar kukan da bai gama sakinta ba tace,"Maijidda ke kike ganin ban rasa komai ba tunda Kaka ta tsaya min, amma a zahirance ni nayi babban rashi tunda har na rasa uba, ba wai don ya mutu ba, yana raye amma na zama kamar banda uba a raye, tunda uwata ta haife ni ban sami soyayyar uba ba irin wacce ko wanne ɗan halak ke samu, ban sami gata ba irin wanda kowanne ɗan halak ke samu daga wurin mahaifi, ban samu tarbiya ba daga wajen ubana, ban sami ilimi ba daga garesa, ban sami kulawarsa ba, ban sami farin ciki daga wurinsa ba balle naji daɗi daga garesa, ya kirani da suna shegiya, ya kirani da ƴar zina alhalin akan shimfiɗar sunnah ya samar da ni...". muryarta ta harɗe tana kifa kanta akan cinyar Maijidda tana ƙara fashewa da sabon kuka. "Maijidda banyi dacen uba ba, ni kaɗai ce

Table of Contents

Chapters

243 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243