Chapter 55
Chapter 55
kike kullum da uzurin da zaki bayar, to ki bar ganin saurayinki ne Allah sai nace ya fara yi miki bulalar makara, wataƙila ki fi maida hankali akan karatun". dariya kawai Fillo tai bata ce komai ba, amma har hangowa take wai Amir zai daketa, tana sonsa dan haka ba zata ƙi tsayawa ba amma shi ɗin tasan ba zai taɓa iyawa ba, ko wani me gangancin yaga zai gwada sai iyakar inda ƙarfinsa ya ƙare. ta fito daga ɗakin sanye da hijab ruwan toka, hannunta kuma tana riƙe ne da qur'ani izu sittin ta rungume shi a ƙirjinta haɗe da dardumar sallah. "na tafi Kaka". Kaka ta ɗago ta kalleta tace,"Allah ya bada sa'a, amma ku gama da wuri kinga Hajiya Madina tace ki koma aikinki yau, kya gaida Amir ɗin kice ina daɗa masa godiya Allah ya jiƙan mahaifa". tace,"tom Kaka". da haka ta fice. daga can bakin gate wurin da ya saba zama ta gansa, a durƙushe a ƙasa da alama ya gaji da tsayuwa ne. bakinsa na motsi yana latsa counter dake saƙale a yatsansa, baƙin yadi ne a jikinsa mai taushi mara tsada wanda ya karɓi jikinsa sosai. ya kuma fito da kyawunsa na usulin bafulatani, sumar nan tasa kwantacciya ta fulani tai luff sai ƙyalli takeyi, da takalminsa da agogonsa dai-dai na me rufin asirin ubangiji. tunda ya ɗaga ido yaga Fillo na tahowa zuwa gare shi kyakkyawan murmushi ya ɓalle a saman fuskarsa, zuciyarsa na ƙara cika da tausayi da soyayyar Halimatunsa, ruhinsa na ƙara buƙatuwa da ƙwaɗaituwar ta zama mallakinsa. a lokacin da ta iso wurin ta sakar masa nata sanyayyan murmushi da yake motsa zuciyarsa. ta durƙusa a gabansa ta gaishesa. Ya amsa yana kasa ɗauke ido daga dogayen yatsunta da ta rufe fuskarta da su, murmushinsa na ƙara faɗaɗuwa. sai da yay gajeriyar ajiyar zuciya sannan yace,"Barka da fitowa gimbiyar Amir, sarauniyar da ta kafa fadarta acikin zuciyar Amir, kazalika uwar ƴaƴan Amir". ta ƙara rufe fuskar da hijab ɗinta, wani daɗi na ratsata. Yay ƴar dariya yana jin tana ƙara burge shi saboda wannan kunyartata. yace,"duk da an hanani ganin fuskar hakan ba zai hana ni faɗin kinyi kyau sosai, matsalar guda ɗaya ce dai da bana so". ya ƙarasa maganar amon muryarsa na sauyawa, tai saurin buɗe fuskarta, so take ta kallesa amma ta kasa, ta sauke idanuwanta a ƙasa da rashin jin daɗi tana jan yatsunta tace,"wacce irin matsala ce?, mecece matsalar da baka so?, a shirye nake da gyara ko menene saboda kai?". ya murmusa kuncinsa sannan yace,"Kunya! itace matsalar kuma itace bana so, amma a iyaka tsakaninmu banda wani daban, sai dai na san ba zaki iya dainawa ba balle ki rage, tunda ba tun yau ba nake roƙon alfarmar a rageta ko ya ya ne saboda tana ƙwarata, amma kamar ma ba'a jin me nake cewa...ni kuma tsakani da Allah ina so ake a bani damar ganin cikin idanuwan gimbiya, ina sonsu, so me yawa ba kaɗan ba". Fillo na murnushi ta ƙara ƙoƙarin sake rufe fuskar sai taga ya haɗe hannayensa alamar roƙo yace,"dan Allah Fillo nah, ki tausayawa zuciyata, ki tausayawa idanuwana". haka dole ta haƙura da rufe fuskar, ba zata iya saka ƙwayar idonta a cikin nasa ba, amma ba zata hanasa ganin fuskarta ba, dan haka ta ɗago kai yanda zai kalleta sosai, amma bata iya barin idonta a buɗe ba ta kullesu. sai da Amir ya ɗauki kusan minti ɗaya yana kallon fuskarta ba tare da ita tai magana balle shi da ya shiga shauƙi. da yana da dama, da yana da yanda zaiyi da yau Fillo bata ƙara kwana a gidan nan ba, da yau Fillo a gidansa zata kwana, kusa da shi, kusanci sosai irin kusancin da zai ɗorata a saman ƙirjinsa ya dinƙa faɗa mata kalaman da zasu mantar da ita duk wani kalar ƙalubale da ta fuskanta a rayuwarta. "ina sonki, ina miki so me tsanani, ƙaunar da nake miki ba mai fasaltuwa bace, bana fatan na rasaki Halimatu, bana fatan Allah ya kawo abinda zai rabani da ke, ke ɗaya ce tal a ƙurya da wajen zuciyata. please ki so ni ko da kwatankwacin yanda nake sonki ne, domin idan babu ke tare da ni Allah babu makawa sai na zama gawa". tai saurin ɗago ido ta kalli raunanun idanunsa. "ina sonka ai kaima kasan da wannan, kuma ba zamu rabe ba insha'Allahu, matarka ce ni har a aljannah insha'Allahu". haka ta faɗa, kuma hakan ke maimaituwa a cikin ransa, maimaituwar kuma ke haifar da jin daɗi tare da shi. da taga kamar yau bai da niyyar suyi karatun muryarta a sanyaye tace,"yau ina da aiki a cikin gida". take annurin fuskarsa ya ɗauke, ya haɗe rai ɓacin rai na ziyartarsa. ya miƙe kawai ba tare da yace mata komai ba ya nufi inda suke zama suyi karatun, baya son wannan aikin nata ya tsane shi. ko wannan karatun da ya tsira yi mata, yayi hakanne dan ya daƙile mata zuwa aikin shi yasa ya saka da safe zasu ke yi, amma ashe na banzar yayi, kamar mayu sun liƙe ita zata ke musu aikin, yanda baya so tai aikin haka baya so Kaka tayi, to amma baida yanda zaiyi, shi ba me ƙarfi ba ne, idan ita ya nemi hanyar hanata bai isa ya hana Kaka tayi ba, to amma me yasa ba zasu nemi wata yarinyar da ta dinga yi musu ba?, su bar masa Fillonsa ta huta kamar a baya. Fillo ta ƙaraso jiki a sanyaye ta shimfiɗa masa dardumar, sannan ta shimfiɗa ɗankwalinta ita kuma ta zauna akai, har sanda ta zauna shi yana tsaye kamar ba zai zauna ba, ita dai bata ɗago ta iya kallonsa ba, saboda hawayen cikin idonta zasu sami nasarar zubowa, ko kaɗan bata son ganin ɓacin ransa, musamman ace itace sila. sai da ya zauna sannan tace da shi,"kayi haƙuri, dole ce tasa ba dan muna so ba mu kanmu. aikin nan shine rufin asirinmu, kana gani Kaka daɗa tsufa takeyi jikinta na ƙara saki, ba zata iya ɗawainiyar da tayi a baya ba, ni kuma da ta riƙe ni bayan banda kowa dole na taimaka mata a yanzu dana kawo ƙarfi, tana buƙatar taimakona. kuma yanzu idan banyi aikin nan mun sami kuɗin ba da me kake so Kaka ta kaini gidanka Amir?". ya tsayar da ƙwayar idonsa akanta yace,"ni ke nake so ba abinda za'a kai ki da shi ba". ta girgiza kai tace,"a'a Amir, duk da bamu da komai, kuma ni ɗin ba kowan kowa bace, amma ina so na wuce gori a ko ina ne. kuma baya nan ina so ko bayan ran Kaka na kalli wani abin da zan gani naji daɗi, na san nima an tafi an bar min gado". yace,"shikenan, bismilillah". ya faɗa yana mata alamar ta fara karatun. tasan maganarta bai masa daɗi ba amma dole ta faɗa, kuma gaskiyar kenan. ba'a san gawar fari ba, kuma ba fata take ba, amma idan Kaka ta mutu, shi kuma ta aure shi shima ya faɗi ya mutu rabo bai samu a tsakaninsu ba, wa take da shi kuma me zata kama?, gwara tai duk kalar wahalar aiki tayi su sami kuɗin da Kaka ke fatan su samu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243