Skip to content
NovelPress

Hausa Novels

Chapter 50

Chapter 50

Lullubin Biri Book 1 Complete Hausa Novel 1,224 words 0 views Progress saved
Download Book

cewa,"Maijidda ce taje take faɗa mana abin da ke faruwa na za'a shiga da ita tiyata, shi ne muka taho. nace ai hakan ma wani gata ne akai mata". Yami tace,"Allah yasa dai ayi a sa'a". ya sosa girarsa leɓensa na fitar da murmushi yace,"ehh likitan ne dama ya bada shawarar hakan". karaf Fillo tayi saurin cewa,"a'a ba shi bane kaine ka fara faɗa masa. ni dan girman Allah Kaka kuyi haƙuri indai abinci ne zanke ci". Kaka tayi mata banza, Yami tace,"to ai magana ta ƙare tunda har likitan ma yayi shirinsa. kiyi adu'a kawai Allah yasa ayi miki a sa'a, hakan ai gata akayi miki Fillo kinga yanzu cikinki ga dinƙa samun abincin kirki. magana kuwa kya dinƙa nuna abunda kike nufi da hannu". Yami na yin shiru Fillo ta fashe da kuka tana kifa kanta a gwiwarta, ta sani babu wanda zaiji tausayinta, kuma babu me jin kukanta tunda bata da uwa bata da uba a raye. Turaki ya ɗauke idonsa akanta, zai fita Kaka tace,"a'a me babban suna tunda dai sa hannunka ne a yin aikin nan to ka ɗan jira likitan yazo a ɗauketa a gabanka. mu ba jin maganarmu take ba,". Tana faɗin haka suka fice su duka suka bar Maijidda a tsaye, itama sai ta fara hawayen. bayan fitar su Kaka ya jawo kujera sosai gaban gadon sannan ya zauna, ya aje wayarsa akan gadon, sannan ya sarƙe yatsunsa wuri ɗaya. yace da ita,"haƙura za'ai da farka cikin ko kukan za ki ci gaba?". kalmar farka cikin ita ke ɗaga hankalinta, tayi saurin ɗagowa fuskarta tayi sharkaf. "dan girman Allah karka sa a farke min ciki, zan dinga cin abinci kullum, ai kana kallo na cinye na ɗazu. dan son da kake yiwa Maama da Adda Zaytuna kace ba za'ai min ba". mamaki yasa kawai ya tsareta da ido, ta ya akai tasan yana ƙaunar mutanen nan guda biyu?, ta ya tasan zai iya yin komai akansu?, wa ya faɗa mata ana roƙonsa da su ya aikata abin da bai niyya ba?. ya sauke numfashi sannan yace,"an fasa". a hankali tace,"na gode, Allah ya kareka daga sharrin maƙiyanka". ta faɗa tana goge hawaye da ɗankwalinta da ya zame. suka haɗa ido tayi saurin ɗauketa nata, ya kalli gashin kanta yace,"ɗaura ɗankwalin ki bani amsar tambayata". Ta ɗaura ya ƙara cewa,"to ki cire tsoron ki nutsu". ta haɗiye wani irin yawu tana saita nutsuwarta. taji yace,"ɗago idonki ki kalle ni". tayi yunƙurin yin hakan amma sai ta kasa, yaci gaba da kallon siraran hannunta da suke ta karkarwa, sai kawai ya miƙa hannunsa ya haɗe hannayenta biyu ya riƙesu cikin nasa guda ɗaya, sai dai da mamakinsa duk da hakan basu bar karkarwar da suke ba kamar ma ƙaruwa abin yayi, cikin ransa ya ayyana duk yanda akayi wannan rawar da jikin nata yake yi bana lafiya ba ne. jin yanda ya riƙe hannuwan nata yasa ta kulle ido wani abu na wucewa ta maƙogoronta. kuma kafin ta buɗe idon taji yace,"me ya kai ki wannan wurin a wancan ranar?". ta buɗe ido ta sauke a saman sumarsa tana jin numfashinta na ƙoƙarin katsewa. **** Yusuf na zaune a office yana operating computer wayarsa tayi ringing, ya kai hannu ya ɗauki wayar, yana duba sunan me kiran yaga Inna Wuro, ya katse tukunna yabi bayan kiran. Inna Wuro na ɗaga kiran ta maka salati,"innalillahii wa'inna ilaihi raji'una. Yusuf kana ina?, kaiwa Allah kazo da sauri babu lafiya". tun salatin farko da ta ja ya miƙe daga kan kujerarsa, tana cewa babu lafiya bai jira komai ba ya kai bakin ƙofa, yabar office ɗin cikin sauri hankalinsa a tashe. daga parlon Inna Wuro ta soke wayarta a gefen zani bayan kiran wayarsu da Yusuf ya katse. ta kalli Nuratu wacce ta tattare carpet ta kwanta a ƙasan tiles, sai yamutsa fuska take yi hannnunta riƙe da tulun ƙasa ƙarami da aka zuba yashi acikinsa, acikinsa take tofa yawu. "ina dalili, gwara ya baro duk abunda yake yi yazo aiwa tufkar hanci, ba zan iya rainon wannan cikin nasa me shegiyar ƙazanta ba. ba ni nayi ciki ba dan haka ba zanyi wahalarsa ba, azo duk abi a dinga tofe min ɗaki da yawu yana ƙarni...yanzu fa fisabillahi ji wani abu, anyi shara kin ɗage min carpet salon dai ayi baƙo a tafi anayi da ni a duniya bana gyara wajena, alhalin ba haka nake ba, kai da gyara wani can da baku haɗa komai da shi ba yazo ya ɓata maka...kuma ni dai gaskiya nake faɗa miki kwanciyar ƙasar nan illa zata miki, inda rabon kin haifo ɗan da sanyi yayi ƙatutu a jikinsa ne ni ba abin da ya dameni ba ne". ta ɗau mayafinta da ke kan kujera ta fita daga parlon, ɗan ƙaramin durstbin na shara ta ɗauka a ƙofar parlon sannan ta wuce ta nufi can inda incilerator yake zata zubar da sharar sai mita take yi. "yanzu ni ba abin na faɗawa Amadu irin cin kashin da ƴaƴansa suke min ba yaga kamar ina tukura musu alhalin nazo ina cin arziƙinsa, Zainabu ta ƙullace ni tace zan haɗa ƴaƴa da ubansu. gwara nayi shiru na haƙura watarana sai labari, amma tsakani da Allah ni ba daɗin hakan nake ji ba, kawai dai dan babu yanda zanyi ne, amma cuta kam ana cutata". ganinta mai gadi ya taso da sauri. "Inna ina za ki haka da kanki?". Ta tsaya tana gyara mayafi tace,"ni ko wa nake da shi da zai min bacin na ƙarfafa jiki na yiwa kaina". ta ɗaga ƙaramin durstbin ɗin sharar tace masa,"kaga dai yanda kwandon nan ya cika ko?". ya ɗaga kai yace,"na gani". tace,"to billahi ina faɗa maka ko dattina ɗaya babu a ciki, bar ganin daga ɓangarena ya fito". Mai gadin yace,"to fa garin ya haka kuma Inna?". tace,"kar ka tsammaci aljanu ne, wallahi ko ɗaya basu da hakki, mutanene marasa tausayin tsoho. Ƴaƴan Amadu ne wallahi, haka suke zuwa su cika min ɗaki alhalin ubansu yayi musu nasu, to ba za su zauna a nasu ba dole dai sai anzo wajena an ɗauki magana. ni kuma bana biye musu kasanni da haƙuri, ban iya ɗaukar magana ba saboda bana son tashin hankali. kuma dai naga gidan na ubansu ne arziƙinsu nake ci shi yasa na iya zamana da su banda haka kullum sai anji kanmu...yanzu fa ka duba ka gani wannan sharar daga safiya zuwa yammacin nan aka tarata, da ci banza ci wofinsu aka mayar min da ɗaki kamar bola. yo ni kuwa me zanyi wanda ya wuci Allah ya isa". Mai gadi yace,"a'a dai Inna haƙuri za'a ci gaba da yi, banda dai Allah ya isan kinga ai jikoki ne". tace,"yo abunda ba ni na haifa ba balle bakina ya bisu su gantale, barni nayi kayata ni dai kam ai Allah ya isar min kawai. kai ai baka san wani abu ba ma, Allah ya isa ai sun saba da ita, dan jiya yaron nan Aliyu ce min yay wai babu wajen shigar tawa, daga nan na sallama nace Allah ya isa kam yanzu na fara har sai tawa ta sami shiga... yanzu ka duba ka gani banda dai rashin tausayi ina uwar me ƙaton gidan nan da kai shara, ko da

Table of Contents

Chapters

243 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243