Chapter 17
Chapter 17
baka lafiya, amma ba dai bada shawarar inda ya kamata akai ka a sama maka lafiya ba, ko kuma maganin da zaka sha...tunda ita Madinar ta ɗauki dukkan yardarta ta ɗora akan bature, yo bature ko gaibu". Zaytuna tace,"Boɗejo asibiti ai ba gaibu bane, yama fi saurin taimakawa lalura". Boɗejo tace,"to ko na asibitin ko na gidan duk wanda akayi ni dai fatana Allah ya ba shi lafiya". Sai kuma ta kalli Turaki tace,"yo kai me ka yiwa mutane suke neman rayuwarka?, gaka dai da kyan hali kuma ni ban san dalili ba, Muhammadu ka faɗa min gaskiya ko dai kana aikata wani mugun abun a ɓoye bamu sa ni ba?". Ya ɗago ido ya kalleta zai yi magana Hajiya Madina ta shigo ɗakin, a cikin wayar da ke kare a kunnenta cikin tsawa tace,"just do as i said! thats all, i don't want that your blabaring". ta ƙarasa bedside drower ta zauna tana dire wayar da ta katse a gefen Turaki, tasa hannu ta ɗan matsa kafaɗar Turakin, yay saurin rumtse ido tare da yin,"ashhhh". Ya faɗa cikin dauriyar zafin ciwon da yaji. "still dai?". ta tambaya. Shi kuma ya ɗaga ma ta kai. Hajiya Madina tace da Boɗejo,"babu wani mugun abu da yake aikatawa, gaskiyarsa ce tayi yawa, saboda yaƙi bada haɗin kai akan wani cuta da mutanen da ke son haɗa partnership da company nasu, bcox hakan zai jawa company ɗin asara babba. shine yasa suke so su kashe shi dan samun biyan buƙatarsu". Baki buɗe Boɗejo ke sauraronta, tana yin shiru tace,"yo ina dalili anan, wallahi sai ya bar musu aikinsu babu dole, dama kai ka ɗorawa kanka ba ce akayi dan kayi karatu dole kaci ribarsa ba, an tara an ajiye muku, ba ku kaɗai ba har ƴan gabanku, to mene kuma na cewar sai anyi aiki a ƙarƙashin wani?, ina su waye masu bibiyar rayuwar taka?". "Boɗejo ai zar...". Hajiya Madina ta dakar da shi daga abunda zai ce. tace da Boɗejo,"zasu shigo hannu ne tunda ƴan sanda na kan bincikensu". Boɗejon tace,"dole ma a binciko ko su waye, dan babu wanda zai yi kasadar shiga rayuwar jinin Sarki Sulaiman Dukko bai fuskanci tsatstsauran hukunci ba...ɗan babban alƙali kuma jikan sarki, a nemi aga bayanka sannan a zuba ido, hakan ba mai yiwuwa bane...aiki kuma ka barshi har gaban abadan". Hajiya Madina tace,"abun da nace nima kenan, to matsalar yana jin sauƙi abin da ya faɗawa uban akai za'a zauna". Baɗejo ta muskuta tace,"ina ce ai na isa ko?, to bari Dukkon ya dawo ya sameni...wallahi sai dai idan bana numfashi amma wannan aiki dai ba zaka koma shi ba, can suje su ƙarata da duk irin asaran da zasu yi, ai ma'aikatar bata ubanka bace balle asarar ta shafeka". Hajiya Madina ta jinjina da kai da jin daɗin hukuncin Boɗejon. sai dai jin sabon furucinta shi yay saurin dakatar da ita daga shafa masa magani da ta ke yi. "aure ma zaka yi, ka wartsake kaje ka nemo matar aure ka kawo mana, cikin ƙaramin lokaci ba da daɗewa ba, abun yayi yawa ace kamarka baka da aure, ga mata da yawa nan a dangi, Allah dai ya baka lafiya". Shirun Boɗejon ya haɗe da walƙiyar wani haske a idon Hajiya Madina, hoton abubuwa da dama suka bayyana acikin hasken. Ta san dai tayi ƙasa da idonta, amma bata san lokacin da murfin idonta ya rufe ya buɗe ba, wucewar sakan 1,2,3, wani abu da ita kaɗai ta barwa kanta sa ni ya dira a tsakiyar zuciyarta. Da daddare Baffa yana dawowa Boɗejo ta same shi da kanta a ɓangarensa, tace zuwa tayi ta faɗa masa Muhammadu ya bar zuwa aikin da yake yi acan Habuja, Baffa da yaso yayi ƙoƙarin fahimtar da ita akan hakan ma da ke faruwa da shi hanya ce ta matakin nasara a rayuwa, kuma ai mutanen ba zasu taɓa samun nasara ba tunda Allah na tare da mai gaskiya a ko yaushe. tace ita dai indai ta isa Muhammadu ya daina zuwa aikin can tunda ba aljanna ake rabawa a wurin aikin ba. **** *8:00am.* Fillo na zaune a uwar ɗaki da ƙur'ani a hannunta tana karatun suratul yasin, taji daɗin jikinta sosai tun aduar da Amir yay ma wancan ranar, da ya je gida haka ya jido mata ruwan adu'oi daga wurin mahaifinsa ya kawo mata, ruwan adu'ar da suka zama na shanta yanzu, shi yasa yanzu sumul ƙalau ta ke jinta kamar bata yi wani ciwo ba. ta rufe qur'anin da ta kai ƙarshen sura, ta tashi ta koma kan katifarsu ta kwanta, idonta na kallon rufin ɗakin. tasa hannu tana shafa kusa da ita wurin kwanciyar Kaka, ji kawai tayi ruwan hawaye ya cika idanuwanta ba tare da ta san da zuwansu ba. tun ƙarfe shida da rabi Kakan ta fita aiki cikin gida, ita ba wai fitar sassafen bace ke damunta, tunda a nan ɓangaren ma ƙarfe shida suke fita, to amma ai anan tana ganin gimlawarta da jin muryarta, amma can idan ta tafi sai dare zata ƙara ganinta. Yunƙurawa tayi ta tashi ta nufi jakar kayanta ta zuge zip ɗin, sai kawai ta zubawa kayan ido, bata san wanne zata saka ba dan yau Kaka ta manta bata ɗauko mata wanda zata saka ba. Kamar zata yi kuka ta shiga ɗebo kayan tana fito da su, kayan duk sun tsufa da yawa, kwana biyu Amir bai yi mata ɗinki ba kasancewar ba shi da kuɗi, kullum haƙuri yake bata. Atamfar ta ɗaya ce me kyan gani ta sallah ƙarama da ya ɗinka mata, kuma da so take sai babbar sallah zata kuma sakata. har tayi choosing wata atamfarta leda sai ta tuna da cewar Amir yace zai zo anjima shi da abokinsa. dan haka sai ta ajiyeta ta ɗauko me sabuntar full cotton ta saka. Ɗinkin riga da skirt ne, ya zauna ɗas ajikinta, rigar ta kwanta a shafaffen cikinta, breastcuff ɗinma yay dai-dai da breast ɗinta maidaidaita, ƙafar nan tata ƴar sirit acikin skirt ɗin. kayan ta maida ta ɗauki ɗankwalin ta fita, wurin Maijidda zata je tayi mata ɗauri irin wanda ta taɓa yi mata Amir yay ta santinsa. don ita ba iya ɗaurin ɗankwali tayi ba, tafi gane ta saka hula akanta. Tana fitowa su kai kiciɓis da Kaka ta dawo, da mamaki ta ke kallon Kakan, wadda kana gani kasan cikin ƙarfin hali take. Saurin riƙeta tayi suka shigo ciki, Kaka ta zauna ta riƙe kanta da taji yana sara mata sosai. "sannu Kaka, ni dama tun jiya nake cewa ba kya jin daɗi kika dage min ke lafiya kike". Fillo tayi maganar kukan da ke bakinta na shirin fitowa. Kaka tace,"ni ƙalau nake...ciwon kai ne kawai, kuma ina shan magani zai daina". Cikin sauri Fillo ta miƙe ta shiga ɗaki ta ɗauko panadol da ruwan adu'a da take sha ta kawowa Kakan. Kaka ta karɓa tasha sannan ta kwanta ta rufe idonta kamar mai bacci. Fillo dai kallonta kawai take yi, tsoro da fargaba fal ranta, idan mutuwa tayi mata haka ya zata yi?, ina zata kama?, wa zai zama gatanta?, shikenan sai ta dawo ainihin maraniya ta gaske. Hannu tasa ta goge hawayen da ya sakko mata, ta kama hannun Kaka ta riƙe gam. Kusan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243