Skip to content
NovelPress

Hausa Novels

Chapter 152

Chapter 152

Lullubin Biri Book 1 Complete Hausa Novel 1,227 words 0 views Progress saved
Download Book

wasu suke kuka da shi zaka yi danasani a sanda kazo mutuwa har bayan mutuwarka, Allah yasa ka gama da duniya lafiya". Hamid ya kasa cewa komai yana dai riƙe da hannunsa yana hawaye, Hayyo na shaƙuwa ya kalla Fillo yace,"zan ƙara ruwan me sunan Umminta". Fullo ta ɗago kansa ta kuma basa ruwan yasha, a lokacin sai da ya shanye jarkan guda, yana kallon Fillo yana murmushin ƙarfin hali yace,"ki tayani roƙon yafiyar mahaifiyarki, ki faɗa mata ina sonta, ina sonta fiye da yadda baki zai furta, dan Allah ta yafe min ko na na samu naga haske a ƙabarina". yana faɗar hakan kansa ya langwaɓne gefe yana shaƙuwa sosai, ya dafe ƙirjinsa yana jin tsananin azaba na ratsa shi, magana yake so yayi amma shaƙuwa sam ta hana shi, can kuma sai ga jini yana fita daga bakinsa kamar zubar yawu, ya damƙo hannun Fullo da Hamid yace,"tawa tazo ƙarshe, ba zan ƙara ko da minti uku ba, mutuwa zanyi ƴaƴana, bana so na tafi na barku amma ban isa na hana mutuwa ta ɗaukeni ba, ba'a son raina zan rabu da ku ba sai don mutuwa ta zama dole a gareni ko ba yanzu ba, idan na mutu ku nema min gafarar Allah, karku gushe face kuna me nemar min gafararsa a ko da yaushe, haƙiƙa ni ɗin me laifi ne a gare shi, mutuwa zanyi babu makawa, iyayena sun rasu tun ina saurayi, baƙin cikina ya zama ajalinsu, ku nemi dangina a ƙauyen Ngurore-Jabu under local government ɗin Karim-Lamiɗo, Wurkum district gidan Hakimin Wurkum, nanne gidanmu, anan ahlina suke, Allah yayi muku albarka, dan Allah kuce da mahaifiyarku ta yafe min, la'ila ha'illahu muhammadurrasulillahi sallahu alaihi wassalam". ɗif kamar ɗaukewar wuta haka numfashin Hayyo ya ɗauke, hannunsa ya saki ya faɗi daga riƙon da yaywa yaransa, Kaka ta fashe da kuka tace,"shikenan, Hayyo Allah ya jiƙanka yay maka rahama yasa can tafi nan". Fullo ta ƙwala wata ƙara tana jijjiga shi,"Abba nah, Abba don Allah ka tashi, Abba kar ka mutu, Abba kar ka tafi ka barmu muna buƙatarka, wallahi mun yafe maka duk abinda kayi mana, dan Allah ka tashi Abba nah, muna sonka a yanda kake Abba ka tashi please". Hamid dai kukansa a hankali yake yi, shi ɗaya yasan me yake ji a zuciyarsa, Kaka ta tashi ta fita dan kiran Ummi idan bata yi nisa ba, tana fitowa ƙofar parlo ta tarar da ita a tsaye tana goge hawaye da mayafinta, ta kalleta tace,"ya mutu ai". wasu sabbin hawaye suka ƙara zubowa a fuskar Ummi, Kaka ma ta goge nata tace,"ki shigo ciki asan abin yi kafin dare yayi, anan za'ai jana'izarsa ko sai mun koma can?, in sai mun koma can dole sai gobe za'a kai shi tunda kinga daren yayi, in kuma nan ɗin ne to na shiga masallacin can na faɗa in yaso ko bayan magriba sai a kaishi". kukan da Ummi ke ta riƙewa ya kubce mata, ta fashe da kuka sosai ta shiga parlon da gudu ta tafi kan gawar Hayyo, wanda take kallonsa kamar zata yi masa magana ya amsa mata, ta kifa kanta a ƙirjinsa tana riƙe hannunsa, kukan da bata taɓa yi ba a duniyarta yazo mata, da ƙyar muryarta ta samu ta fito acikin kukan tana cewa,"na yafe maka, Allah ya yafe maka, Allah yasa ka huta, ubangiji ya lulluɓeka da rahamarsa". lokaci ɗaya parlo ya karaɗe da kukan uwa da ƴaƴanta, zuciyoyin da su kaɗai suka san me suke ji, duk rashin kyan halin mutum yayin da akace babu shi mutuwa ta ɗauke shi sai mutuwarsa ta taɓa zuciya musamman makusantansa, ji suke yi inama zasu iya dawo da shi suci gaba da rayuwa tare da shi a yanda yake. kukan da Fullo da Hamid ke yi ya ƙara tsinkar da zuciyar Ummi, kuka sosai babu me iya lallashin wani, lokacin kuma Dr Yusuf ya shigo parlon, da Yami ya fara cin karo, yana kallonta jiki a sanyaye yace,"lafiya Yami?, waye babu lafiya?, ba dai jikin Ummi bane ya tashi?". tana goge hawaye tace da shi,"a'a ba ita bace, wanda ma aka kira ɗin kazo ka duba shi Allah ya karɓi abinsa". ya kalla wurin da su Ummi suka kewaye gawar sannan ya kalla Yami yace,"ban gane ba Yami?, waye mutu?". tace,"Baban Fullo ne yazo, kuma ashe ajali ne ya kawo shi". Yusuf ya isa wajen da sauri, sai dai yana zuwa fuskar da ya gani ita ta matuƙar basa mamaki har ya razana yaja da baya, ya kalla Ummi ya kalla su Hamid yace,"waye wannan ɗin?". babu wanda ya iya basa amsa acikinsu, ya dinƙa kallon Fullo dake aikin girgiza Hayyo tana faɗin dan Allah Abba ka tashi, ka tashi mun yafe maka kar ka mutu yanzu. Yusuf ya zube a wajen hoton gawar Hayyo da hoton Kawunsa Muhammad da ya sani na haska masa a ido. a fili ya furta,"Kawu Muhammad". sai kuma yasa hannu a aljihu ya ɗauko wayarsa ya kira lambar Ammi, har ta ƙare ringing bata ɗaga ba sai da ya kira lambar Aliyu yace ya kai mata. murya a daƙile tace da shi,"ya akai?". yace,"Ammi Kawu Muhammad". tace,"me ya sami Kawu Muhammad ɗin?, ganinsa kayi?". kamar yana gabanta yace,"Ammi ya mutu". a matuƙar razane ta miƙe jiki na kyarma tace,"ya mutu?, aina ka gansa da zaka ce ya mutu?, yaushe rabonka da shi ma har da zaka ce ya mutu?, wa ma ya san inda yake?". yace,"to ban sani ba Ammi ko idona ne yake gane min ba dai-dai ba, amma tabbas gani ga gawar Kawu Muhammad, zan tura address kizo yanzu ki gani ko shi ɗinne, amma na tabbata gawar Kawu Muhammad ne a gabana". Ammi ta jefar da wayar Aliyu tayi cikin ɗaki da sauri ta ɗauko mayafi tace da shi,"muje muje Aliyu, duba wayarka Yusuf zai turo da address". cikin mintunan da basu haura ashirin ba sai ga su Ammi sun ƙaraso gidan, ta shigo parlon duk a rikice tayi kan gawar da aka lulluɓeta a yanzu, ta kalla Ummi da su Fullo da babu abin da ke tashi a parlon sai gunjin kukansu, ta kai hannunta na kyarma ta ɗaga zanin da aka rufe shi da shi, tana kallon fuskarsa ta saki zanin ta zabura taja da baya tana ambaton ƙalu innalillahi... sai kuma ta fashe da kuka sosai tana faɗin,"ashe rabon ba zamu ƙara ganawa ba sai bayan ka mutu zanga gawarka Yaya". ta kalli Ummi tace,"mijinki ne da gaske?". Ummi da mamaki take kallonta ta ɗaga mata kai kawai, Ammi tace,"Yayana ne uwarmu ɗaya ubanmu ɗaya, tunda ya zama ajalin iyayenmu shikenan kuma ya kama gabansa bai ƙara waiwayon kowa ba, rabona da shi tun Yusuf bai fi shekara goma sha ɗaya ba, yazo gidana sau ɗaya lokacin ko sauraronsa banyi ba". tayi shiru tana bin gawar da kallo tana kuka sosai, "Allah ya jiƙanka Yaya yasa ka huta, Allah ya yafe maka zunubanka, ya haskakaka ƙabarinka, Allah ya sadaka da manzon Allah SAW". nan da nan kuma sai ta ɗauki waya ta shiga kiran ƴan'uwanta waɗanda suke uba ɗaya, dama su biyu ne a wurin mahaifiyarsu daga shi sai ita, duk da irin fushin da aka ɗauka da Hayyo hasalima wasu sun manta da shi, amma kan kace mene

Table of Contents

Chapters

243 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243