Chapter 84
Chapter 84
ɗauke tasa acikin rigarta. taji yace,"ni zan shanye sauran maganin?". ta buɗe ido ta ɗauki ledan da yay mata nuni da shi, cike da ƙaguwar ya sakar mata hannu. tace,"wa zan kaima?". yana sakin hannunta yace,"ki wuce da shi". tace,"ina?". yace,"duk inda kika ga dama". tana hararsa ta ƙasan ido tace,"ƙofan a rufe yake". ta faɗa tana yamutsa fuska. ya miƙe yaje ya buɗe ita kuma ta fice da gudu, wannan gudun nata kuma yasa shi sakin gajeran murmushi yana girgiza kansa. cikin sanɗa ta fita daga side ɗin nasu gaba ɗaya, ko tsayawa ba tayi ba a compound tayi ɓangarensu dan bama taso su haɗu da Maama a yanzu, sai safiya kuma. sai after take jin wani mugun ƙamshi me shegen daɗi na binta, ta dinƙa jan hanci tana so taji daga ina ne, sai da ta shinshina jikinta taji ƙamshin a jikinta yake. tsabar daɗin ƙamshin nunfashinta har kusan sarƙewa yayi, tana tafe tana lumshe ido har ta kusa zuwa ɗakin Yami. aina ta samo wannan ƙamshin to?, ƙamshin da zata iya ce duk duniya babu ƙamshin da ya kaisa daɗi. idanuwanta a lumshe ta ƙaraso ƙofar ɗakinsu, lokacin Maijidda ta fito daga ɗakin suka yi karo da juna. Maijidda ma taja hanci tana shaƙar ƙamshin tare da cewa,"kai Fillo wannan ƙamshin fa?". **** Boɗejo dake zaune kan kujera a babban parlon Mai Martaba tace,"ah tou ni ɗin dai na gama magana...idan kuma kun lalace ne to sai naji, amma batun auren Ilham da Ɗan'uwanta wancan kumburarren babu wanda ya isa ya hana sai dai ko bayan raina, sai in kuma ikon me sama". Mai Martaba ya sauke numfashi yace,"amma Hajjah...". da sauri ta katse shi,"Hashim kai kaɗai ne me shegen taurin kan da ba zaka tuba ka daina kirana da Hajja ba ko?, kasan Allah karka bari raina ya ɓaci akanka, ya nazo ina batun haɗa yara aure kana ce min ba haka ba yanzu kuma kana ƙara kirana da sunan da kasan bana so". cikin kwantar da murya Mai Martaba yace,"kiyi haƙuri". Boɗejo ta ƙara haɗe rai tace,"ka riƙe haƙurinka. muyi batun da ya kawoni wajenka, ba tun yau nake faɗa ba sai dai zan ƙara nanatawa ina so ku haɗa Muhammadu da Rumana aure, in kuma ban isa ba sai inji". Baffa ya ɗago kai ya kalleta yace,"balle ma kin isa Boɗejo, sai dai kawai ya kamata ayi duba a lamarin, tunda bamu san ba ko su yaran nan zasu so haɗa su auren da za'ai". Mai Martaba yace,"abinda nake so ki fahimta kenan Mama, zamanin yanzu ba ɗaya bane da na da, yanzu ba'a haɗa yara aure gudun abinda ka iya zuwa ya dawo a zamantakewar tasu muddin babu soyayyar junansu, amma kuwa idan aka tabbatar da yaran nan suna son junansu shikenan salamun alaikum mu kanmu ba ƙaramin farinciki zamu yi da hakan ba". Boɗejo ta tafa hannu tana salati kafin tace,"na shiga uku, Hashim yanzu al'adar tamu zaka rushe?, kai kasan a yanda akayi aurena da ubanku kuwa?, tabɗijam, to da kasan ta yanda aka laliƙa min ubanka na aura da baka zo min da wannan ƙabali da ba'adin ba...shashashan sarki kawai, kai idan akai hakan ma ba ƙarfafa zumunci akayi ba, amma kana batun wani idan basa son junansu, a'a to da ƙiyayyar junansu suke yi?, ko an faɗa muku su irin ƴan'uwan mahaifinku ne kafin su tuba, kai gaskiya Hashim kana da gurɓataccen tunani, wai idan basa son junansu!, maganar nan naka har ga Allah yayi min zafi, to karka ƙara wallahi, don ni dai kaf jinina babu me mugun hali, kowa son ɗan'uwansa yake yi...tsakani da Allah ina Turaki zai ce baya son Ilham ƴar'uwarsa?, kuma itama ta ina zata ce bata sonsa yarinyar da kullum zancenta akansa yake, babu fitowar rana da faɗuwarta da ba zata ambaci sunansa ba, dan ma dai waccan uwar tata me baƙin hali da mugun nufi na hanata zumunci da shi, to a gaskiya indai ana so aga dai-dai abi umarnina kawai, auren nan yinsa za'ai babu wani zaman tuntuɓe-tuntuɓe balle asa jinina ya hau". Mai Martaba zai yi magana ta ɗaga masa hannu,"a'a dakata, dakata ba sai kace komai ba. ɗaga waya kawai ka kira min Hakimi yazo yanzun nan, ban sani ba ko haɗe kanku kuka yi kuke so ku nuna min kune kuka haifi yaran nan, ni banda wani hurumi da su, in haka ne kuwa sai in kama gabana na barku da halin bijirewa maganata". Baffa ya tausasa murya yace,"ba bijire miki zamu yi ba Boɗejo, zamani muke so ki duba. kuma muma fa bamu ce ba za'ayi hakan ba, ce muka yi a fara jin ta bakinsu tukunna, idan sun amince da junansu mu abin farinciki ne a wurinmu wallahi". Boɗejo ta jijjiga kai ta harɗe ƙafafu tace,"to bara kaji Dikko, tunda uwata ta haifeni ban taɓa ganin Ubanku ba sai a ranar da aka kirani akai min zancen aurenmu da shi...ina zaune lafiya daga zuwa na gaida mahaifiyata zanyi kwana uku a wurinta sai Kakanku yasa Babana ya doka min kira wai inje fada ana nemana, kai kasan tashin hankalin da mahaifiyata ta shiga a dalilin wannan kiran kuwa?, saboda kiran fada bai cika zama alkhairi ba, ina zuwa ga Babana Waziri ga Mai Martaba ga Ubanku a zaune aka ce ga mijin da akayi min, kuma a gobe za'a ɗaura mana aure. yo da ike ni me biyayya ce ban bijire ba daga ni har shi uban naku, hasalima shi tausata yake yana cewa muyi haƙuri mubi umarnin iyaye zamu ga ribar hakan, to dana aure shi Dikko mutuwa nayi ko me?, gashi nan dai ku huɗu na haifa jeras tare da shi, idan bana sonsa zan bari a haife ku ne?. sai akan ƴaƴanku zaku ce ba haka ba, Turakin ma da wancan algungumar Azimar ta raine shi, Turaki fa har goya Ilham yayi, to banda dai rashin tsoron Allah irin naku ina ku ina cewa baya sonta? ku dai ku ke kyautata zato akan abu, ba wai kowa yake hasashe mara kyau ba. na tabbata babu abinda zai sa yarannan suƙi amincewa muddin kun nuna musu kuna so, banƙi ba shi ɗan naka ya iya botsarewa to amma shima na san na ƴan mintina ne tunda yana da ladabi, kana cewa haka kake so ba zai ja ba zaice ya amince, sai dai idan kuma a munafurce ni a hure musu kunne". daga Baffa har Mai Martaba babu wanda ya ƙara yin magana, Boɗejo ta tafa hannu wani bafade ya shigo parlon yana zubewa a ƙasa. tace,"maza kira min sarkin gida". fitarsa babu jimawa sai ga sarkin gida ya shigo, ya zube agaban Boɗejo tace,"ɗau waya ka kira min Hakimi". Sarkin gida ya kira wayar Hakimi da wayar Mai Martaba, bugu ɗaya biyu ya ɗaga. yay saurin miƙawa Boɗejo. ta karɓa tasa a kunne, bayan sun gama gaisawa tace,"kana jina?". a ladabce yace,"ina jinki ranki ya daɗe, Allah ya ƙara miki lafiya da tsawon rai". tace,"amin, Allah yayi maka albarka...dama magana zanyi da kai". kamar yana gabanta saboda tsananin ladabi yace,"tom shikenan, ɗazu ance min kin fita, gidan Dikko zanzo ko fada?". tace,"a'a yi zamanka akan kujerarka. dama batu ne na aure nazo maka da shi, ina so a haɗa auren Turaki da Ilham,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157
- 158 Chapter 158
- 159 Chapter 159
- 160 Chapter 160
- 161 Chapter 161
- 162 Chapter 162
- 163 Chapter 163
- 164 Chapter 164
- 165 Chapter 165
- 166 Chapter 166
- 167 Chapter 167
- 168 Chapter 168
- 169 Chapter 169
- 170 Chapter 170
- 171 Chapter 171
- 172 Chapter 172
- 173 Chapter 173
- 174 Chapter 174
- 175 Chapter 175
- 176 Chapter 176
- 177 Chapter 177
- 178 Chapter 178
- 179 Chapter 179
- 180 Chapter 180
- 181 Chapter 181
- 182 Chapter 182
- 183 Chapter 183
- 184 Chapter 184
- 185 Chapter 185
- 186 Chapter 186
- 187 Chapter 187
- 188 Chapter 188
- 189 Chapter 189
- 190 Chapter 190
- 191 Chapter 191
- 192 Chapter 192
- 193 Chapter 193
- 194 Chapter 194
- 195 Chapter 195
- 196 Chapter 196
- 197 Chapter 197
- 198 Chapter 198
- 199 Chapter 199
- 200 Chapter 200
- 201 Chapter 201
- 202 Chapter 202
- 203 Chapter 203
- 204 Chapter 204
- 205 Chapter 205
- 206 Chapter 206
- 207 Chapter 207
- 208 Chapter 208
- 209 Chapter 209
- 210 Chapter 210
- 211 Chapter 211
- 212 Chapter 212
- 213 Chapter 213
- 214 Chapter 214
- 215 Chapter 215
- 216 Chapter 216
- 217 Chapter 217
- 218 Chapter 218
- 219 Chapter 219
- 220 Chapter 220
- 221 Chapter 221
- 222 Chapter 222
- 223 Chapter 223
- 224 Chapter 224
- 225 Chapter 225
- 226 Chapter 226
- 227 Chapter 227
- 228 Chapter 228
- 229 Chapter 229
- 230 Chapter 230
- 231 Chapter 231
- 232 Chapter 232
- 233 Chapter 233
- 234 Chapter 234
- 235 Chapter 235
- 236 Chapter 236
- 237 Chapter 237
- 238 Chapter 238
- 239 Chapter 239
- 240 Chapter 240
- 241 Chapter 241
- 242 Chapter 242
- 243 Chapter 243