Skip to content
NovelPress

Hausa Novels

Chapter 77

Chapter 77

Lullubin Biri Book 1 Complete Hausa Novel 1,226 words 0 views Progress saved
Download Book

yayi min ba?". Maijidda tace,"ni ba abinda yace min, kuma bana so na sani tunda har ke kika kasa faɗa min, abinda nake so kawai shine ku dawo daidai komai ya wuce..". Fillo tai saurin tarar numfashinta,"har gaban abadan, igiyar soyayyar da ke tsakanina da shi na datseta har mutuwa, kije ki faɗa masa hakan, in ma yana wani lissafin rayuwa tare da ni ne to ya daina deceiving kansa, domin ni Halima na barsa har gaban abadan, wallahi ko Amir ne kaɗai ya rage namiji a duniya ba zan auresa ba". sai kuma ta fashe da kuka,"idan har da gaske Amir sona yake tsakani da Allah ba zai taɓa goranta min ba, duk da banga laifinsa ba. laifin Hayyo ne da ya sheganta ni da bakinsa, in ace Hayyo bai kira ni ƴar Zina ba yau da Amir bai buɗi baki yace min ƴar gaba da fatiha ba...". furucinta na ƙarshe yasa Maijidda tayi zumbur ta miƙe,"kika ce me?, Amir ɗin ne ya faɗi haka?". cikin matsanancin kuka tace,"Allah shahida idan nayi masa ƙarya Allah kar ya ɗagani anan wurin, kije ki tambayesa. daga nace bana so naje gidansa babu kayan ɗaki gudun gori shi ne ya tashi ya juya min baya yana faɗa min wai kar na manta ni ƴar zina ce, saboda haka ko ba'a min gorin kayan ɗaki ba ana iya min gorin an haifeni without marriage. Maijidda wanda nake so da aure ya faɗa min haka tun ban auresa ba, just imagine anyi auren, waɗannan kalamai kike tunanin zai dinga gaya min?". Maijidda ta sauke numfashi da matuƙar mamakin ace Amir ne zai faɗi haka. ta rasa abin faɗa saboda tayi matuƙar girgiza, idonta kawai Amir ɗin yake hango mata, bata taɓa tsammanin zai iya faɗawa Fillo haka ba saboda bala'in son da yake yi mata. Fillo dai kuka kawai take yi babu ƙaƙƙautawa, har sai da wayar hannun Maijidda tayi ƙara ta ɗaga suka gaisa da Dr Yusuf yace musu ga shi a waje, sannan Fillo ta goge hawayenta ta shi suka tafi bayan ta wanke fuskarta. *** A ɓangaren Bello, Turaki da Khalil. zaune suke a parlo bayan sun kammala breakfast, kowanne da takardu a gabansa da kuma biro, suna tattaunawa akan batun sabon company da Baffa yace za'a ƙara buɗewa. Khalil na kallon takardar dake gabansa yace,"anawa tunanin gaskiya gwara a buɗe na sarrafa kayan miya a maida su na gwangwani ko leda. tunda shine kamfanin mafi ƙaranci da muke da shi a nigeria, kuma ina ganin hakan za'a sami abinda ake so fiye da tsammani". Bello yace,"view ɗinka yayi kyau, sai dai yanzu mu fara kammalawa da wannan da Maama tace". Turaki ya kalli Bello tace,"me Maaman tace?". Bello ya duƙa yay rubutu jikin takardar gabansa tukunna yace,"Company ɗin dake Lagos da Baffa yace a siyar, tace ba za'a sayar da shi ba za'a maida shi na fulawa, Shine batun da nai muku jiya cewar zanje Hong Kong, saboda injinan da za'a siyo na yanda za'a sarrafa fulawan. but ina ganin tafiyan ba ni ɗaya zanje ba da kai zamu tafi Turaki, zanyi convincing Maama mu tafi tare. tunda tafiyan jirgi ne ba wai a mota ba, becouse kai ka fini sanin kaya masu kyau, idan ni ɗaya ne za'a iya haɗani da fake one". Turaki ya ɗan ciji leɓensa kaɗan sannan yace,"why not su turo da kayan kawai ba sai anje ba". Bello yace,"yanda ma fake one's ɗin zasu fi zuwa kenan. Maama already ta riga taga hotunan su, dan ko launching nasu ba'ayi ba, shisa tace naje ayi a gabana, so ta re da kai dai zamu tafi". Khalil yace,"shikenan Turaki Flour Mills ya tabbata kenan, dan nasan hakan za'a saka tunda Maama ce ta kawo idean". Bello da sigar tsokana yace,"ah haba dai sai kace shi ɗaya ne ɗa, ai sai dai a haɗa sunan mu duka". Turaki ya taɓe baki ya miƙe tsaye yana faɗin,"i don't think i will go with you, kayi tafiyanka kawai ko kuma kuje da Khalil. beside; Sameer ma na Hong Kong ɗin kana iya samunsa acan". Bello yace,"aiko dole sai kaje, ka zama cikin shiri kawai Malam, coux daga nan ma tictiket ɗinmu zanje amsa". ba tare da Turaki ya ƙara cewa komai ba ya fice daga parlon. direct part ɗin Boɗejo ya nufa, acan ya tarar da sisters nasa duka a zaune sun saka Boɗejo a tsakiya sai hira suke, sai bayan ya zauna kan kujera ya fahimci lissafi suke tayi, lissafin aurensa. Samha cikin zumuɗi da tsananin murna take faɗin,"ai Boɗejo babu zancen wani 1week, biki zamu fara from day 1 to day 10, kuma kowacce rana sai mun zubar da naira, sai doller tayi kuka ita kanta sai ta san ana bikin first born a gidannan". Nihal ta taso a kusa da Boɗejo ta dawo kusa da Turaki, ta kamo hannunsa tana cewa,"please Hammah ka sama mana Anty kaji, Allah mun ƙagu ayi bikinka, Allah duka burinmu na kan wannan ranar Hammah, I feel like your wedding day is the first wedding in the world". shima ya riƙe hannun nata yana kallon innocent face ɗinta yace,"to kun zaɓa min matar ne?". dai-dai nan Samha ta taso itama ta zauna gefensa,"ka yarda mu zaɓa maka Hammah?, akwai friends ena da friends Zaytuna da yawa da suke sonka, duk basa ƙasar nan, gasu kyawawa masu class, sai wacca muka ɗaukar maka". tana kallon Zaytuna tace,"ina wannan balarabiyar ƙawar tawa da mukai vedio call ranar nan?, kin tuna ta?, basu dace da Hammah ba don Allah?". bata jira cewan Zaytuna ba koma garesa tana ƙara cewa,"Hammah ka yarda muyi maka zaɓi?". ya kalleta sai kuma ya kalla Zaytuna wadda ke ta kallonsa da tarin murmushi. kamar ba zai ce komai ba sai kuma yace,"kuyi adu'a Allah ya kawo ta gari, aure ai lokaci ne". Boɗejo tace,"a'a lokacinka fa yayi kai harma ya wuce tuni, dan dai kawai Uwarka da Ubanka sun zuba maka ido ne, sai abinda kake so za'ai, yo wannan gata ai ba gata bane. kai in baka san mutumcin mutum aure ba ai su sun sani, to ni dai ina gajiya sai na haɗaka da duk wadda naga dama, Allah na tuba ƴan mata gasu nan birjik a danki...kuma dai ma ni in faɗa maka yar gida muke so jinin sarauta ba bare ba, ah tou karma lokacin da hankalinka zai dawo jikinka kace zaka ɗauko wata can daban, ina ga Madina ce kawai ta shigo zuri'armu a bare". shi dai bai ce komai ba ya jinginar da kansa jikin kujerar. Nihal ta daɗa riƙe hannunsa sosai tana faɗin,"can't wai to see your wedding day Hammah, wayyo Allah wa ya ganni da Sister inlaw". ta faɗa cikin wani irin expression tana faɗawa jikinsa. ranar a part ɗin Boɗejo suka yi lunching, shi Turakin ma bai iya cin komai ba, yanayinsa kamar dai wanda bai cikin natsuwarsa. after la'asar ma da ya dawo daga masallaci part ɗin Boɗejo ya koma, lokacin da ya shiga bedroom nata tana waya da Inna Falmata. ganin shigowar tasa yasa tace,"to sai anjima Falmata, a dai ci gaba da aiki me kyau don Allah, kinga acikin sati huɗu yau munci kwana biyar, to shi haka lokaci yake sai dai idan ba'a saka shi ba, nan

Table of Contents

Chapters

243 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243