Skip to content
NovelPress

Hausa Novels

Chapter 224

Chapter 224

Lullubin Biri Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
Download Book

kowanne rai, wacca bata da wani banbanci a tsakanin me kuɗi da talaka, babba ko yaro, me mulki ko mara mulki, ita ce wacca bata barin wani don wani yaji daɗi. sau tari ɗan Adam kan zauna yay ta tunanin yaushe ne zai mutu?, kuma ai na?, taya zai mutu ɗin?, mene zai iya zama ajalin nasa?, sai dai waɗannan tambayoyi babu wani mahaluƙi da yake da amsar su, mutuwar ce kawai take zuwa da kanta, walau ɗan Adam ya shirya mata walau bai shirya ba, ko ana so ko ba'a so, da zarar ta zo tafiya kawai ake yi, ta datse wannan numfashin da bawa yake fitar da shi, acikin jin daɗi wa ko akasin hakan. mutuwa ita ce kaɗai abar da ke iya yanke ƙaunar da ke tsakanin uwa da ɗanta, ko miji da matarsa, ko masoyi da masoyiyarsa, ko aboki da abokinsa. ta kan zo ne bagatatan ba tare da ta sanar ba, sau tari mu kan kasance tare da mutum, kuma a yayin da aka sami giftawar wani lokaci bayan rabuwar mu sai muji ance wane ya rasu, ko kuma wane ya mutu, a lokacin ne zamu yi tunanin me ya sami mutum?, taya za'ai ace ya mutu bayan muna tare a ɗa zu muna hira cikin wasa da dariya?, to ita mutuwa haka take, ta kan ɗauki bawa ne da lafiya ko ba lafiya, kuma a lokacin da wani ke kan hanyarsa ta zuwa duniya, a lokacin mutuwa ke ɗaukar wani ta raba shi da wannan duniyar duk son da yake yi mata kuwa, hakana duk son da ake yi masa. in ace mutuwa zata bar wani don wani yaji daɗi, da tabbas bata raba ɗa da mahaifiyarsa ba a lokacin da yake zuwa duniya ba, wata uwar kan samun damar ganin yaronta kafin mutuwar ta ɗauketa, yayin da wata yaron na fito ita kuma zata yi sallama da duniyar. a lokacin da aka ce mutuwa ta raba mu da wani mutum da yake sashi na jikin mu, ruɗewa da tsananin shiga tashin hankali tare da fitar hayyaci kansa mu gaza yarda da cewar an mutu ɗin, anyi tafiyar da babu dawowa, har ta kai ga ba ma gama yarda da cewar tabbas mun rasa wannan da muke jinsa wani ɓangare na jikin mu, har sai lokacin da aka ɗauki gawarsa acikin makara, aka tafi da ita zuwa maƙabarta, aka kama gangar jikin aka zura acikin ramin ƙabari, har a jera tukwane akan gawar, da ƙasar da za'a zuba akan tukwanen, sannan a shafe hasken farin likkafanin dake lulluɓe da gawar. a sannan ne zamu yarda da tabbas an tafi, an yi tafiyar da ba za'a sake dawowa ba, tafiyar da ba zaka ƙara ganin mutum ba sai a lahira, har ko da yaushe fatan guda ɗaya ne, mu mutu muna masu aikata alkhairi, mu zama masu cikawa da imani, mu zamto mun mutu ana yabon mu. a lokacin da kumburarrun ƙafafuwanta ke sakkowa daga matattakalar benen a hankali, a lokacin take jin wani baƙon yanayi yana ziyartarta, a lokacin take jin wani abu da bata saba jinsa ba, wani irin yanayi ne take jinta a ciki, wanda ya ke zarcewa har can ƙasan zuciyarta, ya motsa zuciyar tare da abin da ke cikinta. sai a lokacin da ta isa parking lot, tasa key ta buɗe motar, sannan ne ta fahimci kamar kewa ce take kamata, kamar dai zata yi kewar wani abu me muhimmanci a rayuwarta. sai dai abu guda ɗaya take so ta sani, menene dalilin da yasa take jin jikinta yayi sanyi sosai?, irin wannan sanyi da bai taɓa ji ba. wayar da ke riƙe a hannunta tayi ringing, duk irin farin cikin da take shiga a sanda taci karo da kira daga gare shi, yau sai taji wani mix feeling ya kamata, taji kamar tana tausayin shi me kiran ba ita kanta ba da take zama da ƙyar tashi da ƙyar. ta ɗaga kiran ta kara a kunne cikin jin sanyin jikin da ya ƙaru a gareta. "uwar ƴaƴana ina kewar ki, kullum idan bana tare da ke sai in ji ina kewarki kamar zan mutu, na kasa yin aiki yau gaba ɗaya, tun da na shigo office na zauna nayi jugum, sai nake jin kamar ban taɓa kewar ki ba sai yanzu ne zan fara, gabana yana faɗuwa, zuciyata ta kasa samun nutsuwa, yau jina nake tamkar maraya, kuka zan yi Fulani Nah, ina jin kamar zan yi kuka irin wanda ƙanan yara ke yi, Fulani Nah in taho gare ki yanzu?, in zo in kwanta akan ƙijinki in dinga jiyo sautin bugawar zuciyarki a yayinda kike lallashina?, jikinki kawai nake buƙata ayanzu Fulani Nah, ina ji daga yau ba zan ƙara matsawa daga kusa da ke ba, zan daina fita aiki saboda ke, kina lafiya Fulanin Turaki?". maganganun da suka fito daga bakinsa kenan, kuma maganganun da suka haddasa wata muguwar faɗuwar gaba a ƙirjin Fillo. bata san lokacin data shiga motar ta zauna ba. "ki shirya yanzu kije wurin Maama, yanzu zan taho, ba zan iya zaman office ɗin ba, ina so yau mu yini tare, hira nake so muyi sosai, ɗa zu ta kira ni tace min faten tsaki take sha'awar ta sha". Fillo ta dafe goshinta,"Laaa ƙwara da Allah yasa ka yi wannan zancen, kamar na sani na dafa mata shi tun ɗa zu, kuma kaga har na fito zan tafi na kai mata ashe na barsa ban ɗauko ba". "ki bata ta ci da yawa Fulani Nah, duk yawansa kisa ta ta cinye shi kin ji, tana sonsa, shi ne favorite ɗinta, ta ce me kifi take son ci, in few minutes zan iso gare ku, ki kula min da kan ku, zan siyo miki mangoro, Maama kuma zan siyo mata gwanda". "tom Jannaty sai ka dawo, nima yau kewarka da nake yi ta banbanta da ta ko yaushe". "Fulani Nah saura 20days mu zama Mum and Dad ko?". "insha'Allahu Jannaty". "Allah yasa ki haihu da ranki da lafiyarki". bayan gama wayar ta su Fillo to koma ciki, tana shiga kitchen ɗin ta kira lambar Hajiya Madina. daga ɓangaren Hajiya Madina ta ce,"Daughter yanzu nake shirin kiranki, ina ta jin kewarki na damu na, idan babu abin da kike yi ki taho yanzu, in Me Babban suna ya dawo sai ku tafi tare". Fillo ta ce,"Maama faten tsakin me nama nayi, kina so ko nayi miki me kifin?". fuskar Hajiya Madina ta washe da murmushin jin daɗi, duk duniya tana bala'in son souls ɗin nan guda biyu, Turaki da Fillo. "kar ki wahalar da kanki, ba sai kin ƙara ɗora wani ba, zanci wanda jikana ya ci". "to Maama idan na zo ba zan dawo ba, yau ba'a ɓangarena yake ba". "to shikenan. ki hanzarta ki zo Daughter, ina so zan yi wasa da jikana, ina so yau nayi ta kallon fuskar ki". Fillo na murmushi ta kalli cikin da ke jikinta, haka Hajiya Madina take yi, aikinta yanzu bai wuce tasa Fillo a gaba ba tayi ta magana da cikin tamkar a gaske, in anyi dariya sai tace ai ita tana jinsa su ne basa ji, kuma idan ya fito zai ba su labari ne. haka ɗaya yau zuciyar Fillo taji tana so ta

Table of Contents

Chapters

243 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243