Skip to content
NovelPress

Hausa Novels

Chapter 154

Chapter 154

Lullubin Biri Book 1 Complete Hausa Novel 1,221 words 0 views Progress saved
Download Book

dawo gida ya huta yace min to, sai bayan su Lamiɗo sun dawo suke ce min yana can ɗin dai bai tafi ba, dan Allah Hajiya ku wuce da shi yau ɗin ya samu yaje ya huta shima". Hajiya Madina tayi ɗan jimm kamin tace,"to bari dai muga yanda za'ai, sai kun dawo". Ummi ta kira wani cikin jikokin gidan tace yaywa su Hajiya Ramla iso zuwa wajen Dadda wadda itace matar Maudo babban yayan su Hayyo hakimin yanzu kenan. direct Taraba State Specialist Hospital motar su Dada ta nufa, a reception su Ummi suka tadda Kaka ita da ƙannan Hayyo da suke uba ɗaya su biyar, tare suka wuce ward ɗin da aka kwantar da Fullo, suna tafe Dada nata ƙorafin asibitin basu iya aikin komai ba, ace mutum kwanansa biyu yau amma shiru jiki babu sauƙin arziƙi, to ita dai idan jikarta bata sami lafiya yau ba to gobe ƙasar waje za'a fitar da ita ƙwararrun likita su dubata. Belɗo dai sai bata haƙuri yake yana tayi shiru kar likitocin suji, in suka ji ba zasu ji daɗi ba, tayi masa banza bata saurare shi ba har suka iso room ɗin da Fullo ke kwance. Ummi ta dakata daga ƙofar room ɗin bata shiga ba saboda nauyin sirikinta da take ji, tunda taga su Kaka a reception ta san shine zaune a wurinta. Turaki ya miƙe cikin sauri daga gefen gadon a sanda su Dada suka shiga room ɗin, ba shi yake cutar ba amma kallo ɗaya zaka masa ka hango bala'in ramar da yayi, ga damuwa kamar a lakuta a fuskarsa, ya matsa daga gefen gadon yana yi musu sannu da zuwa. Dada ta kallesa ta girgiza kai saboda tausayinsa tace,"sannu namijin ƙwarai, Allah ya baka ladan kulawa da matarka, ka kwantar da hankalinka zata sami lafiya insha'Allahu". ya kalli Fullo da ke ta bacci sannan yay ƙasa da kansa kamar zai yi kuka yace,"Allah ya amince". Kaka na kallonsa tace,"Me Babban suna ko zaka je gida kai wanka ka samu ka ɗan huta, rabonka da abinci ma tunda jiya da rana, dan Allah kaje kaci tunda likitan yace gobe da safe zasu sallame mu". da damuwa tsantsa a muryarsa yace,"Kaka ina so naga ta farka ne tukunna". Kaka ta gyaɗa kanta tace,"to Allah ya farkar da ita cikin ƙoshin lafiya". Dada ta zauna kan kujera tana fuskantar Fullo cike da jin tausayin yarinyar, sai adu'a take tayi mata a sanda ta kama hannunta ta riƙe, ta zaro wani diamond ring daga yatsanta ta saka ma Fullo, kuma sai ya zama kamar dama na Fillon ne, yay cif a yatsan nata. kamar zata yi kuka ta dubi Kaka tace,"se yaushe ne zai farka ni kam?". Kaka ta kalli Turaki shi kuma ya kalli agogon hannunsa sannan yace,"nan da awa ɗaya insha'Allahu". Dada ta dubi Hadimar da ke ta shigo da kayan abinci tana ajiyewa tace,"Uwar wannan yarinya shina waje ko?". Hadimar tace,"ehh ranki ya daɗe". ta gyaɗa kai tare da jan tsaki tace,"sam matar Hayyo uwar banza ce, kije kice da ita ta shigo ta yiwa ƴarta adu'a, ni ban sani ba ko ƙaunar ƴar ne bata yi". sai kuma ta hau bambami yi take kamar zata haɗiye kowa, da yake mafaɗaciya ta kata'i, sai da ƙyar Belɗo ya tausheta tayi shiru yace in bata so Fillo ta tashi to taci gaba da ɗaga murya sannan aka samu ta rufe baki. Turaki ya kalla ƙofar ɗakin da Adda Asma ke shigowa, idonsa ya sauka akan gyalen Ummi da ya leƙo ta jikin ƙofar, ya juya ya ɗauki wayarsa a kan drower ya fita cikin sanyi jiki kamar mara laka, ya sani in har yana cikin ɗakin Ummi ba zata taɓa shigowa ba, tun zuwansu asibitin sau ɗaya ta iya zama a ɗakin shima duk a takure kuma saboda shi, irin iyayen nanne masu bala'in jin kunyar sirikansu. tana ganin fitowarsa ta matsa gefe, ya durƙusa har ƙasa ya gaida ita, sai ta kasa amsawa ta bisa da kallo tana tsananin jin tausayinsa, kwana uku rak amma ya dawo kamar shine mara lafiyar da aka kwantar, idon nan yay jawur ya ƙanƙance tsabar ba ya samun bacci. ya katse shirun nata da cewa,"Ummi ki shiga daga ciki". tace,"a'a da ka koma kawai, ai ina jin ma yanzu zamu wuce". yace,"a'a Ummi ki shiga". sai ta ƙara kallonsa tace,"ya kamata ka huta haka". yay shiru bai iya cewa komai ba, kowa nata ce masa ya huta ya huta, ta ina zai iya hutawa alhalin Fulaninsa na cikin wannan halin. Ummi tace,"baka ce komai ba". yace,"tom Ummi". ya amsa ba dan yana jin zai iya aiwatar da abinda tace ɗin ba. Ummi na shiga room ɗin likita yazo, Turaki ya tsaya daga jikin window yana sauraron bayanin da Dr ɗin ke yi. "kar ku damu allurar bacci ce muka yi mata domin ta samu ta huta yanda ya kamata, ta yacca ba za'a samu damuwa ba idan ta farka, saboda gaskiya tana buƙatar hutu shisa ku ka kalla an ɗau tsayin wannan kwanakin bata farka ba, amma insha'Allah in the next 50minutes zata farka kuma lafiya lau da izinin Allah". duk suka amsa da amin, shi kuma ya ƙara da cewa,"sai dai akwai abinda ya kamata a kula da shi, kamar yanda na faɗa muku tunda farko ta samu heart failure, dan haka ya zama dole a kiyaye duk wani abu da zai iya zama damuwa a gareta, ai ƙoƙarin kiyaye ɓacin ranta sosai, ko stressing kanta da yawa kar ake bari tana yi, zan ƙara nanata muku duk wani abu da zai zamar mata damuwa ko ya sanyata ɓacin rai ko ya haifar mata da fushi to ya zama dole a kiyaye shi in har kuna sonta da ranta". da sauri Dada tace,"insha'Allahu za'a kiyaye hakan, baza ma mu bari ranta ya ɓaci ba balle kuma damuwa, ai ƴar gata ce gaba da baya, fatanmu dai Allah ya tashi kafaɗunta lafiya lafiya". Dr ya dubi ƴan dubiyan da ke ta shigowa ɗakin, da kuma hayaniyar waɗanda yake ji daga waje, ya sauke numfashi yace,"amm ya kamata a bata space dan wannan hayaniyar ma zata iya zamar mata matsala, da za'ai haƙuri ma ƴan dubiyan su dakata har zuwa ta farka". Dada ta ama masa"to shikenan yanzu kowa zai wuce kam". ya ɗauko wata takarda acikin file ɗinsa ya miƙawa Bobbo wanda ya dawo daga pharmacy siyo magunguna, Bobbo ya karɓa ya karanta sannan ya miƙawa Lamiɗo shi kuma yabi bayan likitan zuwa office ɗinsa. asibiti dai sai ya zama kamar gidan biki, dan cikin lokaci ɗaya ya ɗinke da ƴan dubiya waɗanda suke zuwa gaisuwa a shaida musu ƴar Hayyo na kwance a asibiti to duk sai suyo asibitin, kace wata ƴar ƙusan ce ke kwance dan manyan mutane ma sai zuwa dubata suke, a shiga a fita a shiga a fita haka aka dinƙa yi. irin karramammun mutanen da ke wajen in akace maka ƴan'uwan Hayyo ne sai mutum ya ƙaryata, zaka sha mamaki matuƙa in akace mutum me wannan gatan ne ya tsiyatar da rayuwarsa a iska. ba'a sami sasaucin mutane a asibitin ba sai ƙarfe sha ɗaya da rabi, shima kuma saboda Dada ta koma gida ne, dan tana ta waya tana cewa a bar mutane

Table of Contents

Chapters

243 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
  158. 158 Chapter 158
  159. 159 Chapter 159
  160. 160 Chapter 160
  161. 161 Chapter 161
  162. 162 Chapter 162
  163. 163 Chapter 163
  164. 164 Chapter 164
  165. 165 Chapter 165
  166. 166 Chapter 166
  167. 167 Chapter 167
  168. 168 Chapter 168
  169. 169 Chapter 169
  170. 170 Chapter 170
  171. 171 Chapter 171
  172. 172 Chapter 172
  173. 173 Chapter 173
  174. 174 Chapter 174
  175. 175 Chapter 175
  176. 176 Chapter 176
  177. 177 Chapter 177
  178. 178 Chapter 178
  179. 179 Chapter 179
  180. 180 Chapter 180
  181. 181 Chapter 181
  182. 182 Chapter 182
  183. 183 Chapter 183
  184. 184 Chapter 184
  185. 185 Chapter 185
  186. 186 Chapter 186
  187. 187 Chapter 187
  188. 188 Chapter 188
  189. 189 Chapter 189
  190. 190 Chapter 190
  191. 191 Chapter 191
  192. 192 Chapter 192
  193. 193 Chapter 193
  194. 194 Chapter 194
  195. 195 Chapter 195
  196. 196 Chapter 196
  197. 197 Chapter 197
  198. 198 Chapter 198
  199. 199 Chapter 199
  200. 200 Chapter 200
  201. 201 Chapter 201
  202. 202 Chapter 202
  203. 203 Chapter 203
  204. 204 Chapter 204
  205. 205 Chapter 205
  206. 206 Chapter 206
  207. 207 Chapter 207
  208. 208 Chapter 208
  209. 209 Chapter 209
  210. 210 Chapter 210
  211. 211 Chapter 211
  212. 212 Chapter 212
  213. 213 Chapter 213
  214. 214 Chapter 214
  215. 215 Chapter 215
  216. 216 Chapter 216
  217. 217 Chapter 217
  218. 218 Chapter 218
  219. 219 Chapter 219
  220. 220 Chapter 220
  221. 221 Chapter 221
  222. 222 Chapter 222
  223. 223 Chapter 223
  224. 224 Chapter 224
  225. 225 Chapter 225
  226. 226 Chapter 226
  227. 227 Chapter 227
  228. 228 Chapter 228
  229. 229 Chapter 229
  230. 230 Chapter 230
  231. 231 Chapter 231
  232. 232 Chapter 232
  233. 233 Chapter 233
  234. 234 Chapter 234
  235. 235 Chapter 235
  236. 236 Chapter 236
  237. 237 Chapter 237
  238. 238 Chapter 238
  239. 239 Chapter 239
  240. 240 Chapter 240
  241. 241 Chapter 241
  242. 242 Chapter 242
  243. 243 Chapter 243